Abin da ke faruwa a tsakanin Amal Umar da ’yan sanda
Ya kamata mu riƙa adalci. dan ’yar fim ce sai me? Saurayi ba ya kashe wa budurwarsa kudi ne?
A makon jiya ne wani faifan bidiyo ya karade kafofin sadarwa na zamani, inda a ciki Kakakin Rundunar ’Yan sandan Shiyya ta Daya da ke Kano, CSP Bashir Muhammad yake bayanin yadda rundunar ’ta gabatar da jaruma Amal Umar a kotu bisa zarginta da ba dan sanda cin hanci.
Aminiya ta ruwaito a makon jiya cewa an gurfanar da fitacciyar jarumar ce a gaban Kotun Majistare da ke Gyadi-Gyadi a Kano, kan zargin yunkurin ba wani dan sanda mai suna ASP Salisu Bujama, da ke aiki a Shiyya ta Daya ta rundunar da ke Kano cin hancin Naira 250,000.
- Kotu Ta Tsare Matar Da Ta Watsa Wa Mijinta Ruwan Zafi
- Fasto mai wa’azi da macizai ya tsallake rijiya da baya
Mai gabatar da karar ya ce Amal ta yi yunkurin ba da cin hancin ne domin hana binciken ’yan sanda kan zargin saurayinta da almundahanar kudi.
A ciki ya ce, “Wata jaruma ’yar wasan Hausa wadda aka fi sani da Amal Umar mai shekara 24, an gurfanar da ita a gaban kotu domin yunkurin bayar da cin hanci da ta yi ga ASP Salisu Bujama wanda yake bincike a kan wani batu na damfara ta Naira miliyan 40 da saurayinta ya yi wa wani Alhaji Yusuf Adamu.”
Wannan na zuwa ne, bayan da Yusuf Adamu ta hannun lauyansa ya shigar da korafi ga Mataimakin Sufeto Janar Umar Mohammad Sanda, inda yake zargin saurayin jarumar da yin sama-da-fadi da kudin da ya kai Naira miliyan 40 da sunan kasuwanci.
Korafin da aka shigar ya sa ’yan sanda gudanar da bincike, inda suka gano cewa saurayin jarumar ya tura mata Naira miliyan 13 a asusun ajiyar bankinta.
A cewar Kakakin ’Yan sandan, an gayyaci jarumar domin amsa tambayoyi daga bisani kuma aka bayar da belinta, sai dai an hana ta fita daga wata mota da ake zargin saurayinta ne ya saya.
Idan ba a manta ba, a watan Nuwamban bara jarumar ta nemi Babbar Kotun Jihar Kano da ke Miller Road ta hana ’yan sanda kama ta da kuma bincikar ta.
Jarumar ta hannun lauyarta Barista Adama Usman, ta yi karar Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sanda mai kula da Shiyya ta Daya da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano da dan sanda mai bincike a ofishin Shiyya ta Daya.
Lauyar ta ce jarumar ta yi haka ne sakamakon zargin da wani saurayinta mai suna Ramadan ya yi mata na cin kudin wani abokin kasuwancinsa.
Asalin yadda maganar ta faro
Asalin maganar kan wani saurayinta ne mai suna Ramadan wanda ake zargi da kashe kudin da abokinsa ya ba shi domin su yi kasuwanci.
A watan Nuwamban ne Barista Yusuf Dan Sulaiman ya nemi kotun ta shigar da Amal cikin wadanda ake kara.
“Wanda nake wakilta mai suna Alhaj Yusuf Adamu ya ba saurayin Amal Naira miliyan 40 da niyyar za su yi kasuwancin wayoyin hannu.
“Amma har zuwa yanzu babu labarin kasuwancin, don haka muka nemi ya dawo da wadannan kudi lamarin da ya gagara. Hakan ya sa muka nemi ’yan sanda su shiga maganar,” in ji shi.
Barista Dan Sulaiman ya ce, lokacin da aka nemi kudin shi ne Ramadan ya bayyana cewa, ya saya wa budurwarsa Amal motar Naira miliyan biyar, ya kuma kama mata shago tare da zuba mata kayayyaki na miliyan biyar don yin kasuwanci.
Sannan ya ba mahaifinta Naira miliyan uku don ya biya wani bashi da ake bin sa.
Baya ga wasu kudade da ya ce ya tura wa jarumar ta asusun bankinta a lokuta daban-daban.
Aminiya ta gano cewa bayan da ’yan sanda suka samu wadannan bayanai ne, suka kwace motar jaruma Amal tare da ci gaba da bincikar ta kan wadancan kudade.
