Abbas ya zama Shugaban Majalisar Wakilai ta 10

An zabi Benjamin Kalu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.

Abbas ya zama Shugaban Majalisar Wakilai ta 10

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Zariya ta Jihar Kaduna, Tajudeen Abbas ya zama Shugaban Majalisar Wakilai ta 10 da gagarumin rinjaye.

Abbas ya samu kuri’u 353, inda ya doke tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar, Ahmed Idris Wase da Aminu Sani Jaji wanda kowanensu ya samu kuri’u uku-uku kacal.

Akawun Majalisar, Magaji Tambuwal ne ya sanar da sakamakon zaben.

Ya ce zababbun ’yan majalisu 359 ne suka kada kuri’a a zaben.

Tuni dai Abbas Tajuddeen ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin mamba kuma Shugaban Majalisar Wakilai.

Aminiya ta ruwaito cewa, an kuma zabi Benjamin Kalu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar ba tare hamayya ba.

Gobara ta ƙone shaguna da kayan miliyoyi a kasuwar Nasarawa

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa