Abin da limaman jihohin Arewa 19 suka tattauna a Abuja
Yayin taron, sun tattauna kan samar da maslaha ga al’ummar kasa.
Limamai daga Jihohin Arewacin Najeriya 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja a karshen mako sun gudanar da wani taron karawa juna sani a Abuja.
A yayin taron, sun tattauna kan yadda za a ci gaba da samar da maslaha ga al’umma kan zamantakewar kasa, kamar yadda Aminiya ta jiyo.
- Saukin yin kasuwanci: Yadda Gombe ta yi zarra tsakanin jihohin Najeriya
- UAE ta dage haramcin shiga kasarta ga ’yan Najeriya
Taron, wanda kwamitin limamai na Abuja ya shirya kan cikarsa shekara 17 da kafuwa, ya gayyato limaman ne daga kungiyoyin Musulunci daban-daban daga jihohin yankin, har da limaman rundunonin tsaro.
Da yake bude taron, shugaban kwamitin limaman Abuja kuma babban limamin masallacin Juma’ah na Wuse a Abuja, Sheikh Tajuddin Bello, ya hori limaman da su zama abin misali ta hanyar kasancewa masu hakuri da sadaukarwa da yin adalci a tsakanin al’ummar da suke jagoranta.
Shi kuwa Babban limamin masallacin Alfurqan da ke Kano, Dokta Bashir Aliyu Umar wanda ya jagoranci taron, ya yaba wa kwamitin sannan ya bukaci sauran limaman jihohin 19 da su dauki darasi daga wajen kwamitin.
Wani malami daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ahmad Bello Dogarawa wanda shi ma ya gabatar da lakca a taron ya yi dogon bayani a kan ka’idojin limanci, inda ya hori limamai da su guji amfani da mumbari wajen kawo rarrabuwar kai ko yin tumasanci.
Sannan ya bukaci gwamnatoci da su rika tuntubar limaman idan za su yi wani abu ga jama’a, kasancewarsu mafi kusanci da al’ummar.
Ministan Sadarwa da Kasuwancin Intanet, Dokta Isa Ali Pantami da Babban Daraktan Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC), Kolo Mele Kyari na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron, inda suka taya kwamitin murna kan nasarorin da ya samu.
Shugabannin malaman Izala da na Dariku, sun aika da wakilansu wajen taron wanda za a kammala a ranar Lahadi.