Abduljabbar da malaman Kano: An tashi ba a cimma matsaya ba

Bayan shafe sa’a biyar ana muhawara, ba bangaren da ya gamsu da hujjojin dayan

Abduljabbar da malaman Kano: An tashi ba a cimma matsaya ba

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Bayan shafe kusan sa’a biyar ana tafka mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Malaman Kano, an tashi babu bangaren da ya gamsu da hujjojin daya bangaren.

Da safiyar ranar Asabar ne dai Sheikh Abduljabbar da malaman da aka zaba su fafata da shi a mukabalar da gwamnatin Kano ta shirya suka hallara a ofishin Hukumar Zakkah da Hubusi da ke birnin Kano.

  1. ‘Manoman auduga 65,000 za su amfana da rancen noma’
  2. Mukabala: Yau za a yi ta ta kare tsakanin Sheik Abduljabbar da malaman Kano

Malaman, wanda sun hada da Malam Mas’ud Hotoro, da Malam Bashir Kofar Wambai, da Dokta Sani Umar Rijiyar Lemo, da kuma Malam Abubakar Mai Madatai.

Farfesa Salisu Shehu na Jami’ar Bayero da ke Kano ne alkalin da ya jagorancin mukabalar.Abduljabbar ya bayyana cewar bai gamsu da hujjojin da aka gabatar masa ba a yayin mukabalar.

Yadda aka tattauna

“Na bayyana ra’ayina tun farko, matsalar ita ce ba su ba ni [bayani a kan] yadda tsarin mukabalar zai kasance ba don samun nasara da mafita a zaman.

“Ba karya ce bukatarmu ba, bukatarmu [ita ce] samar wa addininmu mafita, saboda shi addini ibada ce.

“Idan har an tabbatar min da laifina zan amshi laifina sannan na nemi gafarar mutane, amma ba a tabbatar min da laifina ba.

“Abin da duk na kawo babu wanda aka warware min, da an warware min da ni da kaina zan amsa faduwa”, inji Sheokh Abduljabbar.

A jawabinsa na rufe mukabalar, Farfesa Salisu Shehu ya ce Abduljabbar ya ki tsayawa a kan maudu’i daya don samun matsaya a tsakaninsa da sauran malaman.

“Duk tambayoyin da aka gabatar wa malaman Abduljabbar ba ya tsayawa a kansu ya ba da amsoshin da aka masa.

“Na farko yana cewa babu isasshen lokaci, na biyu yana cewa a tsaya a kan maudu’i guda daya a yi magana, amma idan ya zo bayani sai ya dinga kewaye ba ya tsayawa a kan maudu’i guda daya kamar yadda ya bukata.

“Kuma abin da ake bukata a kan wasu tambayoyin, shi ne cewa in ya yi da’awar cewa maganra da ya yi ta kaza daga littafi kaza ya gani, in an bukaci ya bude littafin ya fada wa mutane, sai ya ba da uzurin cewa babu lokacin da zai bude littafin ya karanto inda ya gano abin da yake kafa hujja a kai,” inji Farfesa Salisu.

Haka ba ta cimma ruwa ba

Bayan shafe watanni ana jiran wannan mukabala, kamar yadda Hausawa kan ce ‘Rana bata karya’, ranar ta zo an yi tattauna.

sai dai kuma mai yiwuwa ta bangaren samun gamsuwa a kowanne bangare, haka ba ta cimma ruwa ba.