Abin da ke ƙara ta’azzara adawa tsakanin Davido da Wizkid

Ana ganin cewa dai Davido da Wizkid su ne mawaƙa biyu mafiya shahara a nahiyar Afirka.

Abin da ke ƙara ta’azzara adawa tsakanin Davido da Wizkid

A cikin ’yan kwanakin nan, maganganu a kan fitattun matasan mawakan Kudancin Nijeriya guda biyu, wato Wizkid da Davido ne suka fi mamaye kafofin sadarwa.

Mawakan biyu sun dade suna adawa da juna, inda da zarar sun shirya, ana tunanin komai ya wuce sai kuma su koma gidan jiya.

Aminiya ta ruwaito yadda ake yawan samun sabani a tsakanin jaruman Masana’antar Kannywood, inda wasu suke ganin tamkar shi ne yake hana masana’antar samun ci gaba.

Manyan mawaƙan biyu na da miliyoyin mabiya a faɗin duniya kuma dama an daɗe ana kallon su a matsayin waɗanda ba su ga-maciji da juna.

Yawancin masu son waƙoƙin Nijeriya na alaƙanta kansu da ko dai goyon bayan Davido ko kuma Wizkid.

A ranar Litinin da daddare ne cacar-baki ta kaure tsakanin manyan mawaƙan bayan wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun buƙaci Wizkid ya saki sabuwar waƙa kamar yadda Aminiya ta kalato daga BBC.

Daga nan ne Wizkid ya mayar da martani ta hanyar wallafa wani bidiyon da aka riƙa yaɗawa a baya, inda a cikin bidiyon aka nuna wani mutum ya durƙusa yana neman alfarma daga wurin wani da ba a san ko wane ne ba.

Wizkid ya ce, idan masoyansa za su iya roƙon shi kamar yadda mutumin ke roƙo a cikin bidiyon, to zai saki sabuwar waƙa.

A baya masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi zargin cewa Davido ne mutumin da aka gani yana roƙon alfarma a cikin bidiyon, sai dai Davido ɗin bai ce komai ba game da wannan zargi.

Da yammacin ranar Litinin ne Davido ya mayar wa Wizkid martani, inda ya ce ba zai “ɓata lokacinsa” kan “wani wanda tauraruwarsa ta dusashe bayan an yi ƙoƙarin farfado da ita a ‘yan shekarun da suka gabata ba”.

Wannan lamari ya sa mutane na ta tofa albarcin bakinsu a shafukan sada zumunta da kuma a fili.

Yanzu haka dai magoya bayan mawaƙan biyu na ci gaba da musayar kalamai domin kare gwarazan nasu.

Ana ganin cewa dai Davido da Wizkid su ne mawaƙa biyu mafiya shahara a nahiyar Afirka.

Dukkaninsu sun lashe lambobin yabo na bajinta a ɓangaren waƙa kuma sun yi haɗaka da shahararrun mawaƙan duniya kamar Drake da Chris Brown da Nicki Minaj.

Tags