Abba da Tinubu suna ganawar sirri a Fadar Shugaban Kasa

Aminiya ta ruwaito cewa shugabannin suna ganawa ne a yammacin ranar Litinin a yayin da ake dakgon sauya shekar Gwamna A

Abba da Tinubu suna ganawar sirri a Fadar Shugaban Kasa

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shiga yana wata ganawar sirri da Shugaban Kasa Bola Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

A yammacin ranar Litinin ne shugabannin biyu suka fara ganawar a yayin da ake dakgon sauya shekar Gwamna Abba zuwa Jam’iyyar APC mai mulki daga NNPP.

Gwamnan ya isa fadar shugaban kasa ne da misalin karfe 4.10 na yamma sanye da farar babbar riga inda daga nan suka shiga ganawar da shugaban kasa a cikin ofishin shugaban kasa.