Abin da talakawa suke bukata daga sabuwar gwamnatin Buhari

A yau mun bayar da aron wannan fili ne ga dan kasuwa, dan gwagwarmaya kuma dan siyasa, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, kuma tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Harkokin Noma ta Jihar Kano (KACCIMA), Alhaji Abdulkarim Daiyabu (08023106666, 08060116666), inda ya yi sharhi tare da bai wa gwamnati mai […]

Abin da talakawa suke bukata daga sabuwar gwamnatin Buhari

A yau mun bayar da aron wannan fili ne ga dan kasuwa, dan gwagwarmaya kuma dan siyasa, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, kuma tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Harkokin Noma ta Jihar Kano (KACCIMA), Alhaji Abdulkarim Daiyabu (08023106666, 08060116666), inda ya yi sharhi tare da bai wa gwamnati mai zuwa shawarwari kamar haka:

Hakika an samu kura-kurai a zubin gwamnatin Buhari ta farko, wannan ba zai rasa nasaba da muguwar barnar da gwamnatin ta iske ba, da kuma yadda ba a tsoma wadanda suka san siyasa a cikin gwamnatin ba, sai aka ba da fiffiko ga wadanda ake ganin kwararru ne wadanda a galibi sukan kasa aiwatar da ayyukan da aka dora musu.

Ga fahimtata rashin sanya ’yan siyasa na gidi a gwamnatin ya taimaka ’yan siyasar da suka hadu wajen kafa Jam’iyyar APC suka rika zame kafar gwamnatin ta Buhari, yayin da wadanda ya nada da yake ganin nasa ne saboda rashin sanin siyasar suka daburce suka kasa fidda gwamnatin daga matsalolin da ta samu kanta a ciki.

Hakika rashin iya siyasa daga akasarin jami’an gwamnatin Shugaba Buhari ne ya sanya ta gaza cimma kudirorinta kamar yadda jama’ar kasa suka sanya rai, har ta kai a yau akwai wadanda suke fata Jam’iyyar PDP ta dawo gadon mulki, duk da muguwar barnar da ta tafka a shekara 16 na mulkinta.

Idan ba rashin iya siyasa ba, yaushe za a ce mun fara tuna PDP a Najeriya, lura da barnar da ta rika faruwa a lokacin mulkinta? Mu tuna a zamanin PDP ne aka fi kassara tattalin arzikin kasar nan da sunan tsame hannun gwamnati daga harkokin kasuwanci inda a mahaifata Jihar Kano cikin shekara hudu na farkon mulkin Cif Obasanjo aka rufe masana’antu kusan 200. Kada a yi batun masaku da kamfanonin harhada motoci da na taki da na yin takardu da gwamnatin PDP ta yi gwanjonsu a tsakanin ’ya’yanta wadanda akasarinsu sai da suka ci bashi a bankuna suka iya tsayawa takarar mukaman da suka kai su gadon mulki.

Rufewa da sayar da wadannan masana’antu ne ya fara dora kasar nan a kan turbar rashin aikin yi da kara talautar da talakawa. Kwatsam! Sai kuma gwamnatin PDP ta kwace iko da ’yancin kananan hukumomi ta mayar hannun gwamnonin jihohi saboda burin Obasanjo na tazarce wanda hakan ya dada jawo mugun talauci a yankunan karkara.

Wadannan abubuwa biyu ne ummulhaba’isin talaucin da ya kara jefa masu raunin imani da rashin tausayi suka fara aikata wasu miyagun ayyuka kamar fashi da makami da rikice-rikicen kabilanci da sace-sacen shanu da Boko Haram da satar mutane don tsafi da satar mutane ana neman kudin fansa da sauran miyagun ayyuka.

Haka gwamnatin Buhari ta gaji kasar nan matsaloli sun yi wa kasar nan daurin gwarmai, to amma wajen kafa gwamnatin Buhari aka sake samun matsala wajen dauko wadanda ba ’yan siyasa ba aka nada su a mukaman da ba su dace ba. Hatta wajen tsayar da ’yan takarar mukamai akwai mutanen da kawai sun hau bayan Buhari ne suka kai ga kujerun da suke kai ba don sun cancanta ba, wannan ya sa duk da muguwar barnar da PDP ta yi a kasar nan sai ga wadansu sun fara juyowa suna son wai ta dawo mulki!

A ganina ko hare-haren Boko Haram da kashe-kashen da muka yi fama da su a kwanakin karshe na gwamnatin PDP, sun isa mu dauki shekara da shekaru ba mu yi tunanin PDP ta dawo gadon mulkin kasar nan ba.

Don haka halin da ake ciki a kasar nan akwai bukatar gwamnatoci a matakai daban-daban su samar da wasu hanyoyi ko wata gidauniyar kula da talakawa marasa karfi domin ceto rayuwar mutanen da suke cikin tsananin bukata a daukacin kananan hukumomin kasar nan 774, musamman a wuraren da suka fi fama da annoba.