Soyayya ta haɗa mu da shi — Amal Umar
A wata hira da Amal ta yi da Hadiza Gabon ta ce, “Mutumin nan ya so ya aure ni, iyayena sun sani, wadanda suke kusa da ni sun sani, kuma kafin in fara kula shi, sai da na binciki kasuwancinsa, kuma ya bayyana min.
“Da ya zo Kano, sai ya rika saya wa mata filaye da mota da wayoyi, sai bayan da muka fara maganar aure sai na gane haka, shi ne sai muka rabu.
Bayan mun rabu sai zuwa wani dan lokaci aka ce wai ana nemana na ci kudi, ya yi wa babana kaza ya yi min kaza.
“To ai idan kana tare da budurwa za ka yi mata alheri, kuma maganar aure ce.
“Ya zo gidanmu, dole zai yi min alheri, amma ba maganar da ake fada ba ce.
“Kuma ya tambaye ni kuɗi bayan ya samu matsala, sai ya ce harkarsu ta Kirifto ce, ina kuma ba shi.
“Ya ɓoye asalin yadda yake yi, amma ashe yadda yake yi shi ne idan ka sa Naira miliyan 100, za a dawo maka da miliyan 200.
“Sai mutane suka riƙa sa kuɗi, da farko mutane sun samu kudi, daga baya kuma kudin wasu ya narke.
“Lokacin ni ban sani ba, abin da na sani kawai yana kasuwanci da yawa.
“Daga baya na riƙa zuwa ina ganinsa ina riƙa shiga masa duk da ba ma tare.
“A lokacin ma na ce masa tunda ba ni da kudi sosai, kuma ina so in taimake shi, zan sayar da motata in ba shi kudin.
“Sai ya ce ba sai na sayar da motata ba. Na riƙa ba shi kuɗi kamar Naira 500 haka zuwa kasa, har ya kai yana tambayar dubu 20 ma.
“Kawai a ƙarshe sai na ji ana nemana wai na ci kudi saboda watakila a cikin ’yan matan ni ce ya zo gida, sannan ni ’yar fim ce, ana tunanin za a samu kudi a wajena.
“Kuma asali ba shi ya kai ni kotu ba, ni na kai shi kotu saboda ana neman a alakanta ni cewa tare muke yi,” in ji ta.
Abin da ’yan Kannywood ke cewa
Aminiya ta zagaya shafukan ’yan Kannywood domin ganin wainar da suke tuyawa, inda kusan dukkan ’yan masana’antar suka nuna goyon bayansu ga jarumar.
Wadda ta fi shiga maganar ita ce Mansurah Isa, inda ta rubuta cewa, “Abin da ya kamata ku sani a kan batun Amal Umar da ’yan sanda. Naira biliyan 4 ake nema a wajen mutumin.
“Dan Kirifto ne, ya ci kudin Kirifto. Ba a lokaci ɗaya ya saka mata Naira miliyan 13 ba.
“Sun fi shekara suna tare, sannan a shekara ɗayan nan ne harkar kuɗin da ya wakana a tsakaninsu shi ne Naira miliyan 13.
“Akwai wanda wannan mutumin ya tura wa Naira miliyan 100 da 200 da sauransu, ba a kama su ba, ba a kwace musu mota ko wani abu ba, wai sai wacce yake bai wa dubu 500, miliyan 1 da saurasu.
“Don haka ku yi wa kanku adalci, ya kamata a kama Amal ko a kwace mata mota a wannan batun?”
“Sannan har an sa musu ranar aure fa, yana zuwa shagonta sayen kaya, duk kudin nan ne in aka haɗa ya kai miliyan 13.
“Mu a matsayinmu na Musulmai, mu rika adalci a duk abin da za mu ce ga wani, bai kamata ku yi zagi, sharri a kan abin da ba ku sani ba.
“Idan ’yar fim ce sai me? Saurayi ba ya kashe wa budurwarsa kudi ne?
“In saurayinki ya zo shagonki sayen kaya, za ki ce ba za ki sayar masa ba don kina tsoro za a ce ya ba ki kudi?
“Akwai manyan-manyan harkokin kuɗi da wannan mutum ya yi, wadanda suka fi Naira miliyan 100 a wasu asusun bankin, ba a kama su ba.
“Sannan sun yi amfani da Amal ne kawai sun ga ba ta da laifi kuma za ta fi saukin bata wa suna.
“Don haka masu jin dadin hakan ya faru da ita, ku je ga ku ga duniya nan, wanda suke mata kyakkyawar fata kuma, Allah Ya tsare ku da sharrin mutane, hukuma da duniya, amin.”