Abin da fursunoni suka fi son karantawa a Jami’ar NOUN – Shugaban Jami’a

Fursunoni a sassan kasar nanm suna da wasu kwasa-kwasai da aka gano sun fi son su karanta a Jami’ar Karatu Daga-Gida (NOUN), inda dalibai biyu ne kacal daga cikin 354 daga cikin fursunonin da suke karatu a yanzu suke karanta digiri a darasin da ba ya da alaka da laifuffuka da shari’a. Shugaban Jami’ar Farfesa […]

Abin da fursunoni suka fi son karantawa a Jami’ar NOUN – Shugaban Jami’a

Fursunoni a sassan kasar nanm suna da wasu kwasa-kwasai da aka gano sun fi son su karanta a Jami’ar Karatu Daga-Gida (NOUN), inda dalibai biyu ne kacal daga cikin 354 daga cikin fursunonin da suke karatu a yanzu suke karanta digiri a darasin da ba ya da alaka da laifuffuka da shari’a.

Shugaban Jami’ar Farfesa Abdalla Uba Adamu ne ya bayyana haka, inda ya ce fursunonin dalibai biyu suna karanta digiri ne a kan darussan tauhidi, yayin da saura 352 suke nazari kan Harkokin Laifuffuka da Tsaro da Zaman Lafiya da Rikice-Rikice duk da suna warwatse ne gidajen kurkuku da ke sassan kasar nan.

Shugaban Jami’ar ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin mawallafi da kuma jami’an kamfanin buga jaridun Blueprint a hedkwatar jami’ar da ke Abuja.

Ya shaida wa ayarin maziyartar cewa, yanayin girman jami’ar wadda ta kasancewa ita ce kadai jami’ar da ake karatu daga gida a Afirka ta Yamma, wanda hakan ya sa take da cibiyoyin karatu 78 a sassan kasar nan.

Ya ce, baya ga cibiyoyin karatun 78, Jami’ar NOUN tana da cibiyoyi a uguwanni 19 da kuma cibiyoyin kwarewa a wuraren da suka hada da Hukumar Shigi-da-Fici da barikokin ’ya sanda da na soja da kuma gidajen kurkuku.

“Amma cibiyoyin karatu da muka fi yin alfahari da su, su ne na gidajen kurkuku. Muna da furusnoni 354 da suke karatu a Jami’ar NOUN, kuma daga cikinsu biyu ne kacal suke karanta wasu darussa na daban, yayin das aura suke karanta daruss kamar Tsaro da Zaman Lafiya da Nazarin Magance Rigingimu ko kuma harkokin shari’a, saboda suna haba-haba su fahimci tsarin shari’a wanda ya kawo su gidajen kurkuku,” inji Farfesa Adamu.

Shugaban Jami’ar ya kuma dauki lokaci yana bayani kan dimbin sauye-sauyen da yake yi a jami’ar wadanda ya ce suna dora ta a hanyar dogaro da kanta a makomar jami’ar ta nan gaba, maimakon yadda lamarin yake a baya.

“Nasarorin da muka samu a fili suke, kuma karfin gwiwa da tsayuwar dakarmu ta cin gashin kanmu sun sa mun yi fice,” inji shi.

Ya kara da cewa, samun dalibai dubu 400 da suka yi rajista, yayin da dubu 150 suke kan yi karatu, sannan dubu 95 yanzu haka suke daukar jarrabawa, ya sa jami’ar ta kasance jagorar samar da ilimi daga gida ba ma a nan Najeriya kadai ba, a daukacin yankin Afirka ta Yamma.

Da ya juya kan jaridun Blueprint tun fara bayyanarsu shekara shida da suka gabata, Shugaban Jami’ar ya ce, ya yaba irin dangantakar da ke tsakanin jami’ar da kamfanin, inda ya tabbatar wa shugabannin kamfanin ci gaba da hada gwiwa a tsakaninsu.

Tun farko a jawabin mawallafin jaridar Blueprint Mohammed Idris ya ce, sun je jami’ar ce don nuna goyon baya ga ‘gagarumin ci gaban’ da jami’ar take samu tun nada Shugaban Jami’ar.

Ya taya Shugaban Jami’ar murna kan nasarorin da ta samu a kwanakin baya inda Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da gyare-gyare ga Dokar Jami’ar NOUN wanda hakan zai ba daliban da suka kammala jami’ar damar halartar shirin yi wa kasa hidima da kuma shiga Makarantar Aikin Lauya.

“Muna taya ka murna yallabai kan wannan nasara da kuka samu a Majalisar Dokoki ta kasa ta amincewa da dokar da ta kyale daliban da suka halarci Jami’ar NOUN su halarcin shirin yi wa kasa hidima da kuma yin karatu a Makarantar Lauyoyi ta kasa, wannan babba kuma gagarumar nasara ce,” inji shi.

Malam Idris ya yi amfani da ziyarar wajen shaida wa Shugaban Jami’ar cewa jaridar karshen mako ta Blueprint za ta fara fitowa a mako farko na watan Satumba mai zuwa.