Abin da muka tattauna a taron hadin kan Musulmi na duniya —Sheikh Yahaya Jingir

Manzon Allah (SAW) ya ce idan Musulmi suka yi a rangama da yaki da juna, kada wani ya ce zai sha.

Abin da muka tattauna a taron hadin kan Musulmi na duniya —Sheikh Yahaya Jingir

A watan Azumin Ramadan da ya gabata ne aka gudanar da taron hadin kan Musulmin duniya, wanda Kungiyar Hadin kan Musulmi ta Duniya (RABIDA) ta shirya a Birnin Makkah, karkashin jagorancin Sarkin Salman Bin Abdul’aziz na Saudiyya.

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammed Sani Yahya Jingir, yana daya daga cikin wadanda suka halarci wajen wannan taro. Aminiya ta tattauna da shi a kan manufar taron da abin da suka tattauna:

Mece ce manufar taron da RABIDA ta kira ku?

Wannan taro na Musulunci ne na duniya da aka yi, wanda Sarkin Saudiyya, Salmanu Bin Abdul’aziz ya kira, ta hanyar Na’ibansa na farko kuma Firayi Ministan Kasar, Muhammad Bin Salman.

Manufar shirya taron shi ne, a karfafa zumunci da alaka mai karfi a tsakanin al’ummar Musulmin duniya.

A mayar da hankali, kan tsantsar addinin Musulunci. Kuma wannan taro, dama tsari ne na addinin Musulunci.

Domin Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) ya ce al’amarin Musulmi, shawara ce a tsakaninsu da juna.

Wannan shi ne jigon taron, kuma malaman addinin Musulunci, daga kowane bangare na duniya, sun halarta.

Mu a nan Nijeriya, a lokacin da muka fara zuwa wannan taro, shi ne lokacin marigayi, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Ni kuma a bana, ba zato ba tsammani suka aiko mani da takardar gayyata, a watan Azumin Ramadan da ya gabata.

Kuma abubuwan da muka tattauna a wajen taron, su ne Musulmi mu tsaya mu yi gaskiya, mu hada kai a tsakaninmu, domin duk Musulmi dan uwan Musulmi ne.

A ganinka taron ya shafi siyasar al’ummar Musulmi ne kadai ko ya shafi siyasar duniya ce gaba daya?

Taron yana da alaka ne da siyasar duniya baki daya. Domin idan ka duba yawan al’ummar Musulmi a duniya da karfin tattalin arzikinsu, na albarkatun kasa da dabbobi da yawan al’umma, za ka san cewa Musulmi na da tasiri ga ci gaban wannan duniya.

Da yawa a wasu kasashen sai ka tarar da gida guda ya susuce ta hanyar auren jinsi, wanda a Musulunci haramun ne.

Sai ka ga gidan iyali duk sun kare, saura mutum daya ko biyu. Mu kuma Musulmi ga shi muna ta haihuwa, kuma muna da koshin lafiya, ba giya ba taba. Ka ga wannan taro ya shafi duniya gaba daya.

Domin ko hakar ma’adanai ne za a yi, to ba kasashen Musulmi ne kawai za su amfana ba.

Ita duniya kamar jiki daya ne da Musulmi da wanda ba Musulmi ba. Zaman lafiya ya shafi kasashen Musulmi da wadanda ba na Musulmi ba.

Don haka, wannan taro ya shafi kasashen Musulmi da wadanda ba Musulmi ba. Kuma ya kunshi zaman lafiya da bunkasa ilimi da tattalin arziki da siyasa.

Wane alfanu ne wannan taro ke da shi ga Musulmin duniya?

Alfanun da wannan taro yake da shi ga Musulmin duniya shi ne mun hadu mun ga junanmu. An zo an yi karatun Alkur’ani da hadisai a wajen.

Hankalin kowa ya kwanta, an kuma kyautata dangantaka, mai karfi. Na biyu muna jin zafin a bar wani abokin gaba, ya zo ya yi ta kashe Musulmi, sauran Musulmi suna kallo.

Dole ne Musulmi su tashi su tsawatar ga duk wani mai gaba da Musulunci, kada ya gan mu a rarrabe.

Ka ga a nan za mu ce wannan taro ya kawo alfanun nuna damuwa da damuwar juna. Ta yadda wadanda ba Musulmi ba, za su yi ta musulunta.

Domin za su ga zaman da ba na Musulunci ba, baragada ce da zalunci da cuta.

Wane sako ne kake da shi zuwa ga al’ummar Musulmi?

Sakona ga al’ummar Musulmi shi ne mu ci gaba da neman ilimi tare da aiki da shi, Mu kiyayi shirka da zalunci da karya. Mu rike gaskiya mu so junanmu mu inganta tarbiyyar ’ya’yanmu.

Kuma dole Musulmi a yi hakuri da juna. Idan an yi hakurin nan kada ya zama a fatar baki.

Wauta ce a ce ga kasa ta Musulmi da kasa ta Musulmi, rashin hakuri ya kai ga a dauki makamai, ana yakar juna.

Manzon Allah (SAW) ya ce idan Musulmi suka yi a rangama da yaki da juna, kada wani ya ce zai sha.

Kada mu biye wa abokan gaba, su yi ta hada mu muna fada da juna. Mu hada kai mu gina ilimi da tattalin arziki da zaman lafiya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos