Abin da magoya bayan United ke cewa bayan lallasa Arsenal

Ai daman ruwa ba ya manta hanyarsa.

Abin da magoya bayan United ke cewa bayan lallasa Arsenal

Santos Antony bayan ya ci wa United kwallon farko

Manchester United ta doke Arsenal 3-1 a wasan mako na shida na gasar Firimiyar Ingila da suka buga ranar Lahadi a Old Trafford.

United ta fara cin kwallo a minti 35 ta hannun Santos Antony, sabon dan wasan da ta dauka a bana daga Ajax.

Tun a minti na 12 da fara tamaula Gabriel Martinelli ya ci Manchester United kwallo, amma aka soke ta cewar an yi wa Eriksen keta tun farko.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Bukayo Saka ya farke kwallon da aka ci Gunners.

Sai dai kuma minti shida tsakani Marcus Rashford ya kara na biyu sannan ya ci na uku da ya sa United ta hada maki ukun da take bukata.

United ta ci wasa hudu a jere kenan, bayan da aka doke ta karawa biyu tun farko – sun zama na uku da suka yi wannan bajintar bayan Tottenham a 2011/12 da kuma Arsenal a 2018/19.

Arsenal ta yi rashin nasara a wasan Firimiyar Ingila da yawa a Old Traford fiye da sauran kungiyoyi har sau 17 aka zura mata kwallaye 49 – a filin Anfield ne aka zura mata masu yawa 69.

Arsenal ta kasa yin nasara a wasa bakwai baya, idan ta fuskanci Manchester United tana ta daya a kan teburi, ta yi rashin nasara biyar da canjaras biyu.

Me magoya baya ke cewa?

Wasu daga cikin magoya bayan kwallon kafa da suka tattauna da Aminiya musamman magoya baya na United sun tofa albarkacin bakinsu bayan taka wa Arsenal burki da United ta yi.

Wani mai suna Yarima daga Jihar Yobe dariya ya soma yi da cewa, “wato da sun dauka babu kungiyar da za ta ci su a kakar wasanni bana duba da yadda suka jera wasanni biyar na farko kowanne suna yin nasara?

“Ai ruwa ba ya manta hanyarsa domin kuwa tarihi ya nuna cewa duk rashin katabus da United take yi, in dai wasa ya hada mu da Arsenal wasalin ci sai ya tabbata a kansu.”

Shi kuma wani Mahmud Sanusi daga Kano cewa ya yi “a gaskiya ’yan wasan United sun buga kwallo da zuciya wanda a dalilin haka ya sa muka yi nasara a wasan.

“Akwai kuma tarihi da muke da shi a kansu wanda wannan ma ya taka rawar gani kuma hakan ya sa Arsenal din ta kasa tankwara mu duk da cewa sun fi mu rike kwallo.

“Sannan kuma ’yan wasan bayan United din sun yi kokari domin kuwa sun bayar da gudunmuwa doriya a kan wacca ’yan wasan tsakiya suka bayar musamman bajintar da Eriksen ya nuna a wasan.

“Kuma idan ka duba ko a wasan makon da ya gabata da United ta lallasa Liverpool 2-1, ba wai tsagwaran bajintar murza leda ce ta sa muka yi nasara ba, amma kishin da muka nuna da kuma kwallo da zuciya da ’yan wasan suka buga ce ta ba mu nasara wasan.

“Bugu da kari, sabon dan wasanmu Santos Antony wanda ya ci mana kwallon farko ya kara wa ’yan wasanmu karsashi.”

Idris Abdulaziz, wani mai goyan bayan Manchester City mazaunin Abuja cewa ya yi, “a nawa ganin Arsenal sun fi kokari a wasan, sai dai kuma daman irin haka ce ta saba faruwa a duk lokacin da suka hadu da United.

“Kwallon da Arsenal ta farke ta kara musu karfin gwiwa, lamarin da ya sa United ta kasa gane kanta domin kuwa ta inda Arsenal din take shiga ba ta nan take fita ba.

“Sai dai kuma tabbas kwallo ta biyu da United din ta kara ta zo ne a ba zata, domin kuwa sai da Arsenal din ta gama lugwigwita United ta yadda an kai kadamin da ba mu yi tsammanin za a karkare wasan da wannan sakamako ba.”

Wani mai suna Waspapping a shafin Twitter ya ce, “Kocin United Ten Haag ya soma assasa wani tubali na musamman wajen farfado da kungiyar.

“A bayyane take cewa Arsenal sun fi United kokari a wasan duk da cewa sakamakon bai nuna haka ba, amma idan aka samu isasshen lokaci, babu shakka Ten Haag zai dawo da United kan ganiyarta.”

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50