Abin da ke tilasta mu shiga yajin aiki – Dokta Barde
Shugaban kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) reshen Jami’ar Bayero, Dokta Ibrahim Barde ya ce jami’o’in kasar nan suna bukatar kulawar gwamnatin tarayya saboda mawuyacin halin da suke ciki tun lokaci mai tsawo. Dokta Barde ya bayyana haka ne a hirarsu da wakilinmu a sakatariyar kungiyar kamar haka: Aminiya: kungiyarku ta ASUU ta dade tana […]
Shugaban kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) reshen Jami’ar Bayero, Dokta Ibrahim Barde ya ce jami’o’in kasar nan suna bukatar kulawar gwamnatin tarayya saboda mawuyacin halin da suke ciki tun lokaci mai tsawo. Dokta Barde ya bayyana haka ne a hirarsu da wakilinmu a sakatariyar kungiyar kamar haka:
Aminiya: kungiyarku ta ASUU ta dade tana shiga yajin aiki tun lokaci mai tsawo, ko me ke kawo hakan?
Barde: Babu shakka wannan kungiya tamu ta dade tana shiga yajin aiki a kasar nan domin isar da sako ga gwamnatin tarayya dangane da wasu bukatu dake ci mana tuwo a kwarya. Ba ma yajin aiki kawai domin biyan bukatar kanmu illa mu ja hankalin gwamnati kan abubuwan da suka wajaba kanta musamman kan sha’anin ilimi.
Akwai dalilai masu yawa da suka sanya muke tsunduma cikin yajin aiki wadanda suka hada da bukatar ganin an himmatu wajen samar da dukkanin abubuwan da suka kamata domin bada ingantaccen ilimi kuma mai amfani a mataki na jami’oi, amma idan ka dubi yadda jami’o’in kasar nan suke zaka yarda cewa suna cikin mawuyacin hali na rashin ababen da suka kamata ace kowace jami’a tana da su a wannan kasa tamu mai dumbin arziki.
Akwai bukatar ace kowace jami’a tana da wadatattun dakunan karatu da na daukar lakcoci da ofisoshin malamai da kuma yanayi mai gamsarwa na gudanar da aiki, amma idan ka duba zaka ga cewa kowace jami’a tana fama da wadannan matsaloli inda zaka ga dalibai fiye da ka’ida suna daukar darussa a waje guda ko kuma ka ga wasu suna zaune a kasa suna karatu, ga rashin kyawun dakunan kwanan dalibai da sauran abubuwa wanda ko kadan hakan bai dace da tsarin jami’a ba.
Haka kuma ana fama da karancin malamai a dukkannin jami’o’in kasar nan, inda zaka ga malami daya yana aikin malamai uku ko fiye da hakan, amma har yau din nan ba a iya magance wannan matsala ba. Bugu da kari muna fama da matsalar rashin wadatar kayan aiki da suka kamata kowace jami’a ta kasance tana da su kamar dakunan bincike da sauran abubuwa da ake bukata na koyar da darussa.
Matsala ta gaba ita ce batun kudaden fansho na ma’aikatan jami’o’i duk da cewa kungiya ta yi wani tunani na kafa wani tsari kan fanshon ma’aikata wanda idan an fara aiki da wannan tsari ko shakka babu za a magance matsalar fansho da sauran hakkokin ma’aikata amma har yanzu ba a bada izinin fara aiki da wannan tsari ba wanda kungiyar ASUU ta bullo da shi duk da cewa an cika dukkanin sharuddan da suka wajaba.
Bugu da kari ma’aikatan jami’o’in kasar nan sun dade suna fama da matsalar rashin tsayawa kan cikakken albashi, inda a waau lokutan sai dai a biya wani kaso na albashin kafin daga bisani a cikata sauran, ga kuma rashin biyan sauran hakkoki na ma’aikata wanda kuma hakan yana zamowa barazana ga fannin ilimi a mataki na jami’a.
Aminiya: Amma mun ga ana yin gine-gine a cikin jami’o’i da kyautata yanayin su, ta ya ya aka sami kudaden gudanar da wadannan ayyuka kenan?.
Barde: Wadannan gine-gine ana yin su ne da wasu kudade da gwamnatin tarayya ta bayar a baya a 2013 domin kara samar da gine-gine cikin jami’oi wadda su ne kake gani a kowace jami’a, amma tun daga wannan lokaci ba a sake baiwa jami’o’i wadannan kudade ba, wanda da an ci gaba da bayar da su da ina tabbatar maka da cewa kowace jami’a zata magance matsalar gine-gine da samar da sauran abubuwan da suka kamata ace ana da su a mataki na jami’o’i.
Sannan muna da matsala ta rashin shigar da batun ma’aikatan da suka bar aiki a mataki na farfesa kamar yadda ake yi a sauran bangarori da kuma makamantan wadannan matsaloli wadanda lokaci ba zai bari a fayyace su duka ba, don haka muke shiga yajin aiki a lokuta daban-daban tun dadewa.
Aminiya: Ko kuna samun wasu nasarori na cikar wasu alkawura idan kun yi yajin aikin?
Barde: To, ka san yadda lamarin yake, amma rashin cika alkawura daga gwamnati yasa muke shiga yajin aiki domin tunatar da ita cewa akwai bukatu da suka kamata a duba, kuma a aiwatar domin tabbatar da cewa karatu yana tafiya bisa nasara da inganci, amma ba ma shiga yajin aiki kawai domin biyan bukatun kanmu, illa dai mu ga an samu canji a jami’o’in kasar nan ta yadda ilimi zai bunkasa ta kowane fanni.
Aminiya: Ko akwai wasu abubuwa da idan aka aiwatar za su rage matsalolin dake damun jami’o’in da ma fannin ilimi baki daya?
Barde: Babu shakka idan aka baiwa ilimi kashi 25 cikin 100 na kasafin kudin kowace shekara za a gyara duk wata matsala dake dabaibaye cigaban ilimi a Najeriya. Idan an yi hakan ina da kyakyawan zato cewa ilimi zai bunkasa kuma kasa zata ci gaba ta kowace fuska kuma wannan kalubale ne ga mahukunta da dukkan masu ruwa da tsaki a fannin ilimin. Ina fata kuma za a dubi wadannan manufofi namu da idon rahama domin burin mu a hadu a gyara sabanin yadda ake fassara abin.