Abin da ke haddasa wahalar mai a Najeriya – NNPC
A ranar Talatar da ta gabata ce Kamfanin Mai na kasa (NNPC) ya bayyana cewa yana matukar kokari domin ganin an daidaita farashin man fetur a kan Naira 145 kowace lita a kowane gidan mai, amma masu hada-hadar mai ta bayan fage na y wa shirin kafar ungulu. Shugaban Kamfanin NNPC, Dokta Maikanti Baru ne […]
A ranar Talatar da ta gabata ce Kamfanin Mai na kasa (NNPC) ya bayyana cewa yana matukar kokari domin ganin an daidaita farashin man fetur a kan Naira 145 kowace lita a kowane gidan mai, amma masu hada-hadar mai ta bayan fage na y wa shirin kafar ungulu.
Shugaban Kamfanin NNPC, Dokta Maikanti Baru ne ya bayyana haka ga Shugaban Hukumar Kwastam, Kanar Hameed Ali (mai ritaya), lokacin da ya kai ziyara ofishinsa a Abuja domin hada gwiwa da hukumar a yi maganin masu fasa-kwaurin albarkatun man fetur.
Maikanti Baru ya ce duk da cewa farashin man fetur a Najeriya ne mafi karanci, idan aka yi la’akari da yadda ake sayar da shi a sauran kasashen Afirka ta Yamma, amma masu fasa-kwauri suna amfani da wannan dama wajen fitar da tankokin man da aka loda musu, domin kaiwa wasu gidajen mai da ke iyakar kasashen Nijar da Ghana da Benin suna sayarwa.
Kuma ya dora alhakin ga ’yan kasuwar man fetur masu zaman kansu, yana mai cewa shigar da mai ta wata hanya da kuma fasa-kwauri, na kawo cikas ga samar da isasshen man fetur a Najeriya. “kara kudin man fetur a kasuwar mai ta duniya da yadda kudinsa ke hauhawa sakamakon shigowa da shi daga waje akai da kuma tsadarsa a wasu kasashen da ke makwabtaka da mu na cikin dalilan karancinsa. Najeriya tana sayar da man fetur a kan Naira 145 kowace lita, yayin da Ghana ke sai da shi Naira 311, sai Togo Naira 308, Benin tana sayarwa Naira 292.8, inda Nijar ke sai da shi a kan Naira 367, sai Chadi, Naira 326.35 da kuma Kamaru kan Naira 400. Kuma ana samu karuwar masu amfani da man fetur a Najeriya saboda ana amfani da kasa da lita miliyan 30 a kowace rana, daga nan kuma sai ya karu zuwa lita miliyan 50 a kowace rana, daga nan sai aka kai lita miliyan 84.2,” inji shi.