Abin Da Ke Saka ‘Yan Najeriya Shakku Game Da COVID-19
‘Yan Najeriya da yawa ba su yarda akwai COVID-19 ba, ballantana su dauki matakan kare kai
Sakamakon gwajin COVID-19 samfurin Delta
Alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa a ranar 4 ga watan Agusta kadai mutane fiye da 700 aka tabbatar sun kamu da COVID-10.
Sai dai ‘yan Najeriya masu yawa ba su yarda da cewa akwai cutar ba, ballantana su dauki matakan kare kansu da sauran jama’a.