Abdulmumin Kofa ya jagoranci Alaranmomi sallar rokon samun sauki a Najeriya
Tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kiru da Bebeji na Jihar Kano, Honarabul Abdulmumini Jibril Kofa, ya dauki nauyin shirya wani taron gudanar da addu’o’i kan kalubalen da suka yi wa kasar nan dabaibayi. A ranar Lahadi ne tsohon dan Majalisar ya shirya wani gagarumin taro na gabatar da addu’o’i a gidansa da ke […]
Tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kiru da Bebeji na Jihar Kano, Honarabul Abdulmumini Jibril Kofa, ya dauki nauyin shirya wani taron gudanar da addu’o’i kan kalubalen da suka yi wa kasar nan dabaibayi.
A ranar Lahadi ne tsohon dan Majalisar ya shirya wani gagarumin taro na gabatar da addu’o’i a gidansa da ke garin Kofa domin Mai Duka ya yaye wa kasar nan matsalolin da take fuskanta.
- Masu garkuwa da marayu a Abuja na neman N30m a matsayin kudin fansa
- Kotu ta ba da umarnin a kai matar Sheikh El-Zakzaky asibiti
An gudanar da taron addu’o’in wanda ya kunshi tawagar Alaranmomi 1000 bisa jagorancin Shugaban Kungiyar Izala na Kasa reshen Jihar Kano, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan.
Bayan an gudanar da musaffar Al-Kur’ani mai girma, Honarabul Kofa ya kuma jagoranci daruruwan makaranta Al-Kur’ani limancin sallar nafila da nufin Allah ya karbi addu’o’in da aka gabatar yayin taron.
Kazalika, a yayin taron, an yi gabatar da addu’a ta musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Aminiya ta samu cewa an kiyaye dukkan matakan kariya na dakila yaduwar cutar Coronavirus kamar yadda mahukuntan lafiya suka shar’anta.