AbdulSamad Rabi’u ya zama mutum na biyu mafi arziki a Afirka

Rahoton ya ce Rabiu ya zarce attajirin Afirka ta Kudu, Johann Rupert wanda dukiyarsa ta ragu zuwa dala biliyan 17.9 a shekarar 2026.

AbdulSamad Rabi’u ya zama mutum na biyu mafi arziki a Afirka

Shugaban rukunin Kamfanin BUA Group, Abdul Samad Rabi’u kuma Attajirin ɗan kasuwar Najeriya, ya zama mutum na biyu mafi arziki a Afirka.

Rahoton ya ce Rabiu ya zarce attajirin Afirka ta Kudu, Johann Rupert wanda dukiyarsa ta ragu zuwa dala biliyan 17.9 a shekarar 2026.

A yanzu dukiyar Abdul Samad Rabi’u  ta haura dala biliyan 18.6, kamar yadda jerin masu kuɗi na Bloomberg Billionaires Index ya nuna.

Bloomberg ta kuma bayyana cewa Rabiu ya samu ƙarin arziki mafi yawa a Afirka bana, sakamakon bunƙasar kamfanoninsa na siminti, harkokin abinci da masana’antu.

Wannan sabon matsayin ya kuma sanya shi a bayan Aliko Dangote kaɗai, wanda har yanzu yake matsayin mutum mafi arziki a Afirka da dukiyar dala biliyan 34.4.