Abin da gwamnatin Bauchi mai zuwa za ta mayar da hankali a kai
Zai zamo bidi’ah a tsaya nanata cewa, an tafka kura-kurai a gwamnatin Bauchi mai wucewa, don haka abin da ya fi dacewa a nusar da gwamnati mai zuwa kan alkiblar da ya kamata ta fuskanta don kada a maimaita wadancan kura-kurai. Jihar Bauchi jiha ce ta ma’aikata, ma’aikatan ma na gwamnati babu masana’antu ko kamfanoni, […]
Zai zamo bidi’ah a tsaya nanata cewa, an tafka kura-kurai a gwamnatin Bauchi mai wucewa, don haka abin da ya fi dacewa a nusar da gwamnati mai zuwa kan alkiblar da ya kamata ta fuskanta don kada a maimaita wadancan kura-kurai.
Jihar Bauchi jiha ce ta ma’aikata, ma’aikatan ma na gwamnati babu masana’antu ko kamfanoni, don haka wajibi ne gwamnatin Sanata Bala Mohammed mai zuwa ta mayar da hankali wajen biyan albashi da fansho da ciyar da ma’aikata gaba da biyansu sauran hakkokinsu da kuma bullo da hanyoyin samar da ayyukan yi.
Na biyu gwamnatin ta bullo da hanyoyin tallafa wa manoma da ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu da mata da matasa, kuma a tabbatar tallafin yana isa gare su kai-tsaye. Kada a maimaita irin na baya da tallafin ke karewa a hannun wadansu jami’an gwamnati da ’yan koren siyasa.
Samar da ruwan sha musamman a manyan biranen jihar, misali Bauchi wanda shi ne fadar jihar akan samu unguwannin da sukan shafe mako biyu ba su ga digon ruwa a famfo ba a yanzu haka. Kuma saboda wadatar ruwa a akasarin jihar a baya, da wuya ka ga mai sayar da ruwa yana yawo da shi, wanda hakan ya sanya jama’a a cikin kunci, fiye da lokacin da babu wadatar ruwan domin suna kula da rijiyoyinsu ba kamar yanzu da babu akasarin wadannan rijiyoyi ba.
Sannan a kula da tsabtar muhalli musamman kwashe sharar da ake jibgewa a kan titunan fadar jihar wato garin Bauchi. Kwanan nan dai mun ji yadda cutar kwalara ta barke a birnin, kuma kowa ya san kazanta tana taka rawa wajen yaduwar cutar.
Sannan akwai bukatar gwamnati mai zuwa ta mayar da hankali wajen giggina hanyoyin mota, na san Gwamna mai jiran gado ya ziyarci sassan jihar nan da dama ya ga yadda ake fama da matsalolin hanyoyi musamman a shiyyar da ya fito wato Bauchi ta Kudu.
Wajen samar wa matasa aikin yi za a iya farfado da wasu hukumomi da aka rusa a baya kamar na samar da tsaro da na kwashe shara. Su kuma iyaye mata ya kamata a yi koyi da Jihar Jigawa, inda baya ga tallafa musu da kananan rance ko kyautar jari, ana iya sayen awaki a rika ba su mace da miji guda bibbiyu idan suka shekara su kawo madadinsu a bai wa wadansu. Ta wannan hanya za a iya kawar da talauci sosai musamman a yankunan karkara, ta yadda za a rabu da kananan sace-sace ko kwararar matasa zuwa birane da sunan neman aikin yi inda a karshe suke lalacewa.
Tabbas Gwamna mai zuwa Sanata Bala Mohammed Kauran Bauchi yana da kalubale mai yawa a gabansa, kuma ga shi jihar ba kudin shiga mai yawa take da shi ba, kamar Babban Birnin Tarayya inda ya yi Minista, amma duk da haka idan ya tsaya a kan gaskiya ya sanya ido wajen ganin ana tafiyar da dukiyar cikin gaskiya da rikon amana, insha Allahu zai samu nasarar da ba a zata ba.
Alhaji Gambo Bababa, Shugaban Kungiyar Masu Sarrafa Magungunan Gargajiya ta Jihar Bauchi, 08023622651, 07032096837