Baya ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, manyan kamfanoni da masana’antun da ke Najeriya tun daga Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) da kamfanonin sadarwa da na gine-gine gidaje da na hanyoyi da bankuna da sauran masana’antu a sanya kowanne ya rika bayar da akalla kashi biyu cikin 100 na dukiyar da ya mallaka ko kashi 5 cikin 100 na ribar da ya samu a shekara a zuba a asusun kula da marasa karfin.

Masu hakar mai da sufurinsa da daidaikun masu dukiya su kuma su rika bayar da akalla kashi daya cikin 40 na adadin abin da suka mallaka duk shekara ga wannan asusu. Idan haka ya samu sai gwamnati ta yi amfani da kudin wajen sayen kayan amfani gona da na masarufi a raba a wadace kuma kyauta ga masu tsananin bukata na tsawon wata shida zuwa shekara daya.

Kuma a shigo da magunguna masu inganci a wadace, a zuba su a asibitoci su ishi marasa lafiya marasa karfi na tsawon shekara a rika raba su kyauta, shekara ta gaba kuma a fara sayarwa a kan rabin kudinsu, har sai komai ya daidaita, kowa ya dawo cikin hayyacinsa.

Don haka wajibi ne gwamnatin Buhari ta gaggauta kaddamar da wannan gidauniya ta musamman domin ceto al’ummar kasar nan daga kuncin da suke ciki. Koda za a kashe kashi 90 cikin 100 na duk dukiyar da gwamnati ta mallaka ne wajen ceto al’umma daga kuncin rayuwa riba ce ga kasar nan. A yi watsi da shawarwarin cibiyoyin Jari-Hujja da kullum suke kokarin Sa gwamnatoci su jefa mutanen kasashenmu cikin ukuba, wato irin su IMF da Bankin Duniya da suke cewa gwamnatocin kasashe masu tasowa su daina bayar da tallafi ga jama’a kan kiwon lafiya da ilimi da man fetur da sauran muhimman kayayyakin bukatun rayuwa, domin ran dan Adam yana gaba da duk wani kayan jin dadi da za a tanada masa, kuma rashin ceto rayuwar al’umma muguwar asarar ce a duniya da Lahira.

Saboda hakan ne ke kara haifar da karuwar miyagu a cikin jama’a, yake sanya masu raunin zuciya ko raunin imani su rasa imanin, marasa imanin, zuciyarsu ta dada kekashewa su yi ta aikata barna da fasadi a bayan kasa, kowa ya rika cewa wayyo!

Tabbas a shekara biyu da suka gabata damina ta yi kyau an samu amfanin gona, alhamdulillahi, an samu abinci. To amma, kada a manta ba fa kowane mutum ne manomi ba. Kuma ko a manoman akwai kanana marasa karfi, sannan ga ’yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati ko na kamfanoni da marasa aikin yi da sauran raunanan jama’a da a yanzu suke cikin kuncin rayuwa suke tsananin bukatar a ceto rayuwarsu.

Lallai akwai bukatar a dubi wannan batu domin talakan Najeriya ya sadaukar da rayuwa da jin dadinsa wajen zaben wannan gwamnati, kuma ya sadaukar da kansa wajen ba ta goyon baya duk da kunci da wahalar da ya shiga. Don haka lokaci ya yi da gwamnatin za ta saka masa.

Zai fi kyau a dakatar da kowane aiki a yanzu a koma ga kyautata rayuwa da jin dadin jama’a, domin duk aikin da za a yi, saboda mutanen ake yi. Idan talaka yana cikin kunci ba zai ga amfanin kwaltar da aka yi a unguwarsu ba, idan yana fama da jinya ba zai damu da burtsatsen da aka yi a unguwarsu ba.

Yanzu ga shi Shugaba Buhari ya amince da karin albashi, don haka yana da kyau sauran jama’a marasa aiki da masu karamin samu a waiwaye su. Ba ma’aikata kadai ne mutane a Najeriya ba, ma’aikatan gwamnati ba su wuce kashi biyu da rabi na al’ummar kasar nan ba, sauran kashi 97 da rabi ko dai manoma ne ko ’yan kasuwa ko masu sana’o’in hannu ko masu aiki a kamfanonin ’yan kasuwa da kila karin zai sa su rasa aikinsu ko ma marasa aikin yi kwata-kwata. To su wane tanadi aka yi musu ko kuwa an bar su da dabararsu in ma mutuwa za su yi su mutu?

Shugaba Buhari da ministocinsa da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa (sanatoci da wakilai) da gwamnonin jihohi da kwamishinoninsu da wakilan majalisun jihohi da shugabannin kananan hukumomi da kansilolinsu kuna da babban nauyi da amana a kanku ta kada ku fifita samun kudi daga ayyukan kwangila a kan inganta rayuwar mutanen da za a yi kwangilar dominsu.

Sai jama’a suna da rai za su hau kwaltar da kuka gina ko su sha ruwan da kuka samar da sauransu, sai suna da lafiya za su ji dadin duk wani abin da za ku iya samarwa. Don haka a fifita kula da rayuwa da lafiyar jama’ar kasa a wannan zubi na gwamnati ko da zai kai ga dakatar da ayyukan gine-ginen hanyoyi da sauransu ne.