Abiin da ya ba ni sha’awa na fito takarar siyasa – Asiya Yauri

Hajiya Asiya Abdullahi Yauri,’yar shahararren dan siyasar nan Abdullahi Yalwa, ta nuna sha’awarta ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Dattawa daga mazabar Kebbi ta Kudu, a tattaunawarta da wakilinmu, ta bayyana dalilin fitowarta takara da irin gudunmawar da mata za su iya bayarwa a siyasar Najeriya: Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinki?Asiya Abdullahi Yauri: Na fito daga […]

Abiin da ya ba ni sha’awa na fito takarar siyasa – Asiya Yauri
Abiin da ya ba ni sha’awa na fito takarar siyasa – Asiya Yauri

Hajiya Asiya Abdullahi Yauri,’yar shahararren dan siyasar nan Abdullahi Yalwa, ta nuna sha’awarta ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Dattawa daga mazabar Kebbi ta Kudu, a tattaunawarta da wakilinmu, ta bayyana dalilin fitowarta takara da irin gudunmawar da mata za su iya bayarwa a siyasar Najeriya:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinki?
Asiya Abdullahi Yauri: Na fito daga karamar Hukumar Yawuri da ke Jihar Kebbi kuma an haife ni a ranar 16/4/1969 a Yawuri. Na yi firamare a St. Catherine’s Primary school, Makurdi a Jihar Benuwai lokacin mahaifina yana aiki a hukumar jiragen kasa a can, daga nan na koma Jihar Sakkwato na shiga sakandaren GGSS Illela na shekara biyu na koma ta Tambuwal. Bayan na kammala sai na wuce Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Birnin Kebbi na yi Difloma a aikin banki da kudi. A 1990 na yi aure, sai mijina ya wuce da ni kasar Ireland inda yake aiki, daga baya ya koma UK East Kent Hospitals Unibersity da ke Landan na yi jami’a na kuma yi aiki a Probation Centre Kent a Ingila.  A yanzu kuma na fito takarar kujerar Majalisar Dattawa daga mazabar Kebbi ta Kudu a karkashin Jam’iyyar PDP.
Aminiya: Me ya karfafa miki gwiwar fitowa takara?
Asiya Abdullahi Yauri: Na farko na girma a cikin siyasa domin bayan da mahaifina ya bar aiki ya shiga siyasa kuma ya zama fitacce a kasar nan, don haka na taso ina ganin mutane kullum a gidanmu ana gudanar da harkokin siyasa. Lokacin da aka kirkiro Jihar Sakkwato babana yana daya daga cikin kwamishinoni na farko da aka yi a jihar. Koda na tashi na ga yadda yake hulda da jama’a, wannan sai ya dada ba ni sha’awar siyasa. Don haka na shiga harkokin siyasa. Na biyu babbar matsalar da nake gani kullum idan na zo wannan mazaba da kuma Arewa baki daya, shi ne rashin ingantaccen ilimi ga yaran Arewa. Mahaifinmu ya cusa mana ra’ayin makaranta tun muna kanana, ya nuna mana cewa in ka yi karatu babu abin da ba za ka iya zama ba. Don haka ya matsa mana cewa sai mun gama makaranta kafin mu yi aure ko aiki. Addinin Musulunci bai hana neman ilimi ba, musamman ga mace domin idan mace ta yi karatu tana canja rayuwar iyali. Don haka babban abin da zan sanya a gaba idan Allah Ya sa na samu nasara shi ne wayar da kan al’ummarmu a kan muhimmancin ilimi da kuma bunkasa ilimi.
Aminiya: Daga lokacin da kika nuna sha’awar fitowa takara zuwa yanzu yaya karbuwarki a wurin al’ummar wannan mazaba take?
Asiya Abdullahi Yauri: Babu shakka al’ummar wannan mazaba sun karbe ni hannu bibbiyu. Sun dauke ni a matsayin ’yarsu ba tare da la’akari da cewa ni mace ce ko farkon shigowa siyasa ba, kuma ina son takarar Sanata wanda ba karamin abu ba ne musamman ga mu mata. Kuma mata da yawa sun fito suna cewa lallai suna son su ga abin da mace za ta yi a wannan mazaba. Mace Allah Ya yi mata tausayi, in aka ta shugabanci za a samu zaman lafiya, saboda ba za ta ce a je a yi fada ba.
Aminiya: Wace irin gudunmawa ce kike ganin mata za su iya bayarwa a siyasar Najeriya?
Asiya Abdullahi Yauri: Na farko shi ne, kowace mace ta tabbatar rajistarta na nan, kuma koyaushe aka zo sabuntawa ta tabbatar ta sabunta, wadda ba ta yi ba ta ta je ta yi rajista, a duk lokacin da aka fara bayar da rajista. Kuma idan an yi rajista in lokacin zabe ya zo ta je ta zabi wanda take so, wanda take ganin zai inganta mata rayuwa. Mata su guji siyasar kudi, domin in aka ba su kudi suka zabi mutum, in ya tafi ba su da damar da za su tuhume shi kan bai yi musu aiki ba. Amma in ka zabi mutum don cancanta don ya kyautata rayuwar garinku ta hanyar samar da hanyoyin mota da ruwa da makarantu da asibitoci da wutar lantarki da samar wa matasa aiki, kana da damar da za ka je ka tuhume shi. Kuma mata su sani cewa sun fi maza fitowa kada kuri’a domin akwai namiji mai mata hudu akwai mai uku ko biyu.
Aminiya: A karshe wane sako kike da shi ga al’ummar mazabarki?
Asiya Abdullahi Yauri: Ina kira ga al’ummar wannan mazaba su zauna lafiya, domin sai da zaman lafiya da hadin kai za a samu ci gaba. Kuma ina kira ga matan wannan mazaba su fahimci cewa a cikin wadanda suka nuna sha’awar takarar akwai mace ‘yar uwarsu. Mu mata muna da tausayi, muna jin kunyar a ce an zabe mu amma ba mu yi komai ba. Mu mata mu ne muke cikin wahala, don haka na fito ne domin na taimaka wa mata da kananan yara da al’ummar wannan mazaba gaba daya.