Abbas Sadik: Tun ina dan shekara 6 na fara fim
Tarihi a takaiceSunana Abbas Sadik an haife ni a unguwar Kabalan Doki da ke karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna. Mun koma garin Jos a shekarar 1979, inda a can na yi firamare ta St. Theresa Primary School. Bayan na kammala ne a shekarar 1987, na wuce gaba zuwa sakandare. Daga nan na […]
Tarihi a takaice
Sunana Abbas Sadik an haife ni a unguwar Kabalan Doki da ke karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna. Mun koma garin Jos a shekarar 1979, inda a can na yi firamare ta St. Theresa Primary School.
Bayan na kammala ne a shekarar 1987, na wuce gaba zuwa sakandare. Daga nan na yi digiri kan Lissafin harkokin kudi a Jami’ar Jos a shekarar 1998, sannan na yi aikin yi wa kasa hidima a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Mahaifina ma’aikacin gidan talabijin din NTA Jos ne, wanda shi ne dalilin da ya sa muka koma can da zama. Mahaifiyata kuma ma’aikaciyar asibiti ce, kuma memba ce a kungiyar Mata Musulmi ta FOMWAN. Kodayake na fara wasan kwaikwayo ne tun ina da shekara shida da haihuwa saboda galibi mahaifina kan kai ni NTA Jos duk lokacin da ake daukar shirin da ke bukatar kananan yara a ciki, sai a sa ni a matsayin yaro.
Bayan na dan kara girma ne sai ya dauke ni ya kai ni wajen abokan aikinsa, inda ya gabatar da ni a wajensu. Abokansa a lokacin sun hada da Waziri Zayyanu da Bilya Keffi da sauransu. Ba zan manta ba a lokacin a gabana ake daukar shirin ‘karkuzu na Bodara’ da wani shiri na Magaji Mijinyawa mai suna ‘Kwaskwaro’ da shirin Inglishi na ‘Man Behind The Mask’ da sauransu.
Amma kafin in tsunduma sosai a harkar wasan kwaikwayo mahaifina ya taba fatan in zama dan wasan kwallon kafa, hakan ya sa ya sanya ni makarantar ba da horo kan kwallon kafa ta Greater Tomorrow Soccer Academy da ke garin Jos, wannan makarantar ce shahararren dan wasan kwallon kafar nan wato Mikel Obi ya yi. Amma fatan mahaifina bai tabbata ba, saboda yadda na samu karaya a hannuna har sau biyu a filin wasa ya sa ni da shi muka hakura.
Daga baya ya so in zama malamin makarantar Islamiyya saboda yadda ya jajirce wajen tabbatar da na yi karatun addini sosai.
Nakan tuna a lokacin da mahaifina yake raye, yakan ba ni shawarwari bayan ya kalli fina-finaina, saboda kasancewarsa ma’aikacin yada labarai, don haka ya san ciki da wajen harkar wasan kwaikwayo, wanda hakan na nufin nuna goyon bayansa gare ni.
Idan kuma muka koma baya kadan na fara harkar nan ne da fina-finan Turanci kamarsu: ‘Eba’ da ‘Amina’ da ‘Elebenth Hour’ da ‘Our Life’ da sauransu. Kuma wannan fim din na ‘Our Life’ da muka yi lokacin muna dalibai a jami’a ya kunshi rayuwar matasa ’yan jami’a ne, kuma shi ne wasan da ya fara fito da fitaccen jarumin fina-finan Kudu, Jim Iyke. Ni da shi ne jaruman, kuma hakan na da nasaba da yadda shi ma dalibi ne a Jami’ar Jos, bangaren Ilimin Falsafa wato (Philosophy). Wannan ya sa muka san juna tun lokacin. Kodayake daga bisani ya koma Jihar Legas inda tauraruwarsa ta ci gaba da haskakawa a fina-finan kudu har zuwa yanzu.
Abin da ya ja hankalina na dawo masana’antar fina-finan Hausa
Kishi ne ya sa, saboda a lokacin da muke shirya fina-finan Turanci mun fahimci cewa sakonmu zai fi isa ga jama’armu idan muka sa shi a harshenmu na asali. A gaskiya fina-finan Turanci sun samu karbuwa a Jos. Amma wani dalilin da ya sa ni barin hakar shi ne, akwai wahalhalun da ke ciki, suna da dama, misali idan za ka saki fim dinka zuwa kasuwa sai ka kai sa Jihar Legas, wanda idan na Hausa ne Kano za ka kai, wadda ba ta da nisa daga Jos. Kuma wani dalili shi ne, yawan kudin shirya fim din kansa ya sha bamban da na Turanci. Wadannan ne suka sa muka ga zai fi kyawu mu karkato zuwa fina-finan Hausa.
Fim din Hausa da na fara fitowa
Na fara ne da wani fim mai suna ‘Tirna’ a shekarar 2000 wanda Hajiya Halima Abdullahi ta shirya, Alhaji Garba dan Jos kuma ya ba da umarni. Amma kawo yanzu ba zan iya kayyade yawansu ba, saboda suna nan birjik. Akwai lokacin da idan ina kallon setilayit da ke nuna fina-finan Hausa, nakan ga kaina a cikin wasu fina-finan wanda kafin faruwar hakan ba zan iya cewa ina cikinsu ba.
Nasarori
Alhamdulillahi, nasarar farko da na samu a harkar ita ce, har yau idan ana maganar mai kawo tufafin da ake sanyawa lokacin daukar fim wato Costume a masa’antar fina-finan Hausa zan shiga sahun gaba.
Nasara ta biyu ita ce, ina da rol din da kowa ya san ni da shi, wato yadda nake fitowa a matsayin wayayye ko dan kwalisa. Na samu karbuwa wajen ’yan kallon kuma ni daya ne daga cikin jerin ’yan wasan da ba sa bukatar gabatarwa duk inda suka taka sahunsu.
Wata nasara kuma ita ce, yadda na yi tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare da dama kamarsu: Jamhuriyar Nijar da Ghana da Benin da sauransu. Har ila yau, sanadiyyar wannan sana’ar na zama Jakadan Kamfanin Sadarwa na MTN, yau tsawon shekara takwas ke nan.
kalubale
Abun da ya wuce, ya wuce sai dai mu yi addu’a Allah Ya kiyaye gaba. A gaskiya akwai su da dama amma ba zan iya bayyana su ba, saboda na dauke su ne a matsayin jarrabawa daga Lillah. Sanadiyyar harkan nan, na ga kiyayya da yaudarar da ban taba ganin irinta ba a rayuwata. Nakan manta da duka wadannan kalubalen, saboda duniya juyi-juyi ce, musamman ma lokacin da na tuna da irin nasarorin da nake ganin na samu a sana’ar.
Dalilin da ya sa kwana biyu ba a ganina a fina-finai
Kamar yadda na bayyana a baya, ina wa Kamfanin MTN wasu aikace-aikace ne. Wannan ya sa ba a ganina a fina-finai kamar yadda aka saba gani. Hakazalika, akwai aikin wata kungiya da ke fafutuka kan tsafta da kuma irin abincin da ya dace jama’a su ci, mai suna Global Alliance for Improbed Nutrition (GAIN) da nake yi daga lokaci zuwa lokaci. Akwai kuma wasu kananan harkokin kasuwanci da nake. Wadannan ne suka sa kwana biyu ba a ganina a fim. Amma ban bar harkar gaba daya ba. Ina raba kafa ne.
Burina
Bai wuce fatan cika wa da imani ba
Iyali
Ina da mata daya da ’ya’ya biyu.