Abdulsalami ya je ta’aziyyar mahaifiyar Yar’Adua a Katsina

Abdulsalami ya yaba wa ƙoƙarin Gwamna Radda na inganta harkar tsaro a Katsina.

Abdulsalami ya je ta’aziyyar mahaifiyar Yar’Adua a Katsina

Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya yi wa iyalan Yar’adua, Gwamnati da mutanen Jihar Katsina jajen rasuwar Hajiya Dada Musa Yar’adua.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ne, ya tarbe shi a Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.

A gidan iyalan Yar’adua, Janar Abdulsalami tare da Gwamna Radda da wasu manyan jami’an gwamnati, sun samu tarba daga Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua da wasu daga cikin iyalan mamaciyar.

Janar Abdulsalami ya yi addu’o’i ga mamaciyar kuma ya roƙi Allah Ya bai wa iyalanta haƙurin jure wannan rashi.

A lokacin da yake magana da ’yan jarida, Janar Abdulsalami ya yaba wa Gwamna Radda bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Katsina.

Ya bayyana cewa lokacin da Gwamna Radda ya hau mulki a 2023, kusan kashi biyu cikin uku na ƙananan hukumomi a jihar suna fuskantar barazanar tsaro.

Amma ya ce sakamakon jajircewar Gwamnan da dabarunsa, an samu zaman lafiya, wanda ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu, kuma hakan ya rage hatsarin fuskantar yunwa a jihar.

“Na gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da Gwamnan ya samu nasarar dawo da zaman lafiya a waɗannan yankuna, wanda ya sanya manoma komawa gonakinsu. Wannan zai taimaka wajen rage barazanar yunwa a jihar,” in ji Janar Abdulsalami.

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas

Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.80 — NBS