Abba ya sassauta dokar hana fita a Kano
An sassauta dokar ce daga karfe 12 na rana zuwa karfe na yamma a ranar Juma’a kadai.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sassauta dokar hana fita domin a samu damar gudanar da Sallar Juma’a.
Gwamantin jihar ta sassauta dokar ce daga karfe 12 na rana zuwa karfe 5 na yamma a ranar Juma’a kadai.
Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Haruna Isah Dederi, ya roki Allah Ya zaunar da jihar lafiya.
Gwamnatin Kano ta sanya dokar ce bayan zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar ta rikiɗe ta koma tarzoma da sace-sace.