Abbas Tajuddeen na neman wa’adi na 5 a Majalisar Tarayya
Abbas Tajuddeen, wanda ya fara shiga Majalisar Wakilai tun a shekarar 2011, ya ce wakilcinsa ya kawo gagarumin sauyi ga rayuwar al’ummar mazabar.
Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara domin wakiltar mazabar Tarayya ta Zariya karo na biyar.
A yayin babban taron da ya gudana a ranar Asabar, a filin Idi na Mallawa da ke hanyar Jos Zariya, wanda ya samu halartar magoya baya da al’ummar mazabar, Abbas Tajuddeen, wanda ya fara shiga Majalisar Wakilai tun a shekarar 2011, ya ce wakilcinsa ya kawo gagarumin sauyi ga rayuwar al’ummar mazabar.
Aminiya ta ruwaito cewa magoya bayansa sun gudanar da tattakin nuna goyon baya tun daga Fadar Sarkin Zazzau, ta cikin Babban Dodo, har zuwa Lemu, Kofar Doka da Tudun Wada, kafin su isa filin Idi na Mallawa inda aka gudanar da taron.
“Waɗannan ba hasashe ba ne. Ayyuka ne da kowa yake gani da ido. Sakamako ne da ake iya aunawa,” in ji Abbas, yana mai cewa ayyukan da aka aiwatar sun taimaka wajen inganta rayuwar al’umma da ba su damar dogaro da kai.
- Mayaƙan sa-kai sun kashe mutum 69 a Kongo
- Kwankwaso ya amince a ba wa Kudu takarar Shugaban Kasa ta NDC
“Yau ina sanar da ku a hukumance cewa zan sake neman amanar al’ummar mazabar Tarayya ta Zariya domin ci gaba da wakiltarku a Majalisar Wakilai.
“Wannan sanarwa ba ta ginu ne kan al’ƙawura kawai ba. Ta ginu ne kan aiki, sakamako, da tarihin ayyukan da jama’a za su iya gani da kuma tabbatarwa.
“Lokacin da kuka fara ba ni wannan dama, na yi alƙawarin cewa wakilci ba zai kasance mai nisa da jama’a ba.
“Na ce shugabanci dole ne ya samar da sakamako a bayyane, na kuma ce duk mai muƙamin gwamnati dole ne ya inganta rayuwar jama’a, Kuma tare da ku, muka yi aiki don cika wannan alkawari,” in ji shi.
Shugaban Majalisar Wakilan ya bayyana cewa har yanzu yana daga cikin ’yan majalisar da suka fi ƙwazo a ƙasar nan, inda ya gabatar da kudurori 74, kuma 21 daga cikinsu sun zama dokoki.
“Ba domin neman ɗaukaka ko tallata kai aka yi waɗannan ƙoƙari ba. An yi su ne domin magance matsaloli da ƙarfafa shugabanci nagari,” in ji shi.
Ya tunatar da al’umma irin ayyukan ci gaba da ya kawo wa Zariya, yana mai cewa yin doka kaɗai bai isa ba idan jama’a ba sa jin tasirin wakilci a rayuwarsu ta yau da kullum.
A cewarsa, saboda haka ne ya kawo ayyukan ci gaba kusa da al’umma.