Abin da muke bukata wajen Shugaba Buhari – Dokta Shamsudden

Aminiya ta zanta da Dokta Shamsuddeen Aliyu Maiyasin, dan gwagwarmayar kwato wa matasa ’yanci, kuma shi ne Shugaban Kungiyar National Youth Empowerment Initiatibe, ya bayyana abin da suke bukata daga Shugaba Buhari a kungiyance:   Mene ne ayyukan wannan kungiyar taku? Ayyukan kungiyar su ne taimakon matasa da samar masu da ayyukan yi da wayar […]

Abin da muke bukata wajen Shugaba Buhari – Dokta Shamsudden

Dokta Shamsuddeen A. Maiyasin

Aminiya ta zanta da Dokta Shamsuddeen Aliyu Maiyasin, dan gwagwarmayar kwato wa matasa ’yanci, kuma shi ne Shugaban Kungiyar National Youth Empowerment Initiatibe, ya bayyana abin da suke bukata daga Shugaba Buhari a kungiyance:

 

Mene ne ayyukan wannan kungiyar taku?

Ayyukan kungiyar su ne taimakon matasa da samar masu da ayyukan yi da wayar da su a kan ababen da suka shige musu duhu tare da fafutikar nemo musu hakkinsu da  sasanta rikicin addini ko kabilanci da kuma koyar da matasa sana’o’i domin dogaro da kai, da daukar nauyin karatunsu har zuwa jami’a, da kuma wayar musu da kai su guji shan miyagun kwayoyi da kokarin tsaya musu a kan yin aure domin rage zinace-zinace da wayar da kansu kan su guji bangar siyasa da sauransu.

Yaushe kuka kafa wannan kungiya?

Wannan kungiya an kafa ta tun zamanin mulkin Murtala Muhammed, kuma ni ne shugaba na 27. Kuma duk abubuwan da na lissafa maka su ne ayyukan kungiyar kuma suna cikin dalilan kafa kungiyar, wanda daga kafa kungiyar zuwa yanzu mun yi mambobi na da na yanzu da suka kai miliyoyi. Kuma mun kafa makarantu tun daga firamare da sakandare da na koyon addini da dama a fadin kasar nan. Mun yi daruruwan asibitoci, da wuraren koyon sana’o’i. Kuma mun biya wa dubban matasa sadaki da wurin zama kafin su mallaki nasu, kuma mun dauki nauyin karatun matasa akalla 3,000 masu karatu a jami’a. Sannan mun koya wa matasa sana’o’in hannu tare da jari sannan su ma suka koyar da wadansu ba adadi. Sannan mun dauki nauyin asibiti na marasa galihu da dama, kuma mun yi sulhu a tsakanin kabilu akalla sau 135. Mun fanshi fursunoni da dama, idan kuma bashi ake bin su mu biya musu. Sannan mun kai dalibai su yi karatu a kasashen waje irin su Sudan da Kamaru da Ghana da Nijar da Uganda da  Ingila da sauransu. Amma mukan nemi gurbin karatu ne a jami’o’in kasashen waje ta tallafin scholarship, sai kuma mu san yadda za mu turo daliban. Duk wannan kokarin da muke yi a kungiyance da wanda nake yi, suna cikin abin da ya sa Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris ya nada ni Garkuwan Makarantar Zazzau. Kuma wannan kadan ne daga cikin ayyukan da kungiyar ke yi.

Za ka iya cewa kun samu nasara a kungiyar?

Kwarai kuwa. Nasarorin da muka samu sun hada da rage zaman banza da rage yawan shaye-shaye da taimakawa wajen rage ta’addanci. Mun hada aure da yawa, kuma mun taimaka wurin zaman aure ta hanyar ba matan aure jari. Kuma babban nasarar ita ce yawancin ayyukanmu muke hada kudi mu yi. Muna tara kudin da ya kai Naira miliyan 5 lokaci bayan lokaci. Sannan kungiyar ta samu kudi sai ta juya kudin ya rika kawo riba. A zamanin Janar Babangida kungiyar ta fara sayen motocin haya, kuma ta fara noma. A zamanin Abacha kuma ta fara kafa makarantu masu zaman kansu wanda zuwa yanzu ko makarantun gaba da sakandare muna da akalla 400. Daga bisani muka fara kafa asibitoci da gidajen mai da sauransu.

