Abin boye na fitowa fili

Rahotannin da kafofin watsa labarai suka fi yayatawa a karshen makon jiya da farkon wannan mako shi ne na abin fallasar nan da wani limamin Kirista da Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya gayyato domin shiga tsakani a samu ’ya’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lid Da’awti wal jihad da ake kira Boko Haram su sako […]

Abin boye na fitowa fili
Abin boye na fitowa fili

Rahotannin da kafofin watsa labarai suka fi yayatawa a karshen makon jiya da farkon wannan mako shi ne na abin fallasar nan da wani limamin Kirista da Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya gayyato domin shiga tsakani a samu ’ya’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lid Da’awti wal jihad da ake kira Boko Haram su sako ’yan matan Chibok kusan 300 da aka ce sun sace daga makaranta yau kwana 144.
Baturen dan kasar Ostireliya mai suna Stephen Dabis an ce ya shafe wata hudu a kasar nan yana tattaunawa da wasu kwamandojin Boko Haram, har ya samu ganawa da wasu daga cikin ’yan matan.
Ya shaida wa duniya a karshen makon jiya cewa, cikin masu daukar nauyin kungiyar wajen samar mata da kudi da kayan aiki har da tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Shariff (SAS) da tsohon Hafsan Hafsoshin Sojan Najeriya Laftana Janar Azubuike Ihejirika, sai kuma wani babban ma’aikacin Babban Bankin Najeriya da bai ambaci sunansa ba.
Dukkan mutanen biyun da Stephen Dabis ya ambata sun musanta wannan zargi da ya yi musu, kuma sun ce zargin yana da alaka da siyasa. SAS ma har barazana ya yi cewa zai je har can kasar da Baturen ya yi wannan zargi domin gurfanar da shi a gaban kotu. Shi kuma Stephen Dabis ya ce yana jiransa, shi ne ma zai tarye shi a filin jirgin sama idan ya isa kasar!
Tabbas an dade ana zargin cewa matsalar Boko Haram, akwai lauje a cikin nadi, akwai manakisa, akwai kokarin kassara wani bangare na kasa akwai, akwai, akwa….
Da ma a baya wasu masan sun ce Boko Haram ta karkasu kasha-kashi; akwai Boko Haram ta mabiya marigayi Muhammadu Yusuf, akwai ta gwamnati/tsaro, akwai ta barayi. Ita kanta gwamnati ta ce akwai ta ’yan siyasa da galibi take jinginawa ga abokan hamayya.
Sai dai a wannan karo ne kawai wani fitaccen mutum ya fito ya shaida wa duniya sunan wasu fitattun mutane a Najeriya da yake zargi da hannu a lamarin Boko Haram.
Babban abin bakin ciki har zuwa shekaranjiya Laraba da nake rubuta wannan sharhi, Gwamnatin Tarayy ba ta ce komai kan wannan fallasa da Dabis ya yi ba, duk da cewa ita ta gayyato shi domin shiga tsakani.
Sananne ne cewa zai yi wuya a ce kafin Stephen Dabis ya bar kasar nan bai shaida wa gwamnati sunayen mutanen da ya zarga da hannu a harkar Boko Haram ba. Kuma idan haka ne me ya sa gwamnatin ta yi shiru har Dabis ya gaji ya yi fallasa bayan ya bar kasar nan? Me ya sa SAS ya koma PDP, bayan a daukacin rayuwar siyasarsa a jam’iyyar adawa yake?
Amsa wadannan tambayoyi za tab taimaka jama’a su gamsu cewa gwamnati tana da hannu ko ba ta da hannu a cikin lamarin Boko Haram.
Yadda ’yan Boko Haram ke rawar gaban hansti har suna kora jami’an tsaron kasar nan zuwa kasar Kamaru kuma suka kwace garuruwa masu girma irin su Damboa da Gwazo da Dikwa a Jihar Borno da kuma Gulani a Jihar Yobe, kuma suka tilasta sarakuna bakwai gudu daga masarautunsu tare da sanya dubban mutane yin gudun hijira zuwa Maiduguri da Damatruru da wasu jihohin makwabta da kasashen Kamaru da Nijar da Chadi, ya nuna cewa, kodai gwamnati na da wata manufa ta boye, ko kuma harkokin tsaron kasar nan sun gama susucewa ta yadda kowace irin karamar kasa tana iya kawo mana hari ta murkushe mu.
Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya yi kukan cewa mayakan Boko Haram sun fi sojan Najeriya da aka tura makamai masu inganci, amma mahukuntan soja suka ce atafau bah aka ba ne, har ma aka yi yunkurin a kore shi daga gwamna a nada kantoman mulkin soja. Gwamnan Adamawa Murtala Nyako ya yi zargin cewa akwai boyayyiyar manufa game da matsalar Boko Haram, inda ya zargi Shugaban kasa da hannun a lamarin, sakamakon da ya samu shi ne na rasa kujerarsa lamarin da ya tilasta shi gudun hijira zuwa waje domin tsira da rayuwarsa.
Yanzu ga abin da ake gudu yana ci gaba da faruwa, gwamnati ta ce ba za ta yi sulhu da Boko Haram ba, amma ta gaza samar da kayan aiki ga sojojinta domin su kare banagren Arewa maso Gabasna kasar nan.
 Yanzu kuma ga wannan Bature da gwamnati ta gayyato ya yi fallasa mai karfi irin amma gwamnati ta yi gum da bakinta? Me zai hana a yi zargin cewa da hannunta a cikin lamarin?
Wanin lokaci zuciyata takan yi kamar ta buga idan na kalli hoton dimbin ’yan gudun hijira da rikicin Boko Haram y araba da muhallinsu da masu daukar nauyin rayuwarsu. Nakan yi kamar in kwala kururuwa idan na ga yara a talabijin ko a shafukan jaridu suna wawason garin kwaki a sansanin ’yan gudun hijira! Nakan tambayi kaina shin zan so a ce dana ko ’yata ko matata dayansu ko dukkansu sun samu kansu a wannan hali?
Ina shugabannin da suke cewa suna wakiltar Arewa ne a cikin wannan gwamnati, shin kun sallamar da mu ne a yi ta halaka mu ana lalata mana dukiya, saboda jifan ya tsallake kanku?
Shin a cikinku ba wanda yake jin cewa gwamnati ko ma’aikatarsa ko hukumarsa ko sashinsa ko shi kansa ya gaza wajen sauke amanar da aka dora masa bari ya yi murabus ko za a samu wanda ya fi shi cancanta ya zo ya yi gyara?
Ga sarakuna kun ga dai yadda Shehun Dikwai da Sarkin Bama da na Gwoza da na Askira da na Uba da na Gujba da na Bara, suna ji suna gani yau ba su suke mulkin jama’arsu ba, su ma sun zama ’yan gudun hijira a wasu wurare. Sun tsallake fadojinsu yau ba su san halin da suke ciki ba!
Don haka idan shugabannin Arewa da ke cikin wannan gwamnati suka ci gaba da kame hannu da rufe baki suka zuba ido wannan lamari yana ci gaba saboda suna samun dukiya, to su ji tsoron abin da zai biyo baya! Tilas su dauki mataki kafin lamarin ya wuce tunani.
Ga Bature Stephen Dabis, muna yaba maka kan yadda ka yi wannan fallasa da ta tabbatar da kalaman Shugaban kasa cewa akwai ’yan Boko Haram a cikin gwamnatinsa, kuma suna cin abinci tare da ’yan Boko Haram! Ni dai gizago ko tantama ba na yi cewa gwamnati tana da hannun a lamarin Boko Haram, shi ya sa ta hana sojoji makamai ta ki tura wadatattun sojoji fagen daga, amma ta rika tura su wuraren zabe!