Abin da malamai suka tattauna da Babban Hafsan Tsaro kan Harin Kaduna

Dokta Bashir Aliyu ya bayyana abin da suka tattauna da Babban Hafsan Sojin Najeriya kan harin Mauludin Kaduna

Abin da malamai suka tattauna da Babban Hafsan Tsaro kan Harin Kaduna

Malaman Musulunci daga Arewacin Nejeria sun yi ganawar sirri da Babban Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, kan harin da jirgin soja ya kai wa masu taron Mauludi a Jihar Kaduna bisa kuskure.

A yayin ganawar sirrin, Janar Christopher Musa ya shaida wa malaman cewa tuni hukumar soji ta fara bincike a kan lamarin, kuma ya yi musu alkawarin daukar matakin da ya kamata.

Akalla mutum 100 ne suka rasu a sakamakon bom da jirgi mara matuki na Rundunar Sojin Najeria ya jefa musu bisa kuskure a lokacin da suke taron Mauludin a kauyen Tudun Biri,  Karamar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna a ranar Lahadi, 3 ga Disamba, 2023.

Fitaccen malami daga Jihar Kano, Dokta Bashir Aliyu ne ya jagoranci malaman zuwa ganawar da Babban Hafsan Sojin.

Babban hafsan tsaorn ya bayyana takaicinsa kan abin da ya faru, sannan ya ba wa malaman tabbacin shirin rundunar na “tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kassa”.

“Za mu yi duk mai yiwuwa na ganin hakan bai sake faruwa ba,” duk kuwa da matsalolin tsaro da ke addabar kasar, in ji kakakin rundunar tsaron Najeria, Birgediya Tukur Gusau, bayan ganawar sirrin.

A jawabinsa, Dokta Bashir ya yaba wa babban hafsan tsaron kan irin jagorancin da ya nuna, musamman tausayin da ya nuna kan harin.

Dokta Bashir Aliyu ya yi kira ga shugabanci da su guji yin rauwar bushasha alhali talakawa na cikin halin kaka-ni-ka-yi.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe