AbdulSalami Abubakar ya yi alkwarin taimaka wa kungiyar kwallon Gora ta Neja

Tsohon Shugaban kasa Janar AbdulSalami Alhaji Abubakar ya yi alkwarin taimaka wa kungiyar kwallon Gora ta Jihar Neja wadda za ta wakilci Najeriya a gasar cin Kofin Nahiyar Afirka a kasar Afirka ta Kudu nan gaba a bana.Janar AbdulSalami Abubakar ya yi alkawarin ne lokacin da Shugaban kungiyar Wasan kwallon Gora ta Jihar Neja, Alhaji […]

AbdulSalami Abubakar ya yi alkwarin taimaka wa kungiyar kwallon Gora ta Neja
AbdulSalami Abubakar ya yi alkwarin taimaka wa kungiyar kwallon Gora ta Neja

Tsohon Shugaban kasa Janar AbdulSalami Alhaji Abubakar ya yi alkwarin taimaka wa kungiyar kwallon Gora ta Jihar Neja wadda za ta wakilci Najeriya a gasar cin Kofin Nahiyar Afirka a kasar Afirka ta Kudu nan gaba a bana.
Janar AbdulSalami Abubakar ya yi alkawarin ne lokacin da Shugaban kungiyar Wasan kwallon Gora ta Jihar Neja, Alhaji Sani Idris Kutigi ya jagorance kungiyar zuwa gidansa domin gabatar masa da kofin da suka lashe a gasar kasa da aka gudanar a Kaduna kwanakin baya.
Tsohon Shugaban kasar ya yaba kokarin da kungiyar ta yi a gasar inda ya lashi takobin tuntunbar jama’a da wadanda yake ganin za su iya taimaka wa kungiyar don ta samu nasarar dauko Kofin Nahiyar Afirka a wannan karo maimakon zuwa ta uku a wakiltar kasar nan sau uku da ta yi a baya.
Shugaban kungiyar kuma tsohon dan Majalisar Wakilai Alhaji Sani Idris Kutigi a hira da wakilinmu ya ce hazakar da yaran suka nuna ne ya sa ya dauki nauyin kula da su a sansanin wasan a matsayin daya daga cikin gudunmawar da zai bayar na tallafa musu su samu tudun dafawa a fannin wasanni.
Alhaji Sani Kutigi ya ce sun zauna da shugabannin kungiyar don tsara hanyoyin da za su shawo kan matsalar da ake ganin za ta kawo cikas ga kungiyar kafin lokacin zuwansu Afirka ta Kudu.
Ya ce ganawar da suka yi da Gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello da Janar AbdulSalami Abubakar da cewa karin kaimi ne ga shugabanni da ’yan wasan.