Abdullahi Abbas ya jagoranci taron murnar nasarar APC a kotu

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas da ’ya’yan jam’iyyar sun fito titi suna murnar nasarar zaben gwaman jihar da Nasiru Gawuna ya samu kotu

Abdullahi Abbas ya jagoranci taron murnar nasarar APC a kotu

Abdullahi Abbas

Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya jagoranci magoya bayan jam’iyyar wajen bayyana murnarsu bisa nasara da dan takarar gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna ya samu kotu.

Daruruwan magoya bayan APC ne suka bi kan titi suna kade-kade da raye-rayen ‘sai Gawuna’, bayan da kotun ta soke zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ta ayyana Gawunan a matsayin halastaccen wanda ya ci zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris.

An ga Abdullahi Abbas ya fito saman mota yana ta shan hannu da magoya bayan jam’iyyar da ke ta jinjina masa.

Da farko dai bayan zaben Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya yi nasara, da kuri’u 1,019,692, a yayin da Gawuna ke biya da shi da kuri’u 890, 705.

Daga bisani ne Gawuna da APC suka je kotu suna kalubalantar nasarar Abba, da cewa ba da halastattun kuri’u ya ci zaben ba.

Sun shigar da kara ne suna kalubalantar halascin takarar Abba, wanda babu sunansa a rajistar jam’iyyar NNPP, da kuma zargin magudin zabe, da saba dokar zabe.

Daga bisani kwamitin alkalan kotun suka soke zaben nasa bayan amincewa da korafin APC na rashin sunan Abba a rajistar NNP.

Sannan suka soke kuri’i 165,663 daga cikin wadanda ya samu a matsayin haramtattu, saboda ba sa dauke da sitamfin hukumar INEC.

Wannan ne ya ba wa Gawuna damar shan gaban Abba da kuri’u 36,766, a yayin da yawan kuri’un Abban ya ragu zuwa 853,939.
Da haka ne kotu ta umarci INEC ta janye takardar shaidar cin zaben da ta ba wa Abba, sanna ta mika wa Gawuna.

Sai dai NNPP ta ce za ta daukaka kara kuma tana da kwarin gwiwar cewa kotun gaba za ta warware hukuncin wannan kotun.

Lauyan jam’iyyar, Baritsa Tudun Wuzurci ya ce kafin tafiya kotu na gaba za su tattauna da wadanda yake wakilta domin daukar matakin da ya dace.

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano

Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

Mutum 38 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Kazakhstan