Abin da ya biyo bayan murabus din Ministar Kudi
A karshe dai Ministar Kudi Kemi Adeosun ta yi murabus daga mukaminta sakamakon bankado shaidar bogi kan tsame ta daga aikin yi wa kasa hidima. Ministar dai tsohuwar Kwamishinar Kudi ce a jihar Ogun daga bisani ta zama Ministar Kudin, ba a dai kori Ministar daga mukaminta ba, amma sakamakon cece-ku-cen da ake yi kan […]
A karshe dai Ministar Kudi Kemi Adeosun ta yi murabus daga mukaminta sakamakon bankado shaidar bogi kan tsame ta daga aikin yi wa kasa hidima. Ministar dai tsohuwar Kwamishinar Kudi ce a jihar Ogun daga bisani ta zama Ministar Kudin, ba a dai kori Ministar daga mukaminta ba, amma sakamakon cece-ku-cen da ake yi kan takardar tsame ta daga yi wa kasa hidima, ba tare da wani tashin hankali ba ta mika takardar murabus dinta, bayan fusatar da ta yi na yada jita-jitar da ake yi a kafofin watsa labarai da shafukan sadarwa na zamani hakan zai sa a dakatar yada batun da ake ci gaba da yadawa.
A wasu rahotanni da jam’iyyar adawa ta PDP ke yadawa cewa, wannan babban abin takaici ne ga mai rike da mukamin Minista a kasar nan don haka take bukatar doka ta yi aikinta na tuhumarta da yanke mata hukunci. Sai dai idan za ta samu alfarmar Fadar Shugaban kasa, dokar kasa doka ce a kan kowa, dole ta yi aiki ba a kan Adeosun kadai ba, har da Majalisar Dokoki ta Jihar Ogun da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) wajen wanke ta lokacin da ake tantance ta kafin a mika mata mukamin. Allah Ya albarkaci Najeriya da mutanen da suka cancanci rike manyan mukamai, amma sai wadansu su zo su maye gurbin da bai dace da su ba a karshe a samu gazawarsu.
Duk da magoya bayan da Ministar Kudin ke da su tattalin arzikin kasar bai yi kyau ba. Adadin bunkasar tattalin arzikin bai karu ba. A bangaren yaki da rashawa ya tabbata wa ’yan Najeriya kasar na samun kudade shiga, akwai bayanan da ke nuna cewa, tsohuwar Ministar Man fetur, Diezani Allison-Madueke ta dawo wa kasar nan da Dala biliyan 90, Dubai ta dawo da Dala biliyan 200 da kuma kasar Switzerland ta dawo da Dala miliyan 322 na kudin da Abacha ya boye a kasar.
Buga da kari, akwai rahoton hotunan da ke nuna makudan kudade da aka samu a ofisoshin gwamnati da tashoshin jirgin sama da gidaje da kuma gonaki. Sannan an bayyana nasarar da aka samu a kan kirkirar asusun bai-daya (TSA) inda aka samu rarar kudade sakamakon tushe badakalar da ake yi da kudade; Hukumar Tara Haraji ta kasa (FIRS) ta fadada hanyoyin shigar kudin haraji a bayanan da aka tattara na haraji; Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’o’i ta Najeriya (JAMB) ta samar da kudin shiga da ya kai Naira biliyan 8 yayin da kuma rahoto ke nuna an samu karin adadin kudin shiga daga Hukumar Kwastam daga kudin shigowa da kaya cikin kasar nan. Sai dai wani rahoto na bayyana cewa, an yi rufa-rufa a kan kudaden, sai dai ba a nan lamarin yake ba, Sakatariyar Majalisar dinkin Duniya Amina Muhammed da tsohuwar Ministar Kudi Okonjo-Iweala ta yi nasarar gudanar da wasu hanyoyin taimakon kasar daga fita cikin bashi.
A Oktoban 2005 bayan Najeriya ta biya Dala biliyan 12 daga cikin kudin Kulob din Paris inda aka yi yarjejeniyar yin rangwamen bashin Dala biliyan 18 an dai kammala shirin a ranar 21 ga Afrilu 2006. A lokacin bashin da kasashen waje suke bin kasar nan bai wuce Dala biliyan 3 bashin cikin gida kuma Naira tiriliyan 1. A wancan kwanaki na cikin wani yanayi na karbar basussuka. An dai tara adadin bashin da ake bin kasar lokacin Adeosun da ya kai Dala biliyan 73.21 a ranar 30 ga Yuni 2018. Wannan adadin da ofishin hukumar basussuka suka fitar da Ma’aikatar Kudi ta ce tattalin arzikin kasar yana farfadowa. Amma lokacin Ministar Kudi Adeosun Najeriya ta fada cikin matsin tattalin arziki wanda ba a samu ba a shekara 29. Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar da rahoton cewa rubu’in shekara na 2016 tattalin arzikin kasar na komawa baya tun shekara 25 da suka gabata mafi karanci a cikin talatin, an bayyana Najeriya a matsayin mafi koma-baya a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya cikin masu amfani da kudin gida.
A madadin kowace kasa ta ranto bashin da za ta iya biya, saboda gwamnati ta iya gudanar da harkokinta ne ta hanyar basussuka. Da zarar an bukaci majalisar dokokin kasa ta amince da karbo bashi sai ka ga an gudanar hakan ba tare da bata lokaci ba.
Akwai bukatar karbo bashin sama Dala biliyan dubu 6, ba maganar bashin kudi na Dala biliyan 5.851 da za a ranto daga bankin shige da fice na kasar China na sabunta hanyoyin jiragen kasa Dala miliyan 500 a kan shirin kiyaye abububwan more rayuwa da kuma wani bashi na Dala miliyan 575 don sake gina shiyyar Arewa maso Gabas. Tsohon Kakakin Jam’iyyar APC, Timi Frank ya bayyana wa jama’a yawan bashin da ake bin kasar nan daga waje wanda hakan yana kara wa kasar yawan bashi ya kuma kalubalanci gwamnati a kan rashin iya gudanar da tsarin karbar bashi, idan ’yan Najeriya za su fahimci irin dimbin bashi da ake bin kasar wanda zai iya sa Najeriya mafi talaucin jari a duniya. Don gaskata wannan rahoton bashin majalisar dokoki ta amince da karbar bashin saboda kin bayar da kudin da ke asusun a kan karbo bashin Naira tiriliyan 9.2 a shekarar 2016. Gwamnatin ta ce karbo bashin na da muhimmanci wajen amfani da su a biyan albashi da kudin fansho da biyan alawus din ma’aikata da bashin dillalan man fetur da ’yan kwangila da masu dako da bashin shari’a da kudaden wuta da za a biya sannan a mai da wa gwamnatin jihohi don wani shiri na a madadin Gwamnatin Tarayya.