Abin da shugabannin Ibo ke nufi da batun ballewa -Sanata Abdullahi Adamu
Sanata Abdullahi Adamu ya ce rashin kaiwa ga madafun iko ne ya haddasa guna-gunin
A makon jiya ne Sanata Abdullahi Adamu ya yi doguwar tattaunawa da jaridun kamfaninmu a kan al’amura da dama da suka shafi kasa. Aminiya ta tsakuro wani bangare na tattaunawar don amfanin makarantanmu
Ka bayyana ra’ayinka kan yunkurin ballewa a sassan kasar nan, musamman a Kudu maso Gabas da sake fasalin kasa da sauransu. A ’yan kwanakin nan, gwamnonin Kudu maso Gabas sun bayyana goyon bayansu ga kasancewar Najeriya a dunkule, shin kana jin hakan zai kwantar da kurar yunkurin da kashe-kashe a waccan shiyya?
Yayin da nake maraba da wannan ci gaba, har yanzu ban gamsu da haka ba. Dole ne mu ba da lokaci mu ga abin da zai faru. Mutane ba za su zauna su ba da sanarwa kuma su yi tunanin mu amince da haka ba. Muna fata halin da Najeriya take ciki zai gushe.
Na yi imani batun rashin tsaro a Kudu Maso Gabas da furucin da shugabanninsu na siyasa suke yi, suna yi ne saboda ba su ga kofar samun mulki ba. A wani lokaci za ka yi ta mamakin abin da suke guna-guni a kai.
Idan ka dauki dukkan muhimman ofisoshin da suke kasar nan, za ka ga Ibo da Yarbawa da mutanen Kudu Maso Kudu su ne suka mamaye su. Duk wannan gutsiri-tsoma ana yi ne a kan batun shugabancin kasa.
A wurinsu, domin me wani dan Arewa zai hau kujerar Shugaban Kasa bayan Buhari?
Ba ina fadin shifcin gizo ba ne, shekaruna sun kai in san hakan. Kuma na san Najeriya sosai ta yadda zan iya sanin don me aka yi wancan furuci. Don haka ba zan gasgata su ba, sai na gani a kasa.
Yaya takwarorinka a Majalisar Dokoki ta Kasa? Ko kun zauna tare kun tattauna wannan matsala, saboda kalubale ne ga Najeriya?
Mun yi ta tattaunawa gwargwadon iyawa, shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa, sun yi bakin kokarin kauce wa zama masu karkata ga wani bangare. Sun yi kokarin tafiya tare da kowa don ba kowa hakkinsa. Sannan a wani bangare wannan batu ba wani abu ba ne da zai sa a tayar da jijiyar wuya.
Majalisar Dokoki ta Kasa dole mu ce tana kokari wajen tafiya da kowa gwargwadon iko. Amma wani lokacin akan samu wadansu da suke kawo rudani, amma duk da haka akan tattauna komai gwargwadon abin da ake iyawa.
Wani lokaci ’yan adawa suna son su kawo cikas a kan wasu muhimman batutuwa da suka jibanci ci gaban kasa. Sai dai idan hakan ta faru, mukan amsa musu da duk yadda suka shigo da lamarin. Amma gaba daya, Majalisar Dattawa ta tara ta rage nuna bangaranci zuwa mafi karanci.
Shin akwai wani kokari don kiran taro a tsakanin rukunoni?
Yin hakan sai da takatsantsan don kada a fada a cikin tarkon da wani zai dana.
Abin da suke korafi a kai shi ne dangane da nade-naden da ake yi a yanzu, ba a daukar nasu, shin ka yarda da haka?
A wurina, kowanne bangare na gwamnati yana da matukar muhimmanci. Wane ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya? Wane ne Ministan Ayyuka? Wane ne Ministan Lafiya? Wane ne MinistanWatsa Labarai? Wane ne Ministan Kudi? A tattaro duk wadannan nade-naden a sanya su a kan sikeli. ’Yan Arewa nawa ne a wurin?
