Abbas ya janye ƙudurin hukunta waɗanda suka ƙi rera taken ƙasa

Duk wani mutum da ya ƙi rera taken ƙasa zai yi zaman gidan yari na shekara 10.

Abbas ya janye ƙudurin hukunta waɗanda suka ƙi rera taken ƙasa

Kakakin Majalisar wakilai Tajudeen Abbas

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya janye ƙudurin da ya gabatar na samar da dokar “hukunta masu ayyukan tayar da hargitsi da waɗanda suka ƙi rera taken ƙasa”.

A cikin sanarwar janye ƙudurin dokar, wadda ta samu sa hannun mai taimaka wa shugaban Majalisar wakilan kan yaɗa labarai, Musa Abdullahi Krishi, ta ce an janye dokar ne “bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki da kuma kyakkyawan la’akari da halin da ƙasa ke ciki.”

Sanarwar ta ƙara da cewa Honorabul Abbas “ba zai taɓa goyon bayan duk wani mataki da zai yi illa ga zaman lafiya da haɗin kan al’ummar ƙasar ba.”

Wannan matakin na zuwa ne bayan lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce da suka mai zafi tsakanin ’yan Najeriya, musamman matasa da ke ganin hakan ya saba da tsarin dimokuradiyya.

Matasan sun yi zargin cewa ana ƙoƙarin ɓullo da dokar ne domin murƙushe duk wani yunƙuri na yin zanga-zanga, bayan zanga-zangar matsin rayuwa da al’ummar ƙasar suka gudanar a farkon wannan wata na Agusta.

Ana iya tuna cewa Shugaban Majalisar Wakilan, Tajudeen Abbas ne ya gabatar da ƙudurin mai taken “Counter Subversion Bill 2024” a ranar 23 ga watan Yuli, inda ƙudurin ya tanadi hukunce-hukunce ga mutanen da aka kama da laifin zagon ƙasa ko tayar da hankali ko alaƙa da wasu ƙungiyoyin da aka haramta.

Wani ɓangare na ƙudurin ya tanadi cewa: “Duk mutumin da aka kama da laifin yin karan-tsaye ga zirga-zirgar ababen hawa, ko datse hanya ko ƙaƙaba dokar zaman gida, ko yin tattaki ba bisa ƙa’ida ba ko kuma wasu abubuwa masu kamanceceniya da hakan zai fuskanci tarar naira miliyan biyu ko kuma ɗaurin shekara biyar a gidan yari.”

Haka nan, wani ɓangare na ƙudurin dokar da ya ja hankalin al’umma shi ne wanda ya ce: “Duk wani mutum da ya lalata wani tambari na ƙasa, ko ya ƙi rera taken ƙasa, ko ya yi ƙoƙarin lalata wurin ibada da nufin haifar da rikici da yi wa gwamnati ɓarna, ya aikata laifi wanda za a buƙace shi ya biya tarar naira miliyan biyar ko zaman gidan yari na shekara 10.”

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara