Abin da Buhari ya shaida wa Shugabar IMF

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta nemo wasu hanyoyi na tabbatar da bin dokoki don hana zurare kudin jama’a zuwa aljifan wasu kalilan tare da bin hanoyi mafiya nagarta da ake amfani da su a duniya domin kara samar wa Najeriya kudin shiga don magance matsalar da faduwar man fetur ke yi […]

Abin da Buhari ya shaida wa Shugabar IMF
Abin da Buhari ya shaida wa Shugabar IMF

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta nemo wasu hanyoyi na tabbatar da bin dokoki don hana zurare kudin jama’a zuwa aljifan wasu kalilan tare da bin hanoyi mafiya nagarta da ake amfani da su a duniya domin kara samar wa Najeriya kudin shiga don magance matsalar da faduwar man fetur ke yi a duniya.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da Manajan Daraktan Asusun Lamuni na Duniya (IMF) Misis Christine Lagarde ta ziyarce shi a fadar Shugaban kasa a Abuja, inda ya shaida mata cewa gwamnatinsa za ta kuma tilasta yin da’a da gaskiya da rikon amana a duk hukumomin tara kudin shiga na Gwamnatin Tarayya.
Wata sanarwa daga Kakakin Shugaban kasa, Mista Femi Adesina wadda ta bayyana haka ta ruwaito Shugaba Buhari yana shaida wa Lagarde cewa: “Ba mu dade da yanke shawarwari kan kasafin kudi ba, bayan makonni muna duba bukatun kasar nan da dama da kuma faduwar tattalin arziki saboda faduwar farashin man fetur da illar da ake ji zai yi wa tattali arziki.”
Ya kara da cewa: “Muna aiki wurjanjan kuma a matsayin kasafin na hanyar ci gaba, za mu yi iyakan kokarinmu don tabbatar da mun samu tsallake siradin faduwar tattalin arzikin. Kuma mun gaya wa shugabanni sassa da hukumomin gwamnati cewa za mu rika zuba ido wajen ganin suna yin cikakkien bayani kan duk kudin da ya shiga asusunsu.”
Shugaban kasar ya ce, Gwamnatin Tarayya tana duba yadda take kashe kudi wajen gudanar da al’amuranta kuma ta umarci shugabannin sassa da hukumomin gwamnati su rage kudin da suke kashewa wajen ayyukan ofis. Sai ya ce gwamnatin tana maraba da duk wasu shawarwari da tallafi da Asusun IMF zai ba ta domin cin gajiyar dimbin albarkatun tattalin arzikin da ke jibge a Najeriya don bunkasa ta.
A jawabinta Misis Lagarde ta ce Asusun IMF zai taimaka wa Najeriya waje tushe hanyoyin zurare kudin gwamnati tare da bankado kudaden kasar nan da aka sace da kuma sake fasalin hanyoyi tara kudaden haraji.
Ta ce Najeriya tana da dukkan abin da ake bukata don samun nasara kan matsalolin da faduwar darajar man fetur zai haifar ba tare da ta nemi tallafin kudi daga Asusun IMF ba.
Misis Lagarde tun farko ta bayyana abubuwan da suka tattauna da Shugaba Buhari inda ta ce ba ta zo Najeriya don yarjejeniyar ba kasar nan bashi ba. “Ban zo nan don kulla bashi ba, domin Najeriya ba ta bukatar wani sabon shiri daga Asusun IMF,” inji Lagarde.