Abin da mutanen Taraba suke fata daga gwamnatin Buhari – Shugaban APC
Alhaji Hassan Ardo shi ne Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Taraba a hirarsu da wakilinmu a Jalingo ya zargi gwamnatin PDP a jihar da kuma ta tarayya kan kasa samar da ababen more rayuwa ga jama’ar jihar a shekara 16 na mulkin dimokuradiyya: Aminiya: Al’ummar Taraba suna korafin cewa Gwamnatin PDP ba ta gudanar da […]
Alhaji Hassan Ardo shi ne Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Taraba a hirarsu da wakilinmu a Jalingo ya zargi gwamnatin PDP a jihar da kuma ta tarayya kan kasa samar da ababen more rayuwa ga jama’ar jihar a shekara 16 na mulkin dimokuradiyya:
Aminiya: Al’ummar Taraba suna korafin cewa Gwamnatin PDP ba ta gudanar da ayyukan raya kasa a jihar ba, yanzu an samu canjin gwamnati ta Jam’iyyar APC da Muhammadu Buhari zai shugabata, me kake gani al’ummar jihar za su samu daga gwamnati mai zuwa?
Hassan Ardo: Kowa ya san Muhammadu Buhari mutum ne mai fada da cikawa, kuma ya kamata jama’a su tuna Buhari ya rike Gwamnan soja na tsohuwar Jihar Arewa maso Gabas da ta hada da jihohin Borno da Bauchi da Yobe da Adamawa da nan Taraba saboda haka ya san wannan jiha da bukatunta da dimbin matsalolinta. Shugaban kasa mai jiran gado ya san albarkatun da ke wannan jiha da masana’antun da suka dace da wannan jiha. Kasancewata shugaban Jam’iyyar APC mun san irin bukatun jama’a da abubuwan da ake bukata a yi don bunkasa jihar nan. Kuma a lokacin da Buhari ya zo nan jihar yakin zabe, ya fadi cewa aikin gina madatsar ruwa ta Mambila don samar da wutar lantarki na daya daga cikn muhimman ayyukan da gwamnatinsa za ta ba muhimmanci don bunkasa masana’antu. Abin da muke sa ran gani shi ne da yardar Allah in Muhammadu Buhari ya karbi mulki zai aiwatar da wannan aiki na gina madatsa ta Mambila domin kowa ya san Buhari mutum ne mai cika alkawari. Kuma in an gina wannan madatsar ruwa za a samu ingantatciyar wutar lantarki da za ta bunkasa ayyukan masana’antu. Kuma muna da tabbacin cewa Gwamnatin Tarrayya a karkashin Buhari za ta gudanar da wannan aiki mai muhimmanci ba wai ga Jihar Taraba ko yankin Arewa maso Gabas ba, har ma ga kasa baki daya. Ina yi wa jama’ar jihar nan albishir cewa za su san yanzu akwai Gwamnatin Tarayya wadda za ta kawo ayyuka raya kasa ba irin ta PDP ba.
Aminiya: Akwai maganar yanayi mai kyau da Allah Ya ba yankin Mambila kuma in aka lura za a ga yankin Obudu da ke Jihar Kuros Riba yanayi daya ke da shi da na Mambila, ga shi an gyara Obudu ana zuwa yawon shakatawa ana samun kuzin shiga an yi watsi da Mambila, me gwamnati za ta yin don bukasa wannan yanki?
Hassan Ardo: In ka lura a kullum ba ni da ra’ayi gwamnatin PDP a jiha da kuma ta tarrayya, saboda rashin bayar da muhimmanci ga ayyukan da za su kawo ci gaban kasa. Sai cin hanci da rashawa, In ka lura da kyau za ka fahimci cewa yankin Mambila shi ne yankin da ya fi cancanta a bunkasa don samar da wurin yawon shakatawa amma gwamnatin Jihar Taraba a karkashin PDP ba ta maida hankali wajen bunkasa albarkatun wannan jiha ba, illa kawai almundahana da nuna bambanci a tsakanin jama’ar jihar wanda hakan ya haifar da koma baya ga jihar.
Yankin Mambila yanki ne da Allah Ya ba ni’ima mai yawa ga sanyi kwatankwacin na kasashen Turai ga koguna da ruwa ke gudu a kowane lokaci a cikinsu. Da an bunkasa wannan wuri al’umar kasar nan ba za su yi burin zuwa kasashen Turai don yawon shakatawa ba. Kuma in aka bukasa wannan yanki ta fuskar yawon shakatawa, Jihar Taraba za ta samu kudaden shiga masu yawa da ba sai mun dogara ga Gwamnatin Tarraya ba. In dai jihohi kamar Legas da Kano da Kuros Riba da sauransu za su rika samun kudin shiga mai yawa ba tare da dogaro kacokan kan kason tarayya ba, mafita ita ce dole ne a bunkasa albarkatun wannan jiha. Jihar Taraba za ta iya dogaro da kanta domin masu hannu da shuni za su kawo jari su kafa masan’antu da za su samar da ayyukan yi da za su samar wa jihar hanyoyin samun kudi ta fuskar haraji. Bai kamata a ce Taraba ce koma baya ta fuskar samun kudin shiga a kasar nan ba, duk tana da albarkatun kasa masu yawa. Yanzu jihar da Gwamnatin tarrayya ta dogara wajen samun kudin shiga muddin Gwamnatin Tarrayya ba ta raba kudi ba, to, ko albashi ba za a iya biya ba.
