Abba ya rufe duk asusun ma’aikatun Kano
Ya ba da umarnin ne a yayin ganawa da shugaban hukumar tara haraji ta KIRS
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci Ofishin Akanta-Janar na jihar da ya rufe duk asusun hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar nan da mako guda.
Abba ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake ganawa da Shugaban Hukumar tara Kudaden Shiga (KIRS) da kuma shugabannin hukumomi da ma’aikatun jihar.
Da yake ba da umarnin a zaman da ke gudana a Gidan Gwamnati, Abba ya ce daukar matakin ya zama dole, domin hana a karkatar da kudaden shigan jihar daga aljihun gwamnati.
Hakan kuma zai ba da damar aiwatar da tsarin asusu guda na tara kudaden shiga domin hana zurarewarsu da kuma tabbatar da shugabanci na gari.
- Mutane 16 sun kone kurmus a hatsarin mota a Ondo —FRSC
- Rabon Gado: Alkali ya soke hukuncin kotun Musulunci
- Matashi ya yi wa ’yar shekara 4 yankan rago a gidansu
Gwamnan ya umarci daukacin shugabannin hukumomi da ma’aikatun jihar da su gaggauta bin umarnin hade asusun kudaden shigan a wuri guda.
“Akanta-Janar zai ba wa bankuna umarnin rufe duk wani ausun hukuma ko ma’aikatar wannan jihar, su tura kudaden da ke ciki zuwa asusun Ofishin Akanta-Janar.
“Bankunan za su ba mu takardar shaidar bin wannan umarni ta hannun Akanta-Janar da Shugaban KIRS domin daukar mataki na gaba,” in ji gwamnan.
Ya ba wa al’ummar jihar tabbacin gudanar da kudaden jihar wajen bunkasa tattalin arzikin jihar da inganta rayuwarsu da kuma a fannin ilimi, lafiya, noma da dai sauransu