Abin da ya biyo bayan hatsaniyar ’yan Shi’a da ’yan sanda a Kano
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi wani dauki ba dadi tsakanin ’ya’yan kungiyar IMN wacce aka fi sani da Shi’a a daidai lokacin da ’ya’yan kungiyar ke gudanar da tattaki a kan titin Zariya a Jihar Kano, a wani bangare na bikin zagayowar ranar jimamin kwana 40 na rasuwar Sayyidina Hussaini (ra). […]

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi wani dauki ba dadi tsakanin ’ya’yan kungiyar IMN wacce aka fi sani da Shi’a a daidai lokacin da ’ya’yan kungiyar ke gudanar da tattaki a kan titin Zariya a Jihar Kano, a wani bangare na bikin zagayowar ranar jimamin kwana 40 na rasuwar Sayyidina Hussaini (ra).
Rahotanni sun bayyana cewa kimanin ’ya’yan kungiyar biyu ne suka rasa ransu yayin da wasu da dama suka jikkata.
A wani taron manema labarai da kungiyar ta IMN ta gudanar, Jami’in hulda da jama’a na kungiyar Ibrahim Musa ya bayana cewa ’yan sanda sun kashe ’ya’yan kungiyar hudu wadanda suka hada da Umar Bako Gano da A’isha Muhamamd Azare da Hussaini Dauda Naladi da cikon na hudun da ba a tantance sunansa ba.
“A ranar Lahadi, bayan mutanenmu sun gama tattaki a daidai gadar Lado, suna shirye-shiryen barin wurin ne sai ga ’yan sanda sun zo wurin; inda suka shiga harba musu barkonon tsohuwa kafin daga bisani su kai ga yin harbi a kansu, inda wasu ’yan uwa suka riga mu gidan gaskiya, wadanda kuma ’yan sandan suka kwashe gawarwakin nasu,” inji shi.
Sai dai Rundunar ’yan sanda a takardar da ta fitar dauke da sa hannun Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Magaji Musa Majiya, ta musanta zargin da kungiyar da IMN suka yi ga rundunar, inda ta bayyana shi a matsayin kage don kawai kungiyar ta samu tausayawa daga al’ummar jihar.
DSP ya kara da cewa kafin aukuwar wannan al’amari, tun da farko rundunar ’yan sandan ta gargadi shugabannin kungiyar da kada su gudanar da wannan tattaki, la’akari da irin yada tattakin yake zama barazana ga rayuwar al’ummar jihar, sakamkon toshe hanyoyi da suke yi. “Sai dai ’ya’yan kungiyar sun sa kafa sun shure wannan gargadi da rundunar ta yi masu, inda suka ci gaba da gudanar da tattakinsu tare da gayyato mutane daga garuruwan Gombe da Jigawa da Borno da Yobe da Bauchi da Taraba da sauran jihohin da ke makwabtaka da Kano. Haka kuma a lokacin da suke gudanar da tattakin, sun rika amfani da gwafar roba suna kuma jifan jami’an na ’yan sanda da duwatsu.”
A cewar Majiya, ’yan sanda sun yi kokarin kwantar da tarzomar, inda suka tarwatsa ’ya’yan kungiyar ta hanyar amfani da abubuwa marasa illa. “Ba mu yi amfani da makamai masu illa ba, ba mu harbi kowa ba, sai dai mun kama mutane goma daga cikin ’ya’yan kungiyar da gwafar danko guda 8 da takardun manufofin kungiyar da wayar hannu guda 3 da wani makami mai guba da risho-risho da takalma da jakar hannu.”
Har ila yau, rundunar ’yan sandan ta jaddada kudurinta na tabbatar da ba ta tauye wa al’ummar jihar ’yancinsu na yin addini ba, sai dai duk da haka, a cewar rundunar ba za ta zuba ido ta kyale masu son tayar da zaune tsaye su fake da rigar addini ba. “Rundunar ’yan sandan Jihar Kano za ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin ta tarwatsa duk wani kokarin da kungiyar IMN ke yi wajen ganin ta mayar da Jihar Kano wata matattara ta gudanar da haramtattun ayyukanta.”
Rundunar ta bayyana cewa tuni dai abubuwa suka koma daidai tare da ci gaba da gudanar da tsaro tare da bibiyar halin da al’ummar jihar ke ciki.