Abba ya umarci jami’an tsaro su kawo ƙarshen faɗan daba a Kano

Faɗan daba na ci gaba da yin ƙamari a jihar.

Abba ya umarci jami’an tsaro su kawo ƙarshen faɗan daba a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci jami’an tsaro da su kawo ƙarshen daba da masu tada zaune-tsaye a jihar.

Yusuf, ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jihar (SEC) a Kano.

Gwamnan ya yi Allah-wadai da yadda ake samun tashe-tashen hankula a sanadin faɗan daba a wasu sassan jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro ba a jihar ba.

Ya ɗora wa alkalan jihar alhakin zartar da hukuncin waɗanda suke tsare cikin gaggawa da adalci.

Ya buƙaci hukumomin tsaro da su mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Kazalika, Yusuf ya buƙaci jama’ar jihar da su bai wa gwamnatinsa gudunmawa, sannan su kasance masu kiyaye doka da oda a jihar.