Abin da ka shuka shi za ka girba
“Kada ku bata; ba a yi wa Allah ba’a ba: gama iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe. Gama wanda ya shuka ga jiki nasa, daga wurin jiki za ya girbe ruba; amma wanda ya shuka ga Ruhu, daga wurin Ruhu za ya girbe rai na har abada. Kada mu yi kasala […]
“Kada ku bata; ba a yi wa Allah ba’a ba: gama iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe. Gama wanda ya shuka ga jiki nasa, daga wurin jiki za ya girbe ruba; amma wanda ya shuka ga Ruhu, daga wurin Ruhu za ya girbe rai na har abada. Kada mu yi kasala kuma cikin aikin nagarta: gama in lokaci ya yi, za mu girbe in ba mu yi suwu ba.” (Galatiyawa 6:7– 9).
Kowane manomi ya sani cewa duk abin da ya shuka a gonarsa shi ne za ya girbe; idan ka shuka gyada, babu shakka gyada ne za ka girbe, idan doya ne ka shuka, ba za ka taba girbe gwaza daga gonar ba. A cikin wannan koyarwar da za mu yi idan Allah Ya yarda, za mu duba irin shukar da Allah Yake magana a kai. Mafarin ayar da muka karanta tana cewa, ba a yi wa Allah ba’a ba, gama iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe, shuka iri-iri ce, yadda mutum ke rayuwarsa zai iya zama kamar shuka ne, a cikin Littafin Misalai 22:8; maganar Allah na cewa “Wanda ya shuka mugunta za ya girbe bala’i, Sandar fushinsa kuma za ta kasa.”
Yawancin lokaci mutane sukan manta cewa duk abin da suke yi a yanzu zai sake dawowa gare su, ba lallai nan take ba, amma babu shakka lokacin na zuwa. Ko aikin nagarta ne ko kuwa aikin mugunta, kowane iri ne ma akwai sakamakonsa, masu iya magana sun ce ‘ramin mugunta; a tona shi gajere,’ dalilin kuwa shi ne mai yiwuwa kai ne za ka fada a ciki.
A inda muka duba yanzu, Allah Yana cewa duk wanda ya shuka mugunta, za ya girbi bala’i; abu na farko da ya kamata kowa ya yi la’akari da shi, shi ne aikata mugunta kan haifar da bala’i. Yawancin lokaci mutane suna ganin kamar idan suka yi wa wani mugunta, sun cuce shi ne, amma ba su sani cewa kansu suke cuta ba, gaskiya komai dadewa; lokaci na zuwa da dole abin da ka aikata zai kunno kai. Shi ya sa wani lokaci muguntar da ka yi yau, sakamakonta zai iya zuwa ne a zamanin ’ya’yanka da jikokinka, haka idan ka shuka nagarta. Dole ne mu yi hankali da yadda muke yin wadansu abubuwa a yau da kullum. Zai zama wauta ga kowane mutum ya yi tsammanin girbar abin da bai shuka ba.
Ina so mu kawo hankula ga wannan koyarwa – mu duba aya takwas har yanzu; “Gama wanda ya shuka ga jiki nasa daga wurin jiki za ya girbe ruba……..” mene ne ma’anar shuka ga jiki? Mu gane cewa ba maganar lura da jikinmu ne muke yi ba; ko kuwa sayen sutura domin kyautata rayuwarka cikin wannan duniya ba ne; amma abin nufi a nan shi ne duk wanda yake son jikinsa kawai, kuma duk abin da yake yi; yana kaunar kayan duniyar nan sosai, sha’awar kayan duniya ta cika masa zuciya har ya kai ga matsayin da ba ya da lokaci domin yin ibada, ba su da lokacin bauta wa Allah, suna nan kamar mutanen da Allah Ya yi magana a kansu cikin Littafin Yohanna ta Fari Sura ta Biyu, aya ta 15 zuwa 16, (1Yohanna 2:15–16) da take cewa “Kada ku yi kaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya. Idan kowa ya yi kaunar duniya, kaunar Uba ba ta cikinsa ba. Gama duk abin da ke cikin duniya da kwadayin jiki da sha’awar idanu da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne.”
Akwai mutane da yawa da suka sa ransu bisa kayan duniya, kwadayin jiki, wato neman su zama cikin wadanda ake ji da su bisa ga ra’ayin mutum, babu ruwansu da maganar Allah balle yi masa biyayya; wadansu kuwa sun sa kansu a cikin siyasa, suna neman matsayin cikin wannan duniya na shugabanci; ina so mu gane cewa ba laifi ba ne mutum ya shiga siyasa, ba laifi ba ne mutum ya samu kudi ya zama mai arziki a wannan duniya, gaskiyar ita ce Allah Yana so mu yi arziki, kuma Shi ne Yake da ikon ba da arziki ga kowa yadda Ya so, amma idan mutum ya ki bin shirin Allah domin rayuwarsa, ya kuma shiga neman kayan duniya domin ya cimma burinsa, babu shakka zai shiga wani yanayi da a karshe shi da kansa ba zai ji dadi ba. Shuka ga jiki zai sa ka girbe ruba – rubabben abu ba ya da kyau ko kadan, akwai shi da wari; ba ya da amfanin komai, a karshe kuwa zubar da shi za a yi. Babu kayan duniya guda daya da zai dauwama, komai da ke doron kasa ko ba dade ko ba jima zai lalace; tsutsa za su iya cinyewa; ko kuwa ya yi tsatsa, ko kuwa barayi za su iya sacewa. Wauta ce ga kowane mutum ya kafa begensa bisa kayan duniya domin ba za mu iya rike su har abada ba. Abu daya da zai dauwama shi ne ranmu. Domin za mu je gaban Allah Madaukakin Sarki domin Ya shar’anta mu; kuma kowa ya karbi sakamakon yadda ya yi rayuwa cikin wannan duniya, ba domin kudin da yake da shi ko ba shi da shi ba, zuciyarmu ce Allah Yake dubawa. Komai yawan kayan duniya da kake da shi a yau, ba zai yi amfani ba a wancan lokaci ba. Akwai mutuwa ta biyu wadda ita ce rabuwa da Allah na har abada. Wane irin shiri ne kake yi domin saduwa da Allah? Yaya matsayinka gaban Yesu Kiristi?
Abu na biye shi ne shuka cikin Ruhu!! A wannan wuri ba maganar ruhunka ba ne Littafi Mai tsarki yake nufi; amma Ruhun Allah ne, abin nufi; mutum ya yi amfani da duk dukiyarsa domin bisharar ceto, domin yada maganar Allah, yana kuma taimaka wa masu wa’azin ceto, hanunsa a sake domin tallafa wa masu bin Yesu Kiristi. Yana ci gaba da yin abin da Allah Ya sa cikin hannunsa, duk lokacin da muka kasa kunne ga muyar Ruhu Mai tsarki; muka kuma yi biyayya ga umarninsa, shuka ne muke yi cikin Ruhu kuma lokacin girbi na zuwa ba da dadewa ba. A cikin Littafin Galatiyawa maganar Allah na cewa “Amma ’yan Ruhu kauna ne, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa, irin wadannan babu shari’a a kansu” (Galatiyawa 5:22–23).