Abin da ke sa matasa shiga ISIS da Boko Haram – Limamin SMC

Sheikh Saidu Abubakar Muhammad shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a na Kwalejin  Sardauna (SMC) Kaduna. Ya yi karatun allo, sannan ya yi na boko. Yanzu haka yana karatun digiri na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Aminiya ta tattauna da shi domin jin dalilan da ke sanya matasa suna shiga kungiyar Boko Haram […]

Abin da ke sa matasa shiga ISIS da Boko Haram – Limamin SMC

Sheikh Saidu Abubakar Muhammad shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a na Kwalejin  Sardauna (SMC) Kaduna. Ya yi karatun allo, sannan ya yi na boko. Yanzu haka yana karatun digiri na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Aminiya ta tattauna da shi domin jin dalilan da ke sanya matasa suna shiga kungiyar Boko Haram da kuma ISIS. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Mene ne laifin Malamai da ke sanya matasa suna shiga kungiyar ISIS da Boko Haram suna yin kunar bakin wake?
Liman Sa’idu: Annabi ya ce akwai masu da’awa masu kira da cewa su ne malamai amma suna kira ne daga kofar Jahannama. Ya ce ba ya ji mana tsoron ko mu kafirta daga baya, amma ya fi ji mana tsoron munafiki mai kaifin harshe wanda zai yi wa Allah karya ya ce Allah ne Ya ce a yi abu, amma karya ne, don zai gaya wa mutane da ba su da ilmi idan sun ba shi amanar sai ya kai su ga hallaka. Tura matasa suna kashe jama’a yara da tsoffi da mata a kasuwa ko banki, wannan bala’i ne. Yaran ba su sani ba, wadannan mutane ‘yan siyasa suke amfani da su a kan wata manufa da za a ce a shiga aljanna. Ya kamata a ji tsoron Allah a daina yin karya da addini. An ce Maitatsine a Kano ya ce wanda duk ya riga shi mutuwa cikin mabiyansa, zai shiga aljanna, wanda bai riga shi ba ba zai shiga ba. Wannan araya ta sa suka yi ta kunar bakin wake suna hallaka. Wannan abu ne mai muni kwarai.
Aminiya: Me ya kamata iyaye su yi don ‘ya’yansu kar su zama masu shiga ISIS da Boko Haram?
Liman Sa’idu: Muna kara kira ga mutane su kara kula da ‘ya’yansu, don wata dabi’a da mutanen arewacin kasar nan ke yi ita ce barin yara ‘yan shekara hudu ko biyar ko shida suna yawo da sunan almajiranci. Wani yaron a gidansu da kyar mahaifiyarsa take yi masa wanka, sai ta yi da gaske. To irin wannan ne za ka ce ya je ya nema wa kansa abinci da sutura, bayan Allah ya ce a kula da yara har sai sun balaga?
Ina mamakin iyaye mata da suke barin mazaje su cutar da ‘ya’yansu da sunan addini, wannan kuskure ne. Domin juya hankalin irin wadannan yara ko matasa yana da sauki, don ba su san komai ba sai bara,  don yawanci ma ba karatun suke yi ba. Tun da a yanzu ga makarantun haddar Alkur’ani nan a ko’ina a kowace jiha ko karamar hukuma ko gari.
Abin ban haushi shine wadansu za ka ji suna bara suna cewa a taimake su za su sayi takalmi, wadansu ba lafiya, sauro na cizo, abin da ban takaici. Yakamata gwamnati ta lura da irin wadannan don samar da tsarin da za a hana bara irin wanda ake fita da yara kanana ba manya ba. Allah Ya umurci a yi wa yara tarbiya da koya masu sana’a, idan ya shekara sha biyar ya balaga ya yi wayau ka yi masa auren farko. Amma ka sake shi yana dan karami, wa ka sakar wa wannan tarbiya din? Don Allah iyaye su daina haka, don kar yara su zama ‘yan ta’adda.
Aminiya: Me za ka ce game da ‘yan Najeriya da sauran na duniya ‘ya’yan masu hali da suke zuwa Syriya da Afghanistan don shiga ISIS da kuma masu shiga Boko Haram a nan gida Najeriya?