Ka ce kun taimaka wa kamfe din Buhari, ta yaya?

Mun taimaki Buhari ta hanyar tura masa kati lokacin kamfen domin mambobinmu kusan kashi 80 cikin 100 sun tura masa a matsayinsu. Kuma ni kaina na tura da yawa, sannan duk inda zai je kamfe, mukan sa shugaba na wannan jiha da Buhari za shi ya jagoranci matasa, kuma su kara taimakon tsaron wurin, sannan masu nisa kungiya kan biya musu alawus na tafiya. Mun yi masa kalanda, mun sa an yi masa wakoki, mun tara masa matasa. Kai wani abin ma idan na tuna, raina kan baci inji kamar zan yi kuka domin wallahi, mun dauki nauyin zuwan wadansu Saudiyya wadansu Jerusalem don su yi masa addu’a, mun raba motocin shinkafa da taliya saboda kaunarsa. Kai mun hana kanmu sukuni muna addu’a domin ya samu nasara.

Yanzu me ya sa kuke neman ganawa da shi?

Dalilin da ya sa muke neman mu gana da shi shi ne yadda yake mulkin kamar ba shi ne Shugaban Kasar ba, kawai wadansu ne ke sarrafa kasar. Domin ya fada mana sau daya zai yi mulki. Muna so mu yi masa tuni, muna so mu shaida masa ya ce da matasa za a yi mulki, amma Ministan Matasa ma tsoho aka ba, kuma an mayar da matasa baya. Muna so mu yi masa magana a kan kashe matasa da aka yi a rikicin Shi’a na Zariya. Muna so mu yi magana da shi a kan Zamfara domin barayi na kashe mana matasa, muna so mu yi masa tuni a kan ana korar matasa a aiki da yawa kuma rashin aikin yi na sa mutane zama ’yan ta’adda, muna kuma so mu yi magana da shi domin mu ja hankalinsa ya rika girmama doka. Da kuma wasu korafe-korafe da ba zan iya fada a jarida ba yanzu.

Ke nan domin bukatar kungiyarku da kanku kuke neman ganinsa ba na mutane ba?

Bukatar al’umma ce. A nan ka ji wani abu da zai taimaki Shamsudeen ko iyalansa? Da yawan mambobinmu fa suna da abin yi kuma masu ilimi ne kuma har da manyan sarakuna da hakimai a cikinmu. Mu dai lafiya da gamawa lafiya muke so. Don haka don bukatar al’umma muke son ganinsa domin babbar kungiya irin wannan mai dimbin ci gaba da dimbin tarihi. Kuma ta matasa, kuma matasan nan kuwa muke da kashi 68 cikin100  na mutanen kasa, to muna ganin idan ba ma tare da shi, to ban ga yadda za a yi  ya ci zabe ba. Shi ya sa ba mu so mu yi wannan maganar da ’yan jarida.

Wane kira kake da shi ga Shugaba Buhari?

Kiranmu ga Buhari shi ne ya ji tsoron Allah domin mulki na da karshe. Su kuma wadanda ke nuna masa matasa ba su da wani amfani wallahi ba masoyansa ba ne, kuma suna yaudararsa da kawo wasu kananun kungiyoyin matasa cewa wai suna goyon bayansa, har ma suna saya masa fom din takara. Sannan ya kamata ya gyara yadda yake gudanar da mulki. Idan abubuwa suka gyaru, za mu yi kuri’a a kungiyance mu gani. Idan wadanda suke son Buhari suka fi yawa, ya zama dole mu hadu mu goya masa baya. Amma gaskiya sai mun ga alamar gyara.