Amma sun ce ’yan Arewa ne suka mamaye harkar tsaro. Me muke kira da mamaya? Tsaro harkar kwarewa ce ta lokaci, suna tafiya ne ta hanyar wannan yana gaba da wancan daki-daki; kana daukar wani mataki wajen nada mai rauni sai tsarin ya shiga matsala.
Muna son kirkiro abubuwan da za su kawo rikici ne ba tare da wani dalili ba.
Bai kamata mu rika yaudarar kanmu ba, wani yana magana a kan yana so a raba kasar nan, kuma a lokaci guda ya ce yana son ya zama Babban Hafsan Sojin Kasar nan ko Babban Hafsan Tsaro?
Shin haka ake tafiyar da gwamnati? Ba zai yiwu ba. A wannan mataki dole ne mu fada wa ’yan Najeriya gaskiya kamar yadda muka fahimta.
Lura da canjin batun, ina kake ganin Najeriya ta dosa?
Da kyau, na yi imani sosai cewa Shugaban Kasa yana yin iyakar kokarinsa.
Muna sake duba tsarin mulki a halin yanzu a Majalisar Dokoki ta Kasa, haka ne ya kamata ya faru maimakon kawo batun rarraba kasa.
Idan aka zo batun kundin tsarin mulki, akwai tsari, kuma Shugaban Kasa ya sha fadin cewa masu son a sake fasalin kasar nan, ya kamata su je Majalisar Dokoki ta Kasa su gabatar da haka.
Shin kuna canja muhimman bangarorin tsarin mulki ne?
Ba na son in yi riga-malam-masallaci, don kada wani ya ce Abdullahi Adamu ya fadi kaza a hira da gidan talabijin na Trust TV. Ina shugabantar daya daga cikin tarukan sauraron ra’ayin jama’a na shiyya.
Shin akwai wani yunƙuri daga bangarenka?
Akwai yunkuri na sauraron ’yan Najeriya, tare da duba da idon basira a kan muhimman batutuwa gwargwadon yadda muka fahimce su. Abin farin ciki, ’yan sanda sun halarci taron sauraron ra’ayin jama’a na shiyya da muka yi, don haka muna fata majalisun dokoki na jihohi, su ma za su bi sahu domin a kammala akasarin aikin, kuma a hanzarta sanya masa hannu.
Wani muhimmin abu da nake da yakinin ka magance a lokacin da kake Gwamna shi ne tafiyar da kananan hukumomi. Hatta Shugaba Buhari ya koka da yadda gwamnoni suka rusa ko suka kusan rusa wadanan hukumomin saboda suna kwace kudadensu da galibin ayyukansu. A wancan aikin gyaran kundin tsarin mulki, an yi kokarin sauya hakan, amma aka kashe batun a majalisun dokoki na jihohi, ba su tabo muhimman batutuwan da za su kawo sauye-sauye na ba da karin ’yanci ga kananan hukumomin ba. ku ’yan siyasa kuna wani yunkuri ne na rusa tsarin kananan hukumomi a Najeriya?
Zan yi tsayin daka matukar ina numfashi don in tabbatar da ganin kananan hukumomi sun ci gaba da samun ’yancin cin gashin kansu.
Ana nuna rashin adalci sosai a kan tsarin tafiyar da kananan hukumomi a kasar nan, har an kai matsayin da kamar ma babu su.
A kowane wata, akwai zama a kan kudin da ake rabawa. Kamar yadda Gwamnatin Tarayya take bayar da kaso, jihohi su samu kasonsu, haka kananan hukumomin da suke cikin Kundin Tsarin Mulki ya wajaba su samu nasu.
Dokokin ba su canja ba. Amma wani lokacin muna da girman kai.
Wani lokaci mukan ki yarda da gangan mu fada wa kanmu gaskiya.
Me ya sa gwamnatocin jihohi suke nuna wannan hali na danne kananan hukumomi?
To watakila suna da wani dalilinsu na son yin hakan, amma dai ni na san, lokacin da nake Gwamna, ban yi haka ba, ba na taba kudin kananan hukumomi, kai ko da kudin da muka samu daga Asusun Tarayya ya kare, akwai kwamitin da muka samar da ke lalubo mana hanyoyin samun kudin shiga.
Amma ba na shiga cikin asusun kananan hukumomi.