Abin da Sanusi II ya tattauna da gwamnatin sojin Nijar

Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi wa Tinubu bayanin tattaunawarsa da masu juyin mulkin Nijar gabanin taron ECOWAS kan ɗaukar matakin soji a Nijar

Abin da Sanusi II ya tattauna da gwamnatin sojin Nijar

Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya a Yammacin Afirka, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce shugaban mulkin sojin Nijar, Abdourahamane Tchiani ya ba shi muhimmin sako ga shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda ke jagorantar ƙungiyar ECOWAS.

A daren Laraba Sanusi ya kai wa Tinubu saƙon, ya kuma bayyana masa sauran abubuwan da suka tattauna da shugaban mulkin sojojin da suka kifar gwamnati a Jamhuriyar Nijar.

Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi wa Tinubu bayanin ne gabanin taron ƙungiyar ECOWAS da ke duba yiwuwar ɗaukar matakin soji a Nijar, shawarar da ta bar baya da kura.

Sanusi ya ziyarci birnin Yanayi ne bayan gwamnatin sojin Nijar ta ki yin maraba da wakilan ECOWAS da ƙasahen Turai da suka nemi zuwa domin tattaunawa da su, inda sojojin suka ce ba za su iya tabbatar da tsaron baƙin ba, saboda halin da ƙasarsu ke ciki na ƙyamar waɗancan kasashe.

Bayan dawowar Sanusi II daga Nijar ne ya ziyarci Tinubu a cikin dare inda ya yi masa bayanin tattaunawarsa da Janar Abdulrahmane Tchiani.

Ganawar Sanusi II da Tinubu ta kasance ne bayan shugaban ƙasa ya gama tattaunawa da manyan malaman Musuluncin Najeriya kan taƙaddamar ta Nijar.

Dalilin ganawar Sanusi da Tinubu

Khalifa Sanusi ya bayyana cewa ya kai ziyarar ce a matsayinsa na jagora ba wakilin gwamnati ba, domin guje wa illar da rikicin na Nijar da matakin soji da kungiyar ECOWAS ke shirin dauka a kan masu juyin mulki zai yi wa Nijar da babbar maƙwabciyarta Najeriya.

Majiyarmu ta ce duk da cewa ziyarar ta ƙashin kai ce, amma kafin tafiyar Khalifa Sanusi sai da ya sanar da Shugaba Tinubu, don haka da ya dawo ya je ya sanar da shi abin da suka tattauna.

Aminiya ta kawo rahoton ganawar jagoran gwamnatin sojin Nijar Janar Abdulrahmane Tchiani da Sarki Sanusi II, wanda ya samu rakiyar Sarkin Damagaram.

Ɗariƙar Tijjaniyya wadda Sarki Sanusi II ke jagoranta na da dimbin mabiya a Jamhuriyar Nijar.

Jajibirin taron ECOWAS

Tinubu shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS wadda ta ƙaƙaba wa gwamantin sojin Nijar takunkumin karya tattalin arziƙi.

Hakazalika Najeriya babbar maƙwabciyar Nijar ta yanke wutar da take bayarwa a matsayin wani mataki na ƙara takura wa masu juyin mulkin su sauka.

Ganawar tasu dai na zuwa ne kasa da awa 24 kafin taron shugabannin ECOWAS da Tinubu ke jagoranta, inda za su cim-ma matsaya kan sabon matakin da za su ɗauka bayan wa’adi na biyu da suka ba sojojin na Nijar su mika wa Bazoum mulki su koma barikin.

An ja layi

Sojojin da suka hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum dai sun yi watsi da barazanar ECOWAS tare da katse hulɗa da Najeriya da Togo da kuma manyan ƙasashen Amurka, Faransa da Italiya da Gwamnatin Bazoum take ɗasawa da su.

Sun kuma rufe sararin samaniyar kasar tare da barazanar yaƙar duk ƙasar da nemi yi wa ƙasarsu shisshigi a harkokinta na cikin gida.

Sun kuma nemi taimakon Rasha, babbar kishiyar Amurka da ƙasashen Turai, kuma ta amsa kira.

Haka kuma maƙwabtan Nijar da ke hannun sojoji, Mali da Burkina Faso sun yi alkawarin taimaka musu yaƙar masu neman yi musu kutse.

Tuni dai ECOWAS ta dakatar da kasashen uku, waɗanda tun kafin yanzu suka kaurace wa zaman taron kwamitin Manyan Hafsoshin Tsaron kungiyar.

Kungiyar ta kuma rufe asusun ajiyar Nijar a yayin da Amruka da Faransa da Majalisar Ɗinkin Duniya suka dakatar da tallafi da kuma ayyukan jin kai da suke gudanarwa a Nijar.