Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano

Wanda gwamnan ke shirin naɗawa muƙamin kwamishina shi ne Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Kano, KNUPDA.

Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar dokokin jihar sunan Ibrahim Yakubu Adamu domin tantancewa da tabbatar da naɗinsa a matsayin sabon Kwamishina.

Kakakin Majalisar, Alhaji Jibrin Falgore ne ya bayyana hakan yayin da yake karanta wasiƙar gwamnan a zaman majalisar da ya gudana a yau Litinin.

Aminiya ta ruwaito cewa, Ibrahim Yakubu Adamu wanda gwamnan ke shirin naɗawa muƙamin kwamishina shi ne Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Kano, KNUPDA.

Falgore ya ce nan gaba kaɗan za su aika masa goron gayyata domin tabbatar da buƙatar gwamnan.

Kazalika, majalisar ta kuma tabbatar da dokar kafa sabuwar Hukumar Kula da Gine-Ginen Gwamnati da Ababen More Rayuwa.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussein na jam’iyyar NNPP daga Ƙaramar Hukumar Dala, ya ce sabuwar hukumar ce za ta riƙa ɗawainiyar kula da gine-ginen gwamnati da sauran ababen more rayuwa da suka haɗa da tituna, gadoji da sauransu.

’Yan bindiga sun kashe manoma 14 a Ondo

Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano

Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad

Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC