Abbas ya bukaci ’yan kwadago su janye shirin shiga yajin aiki
NLC ta shirin shiga yajin aikin sai Baba ta gani.
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bukaci kungiyoyin kwadago na NLC da TUC da su janye shirin shiga yajin aikin da suke shirin farawa.
Ya ce majalisar za ta shiga tsakanin kungiyar kwadagon da Gwamnatin Tarayya don ganin an lalubo bakin zaren.
- Darussan da muka koya daga tarihin Tafawa Balewa —’Yan Najeriya
- EFCC ta tsare masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba 80 a Kwara
NLC dai ta sha zargin Gwamnatin Tarayya da gaza magance kalubalen da ke tattare da cire tallafin man fetur.
Sai dai Abbas ya yi wannan roko ga NLC a ranar Talata, bayan da aka koma zaman majalisar bayan hutun makonni shida.
Ya roki kungiyoyin da su yi la’akari da irin matakan da gwamnati ta dauka domin magance matsalar tattalin arzikin kasar.
A cewarsa, shiga yajin aiki a halin yanzu ba abin da zai kara face dagula halin da ake ciki a yanzu.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago ta NLC ke shirin shiga yajin aiki, bayan yajin aikin gargadi na kwana biyu da ta yi a baya.
Shirin shiga yajin aikin ya biyo bayan gazawar tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da NLC a makon da ya wuce.