To, gwamnatin Buhari tana da shirin da zai bunkasa kudin shiga na jihohi ba tare da sai sun dogara ga kudin da ake samu daga man fetur ba, wannan shiri zai bunkasa hako albarkatun kasa a kowace jiha, kuma da yardar Allah za a samu nasara kuma al’ummar kasa za su ga alfanun shirin musamman jihohin da ba su da mai fetur. Ka duba saboda sakaci da rashin adalci irin na gwamnatin PDP kungiyar Tarayyar Turai ta zuba jari na miliyoyin Dalar Amurka don bunkasa kamfanin ganyen shayi na “Mambila High Tea Company,” bayan haka kaddarorin kamfanin an kiyasta a kan sama da Naira biliyan shida sai ga shi an sayar da kamfanin a kan Naira miliyan 500 biyar kacal. Kuma abin ban haushi shi ne an sayar da kamfanin ne a kan bashi. Ganyen shayin da ake sarrafawa a kamfanin yana da farin jini a kasuwannin cikin gida da wasu kasahen waje. Mun san mugudin da aka yi wajen sayar da kamfanin za mu fadi domin a kwato wa jama’a dukiyarsu.
Aminiya: Ana ce yankin Mambila ya fi ko’ina a kasar nan yawan shanu, amma ga shi har yanzu ba wani kamfanin sarrafa naman shanu ko na madara ta ina kake ganin gwamnati ya kamata ta taimaka?
Hassan Ardo: Ka san ni Bafillace ne kuma ina kiwon shanu, a saninmu akwai shanu sama da miliyan hudu a tsaunin Mambila, domin yanki ne da ba sauro ba kudan tsando kuma akwai wurin kiwo mai fadi tare da ruwan sha na mutane da dabbobi duk tsawon shekara. Wannan ya sa kiwon dabbobi ke da sauki a wannna yanki. Ana samun kudi masu yawa ta fuskar hajarin shanu kuma ga kasuwannin shanu a duk fadin yankin Mambila, amma duk da wannan karamar Hukumar Sardauna ita ce ta fi kowace karamar hukuma koma baya a jihar nan.
Wannan bai rasa nasaba da cin hanci da rashawa, kuma abin kunya ne a ce duk da kudin da ake samu ta hanyar haraji har yanzu karamar hukumar tana fama da rashin kudi. In aka samu gwamnati mai adalci wadannan abubuwa za su kau. Yanzu saboda rashin masana’antu dole sai mun kai shanu Kudu, kamar su Enugu da Legas da Kalaba don sayarwa, wannan yana da hadari a halin da ake ciki. Da a ce akwai masana’antun sarrafa naman shanu da na Madara da an samu saukin kasuwanci tare ba matasa ayyukan yin. Sarrafa albarkatun da Allah Ya ba kowane yanki shi ne muke sa ran Gwamnatin Muhammadu Buhari za ta ba muhimmanci don bunkasa tattalin arzukin kasa da samar wa matasa ayyukan yi. Kuma matsalar tashin-tashina a tsakanin manoma da makiyaya za ta ragu in aka samu masana’antu, domin ’ya’yan manoma da na makiyaya za su samu aikin yi kuma za a samu riba kan albarkatun dabbobin. A wannan jiha muna kyautata tsammanin Gwamnatin Tarayya za ta yi duk abin da ya kamata wajen zakulo albarkatun kasa don bunkasa tattalin arzikin jihar da na kasa baki daya. A wannan jiha yanzu an daure wa wasu gindi suna aikata rashin gaskiya wasu har sayen makamai suke yi suna ba ’yan uwansu don tayar da husuma, amma an kyale su har ma manyan mukamai ake ba su. Wannan ya nuna rashin shugabanci nagari da rashin adalci da gwamnatin PDP a jihar da daurin gidin Gwamnatin Tarayya suke yi. Na tabbata Shugaba Muhammadu Buhari ba zai yarda a zalunci wani don addini ko kabilarsa ba, zai ba kowa hakkinsa yadda doka ta tanada. kasa ta zauna lafiya kowa ya yi walwala lami lafiya ba tare da tsangwama ba, kuma ta haka ne kasa za ta ci gaba, tattalin arziki ya bunkasa.