Liman Sa’idu: Kowa zai iya yin aikin Allah na kwarai a garinsu. Koyarwa jihadi ne, yin kira ga mutane da su aikata alheri jihadi ne. Kuma ana yin Jihadi ta hanyar yin magana mai kyau a rediyo ko a jarida, ba sai an je an zare takobi ko bindiga ba.
Irin wadannan idan sun je sun ga wani abu da ba a yinsa a nan kasar suka koyo sai su dauko su zo da shi, wanda kuma zai kawo rudani matuka da yake kaiwa ga zubar da jinin bayin Allah. Ya dace matasa su nemi ilmin abu kafin su aikata shi. Su kuma ‘yan ISIS da Boko haram bai kamata suna karbar baki a cikinsu ba. Wadansu kuma suna rabewa ne da haka suna aiki barna da yin fashi da makami, kamar yadda yake faruwa.
Aminiya: Wane ne malamin kwarai?
Liman Sa’idu: Malamin sunna mai cewa Allah Ya ce, Annabi ya ce, ba tare da kage ba. Kamar yadda ya faru a kasar Faransa inda aka hana musulmi sanya hijabi ko nikabi, sai Sheikh Yusuful kardawi ya ce idan musulmi sun bar karatu saboda hijabi ko nikafi, za su cutu, sai ya ce kowace yarinya ta sanya hijabinta idan ta je kofar makaranta ta cire hijabin, idan an tashi ta fito kofar makaranta ta sanya hijabinta.
Bayan wani lokaci sai Sheikh Yusuful kardawi ya ziyarci shugaban kasar Faransa, don sun yi karatu tare, ya ce kada a bata zamantakewa tsakanin musulmi da kirista, ya ce ba za a yi zanga-zanga ba. Wannan ai shi ma jihadi ne cikin ruwan sanyi.
Aminiya: Mene ne dalilin da ya sanya wadansu malaman ba su da aikin yi ko kasuwanci?
Liman Sa’idu: Malami ya zauna babu sana’a mummunan abu ne. Malami tsakanin masu kudi da mukami zai iya fadin son rai, don yana gudun dan abin da yake samu kar ya daina zuwa, don yana da iyali. Wannan bai kamata ba mutum ya zama kamar kaska yana shan jinin mutane. Annabi Dawud yana aikin hannu. Sauran Annabawa akwai manomi da makeri. Ya kamata Malami ya zamo yana koyarwa ana biyansa, sannan ya hada da wadansu ababe na halal don ya tsira da mutuncinsa.
Aminiya: Mene ne bambancin Malami da boka, ganin yadda mata su ke kanbama su?
Liman Sa’idu: Mutanenmu idan suna samun abu a wurin boka sai su kira shi Malam. Amma Malam daban Boka kuma daban, amma akwai malam-boka, wanda ya iya karatu da rubutu amma yana bokanci. Amma kuma shi boka bai san dama da hagunsa ba, don duk wanda ya ce ya san gaibu makaryaci ne. Shi Boka mutumin banza ne. Idan ba a fada shi ba zai samu abincin da zai ci ba. Zai ce wani ne sanadin da kasa kaza, yana kawar da mutum daga Allah, ya hada shi fada da mutane, wannan ba mutumin kirki ba ne. Amma shi Malam yana cewa a bi Allah a zauna lafiya, kuma idan an samu sabani yana yin sulhu.
Aminiya: Wane kira za ka yi ga mata kan rage zafin kishi, har wadansu na cewa gara mazansu su yi zina da su yi musu kishiya?
Liman Sa’idu: Su ji tsoron Allah. Duk wanda yake son ya gama lafiya to ya bar abin da Allah ya ce a bari. Addini ya yarda a yi mata biyu ko uku ko kuma hudu. Mata su yi hakuri a zauna lafiya. Ya kamata ki zauna da kishiya don kowa da alherin da yake da shi. Ba a san wanda zai fara mutuwa ba tsakanin mata da miji, balla ki ce kashi daya bisa takwas na gado shi ne abin da yake damunki. Idan akwai matsala ki gaya wa magabata a yi wa miji nasiha. Kuskure ne mace ta ce da a yi mata kishiya gara majinta ya fita ya yi zina, ko da mata goma ne.
Aminiya: Wane kira za ka yi, don a yanzu mutane ba su san makwabtansu ba?
Liman Sa’idu: Makwabci babban mutum ne. Annabi ya ce ko tafiya ka yi ka raba wa makwabta tsaraba. Kada a cuci makwabci, kuma idan ya cuce ka ka yi hakuri. Ya ce imanin mutum ba ya cika idan mutum ya kwana da koshi amma makwabcinsa ya kwana da yunwa. Wadansu sai su shekara ba su san makwabcinsu ba. Mai cutar da makwabci bai da imani. Akwai makwabci a gida ko a hanya, da dai sauransu.