Abba ya yi tafiya yayin da rikici ya dabaibaye NNPP a Kano
A baya-bayan na dai rikicin cikin gida ya dabaibaye jami’yyar NNPP a Jihar Kano.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi tafiya zuwa Abuja, yayin da rikici ke ƙara tsamari a jami’yyar NNPP a jihar.
A ranar Litinin, gwamnan ya yi sasanci tsakanin Sakataren Gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi, da wasu wakilan mazaɓarsa da suka nuna rashin jin daɗinsu kan yadda abubuwa ke tafiya.
- Kotu ta hana EFCC kama tsohon minista kan taƙaddamar fili
- Ba zan ce uffan kan rikicin NNPP a Kano ba — Kwankwaso
Duk da sasancin gwamnan, jam’iyyar ta dakatar da Bichi da Kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggol, bisa zargin rashin biyayya ga jam’iyyar.
Gwamnan ya yi jiran kusan sa’o’i biyu a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, kafin daga bisani ya tashi zuwa Abuja.
A lokacin da gwamnan ya yi tafiya, jagoran jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na ganawa jiga-jigan jam’iyyar jihar.
Ko da aka tambayi Kwankwaso kan rikicin NNPP, ya ƙi yin tsokaci, inda ya ce shugabannin jam’iyyar sun ɗauki matakin da ya dace.
A baya-bayan nan dai wasu sun nuna damuwa kan irin ikon da Kwankwaso ke da shi a siyasar gwamnatin Kano, wanda suke ganin hakan yana hana Gwamna Yusuf gudanar da ayyukasa yadda ya kamata.
Hakan ne ya sa wasu ƙungiyoyi fara kiran da “Abba Tsaya da Kafarka”, a wani yunkuri na raba Gwamna Yusuf da Kwankwaso.
Sai dai wannan kiranye-kiranye da ake yi wanda aka alaƙanta su da Sakataren Gwamnatin jihar, amma ya musanta zargin.