Abin da ya faru bayan kama ni –Malam Bello Yabo

Sanannen malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Sakkwato, Malam Bello Yabo, wanda ’yan sanda suka kama kafin Sallah, ya ce lokacin da aka dauke shi ya zata Abuja za a kai shi amma sai ya ga an tsaya a Kaduna. Kwana daya da sako shi wakilinmu ya iske shi a masallacin kofar gidansa yana yi […]

Abin da ya faru bayan kama ni –Malam Bello Yabo

Malam Bello Yabo

Sanannen malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Sakkwato, Malam Bello Yabo, wanda ’yan sanda suka kama kafin Sallah, ya ce lokacin da aka dauke shi ya zata Abuja za a kai shi amma sai ya ga an tsaya a Kaduna.

Kwana daya da sako shi wakilinmu ya iske shi a masallacin kofar gidansa yana yi wa wadansu mutane bayani a kan yadda lamarin ya kasance, inda ya ce ’yan sandan sun zo gidansa ne suka nuna masa takardar gayyata cewa Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya yana nemansa.

Ya ce  ya dauka hedkwatar ‘’yan sanda ta kasa da ke Abuja za a tafi, sai suka tafi hedkwatar ’yan sandan Kaduna, inda a nan aka ba shi takardar tuhume-tuhumen da aka yi masa guda bakwai, amma nan take ya karyata su gaba daya.

Bayan nan ne, a cewarsa, aka ba shi takarda ya rubuta jawabinsa kan tuhumar da ake yi masa, amma ya tabbatar musu ba zai karbi kowace tambaya ba domin ba a makaranta yake ba.

“Na fada musu karara cewa na rubuta jawabina a nan kuma in suka bari na rike takardar zan keta ta, ni ba dan Kaduna ba ne, ba a nan na yi laifin da suka ce suna tuhuma ta ba, don haka ba wata tambaya da zan amsa tun da ba a makaranta nake ba.

“A daren, Kungiyar Lauyoyi Musulmi ta Jihar Kaduna a karkashin jagorancin shugabansu suka zo domin su tsaya a maganata, ba tare da sun san lauyana a jihar yake ba, kuma ya san da maganar kafin mu zo,” inji shi.

Yadda manya suka samu labari

Malam Bello Yabo ya ce a ranar Asabar da safe Kwamhinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna ya zo ofis aka kira shi tare da mukarrabansa ya fada musu kada su walakanta shi don bakonsa ne su sama masa wuri mai kyau kada su mayar da shi bayan kanta.

Ya ce daga baya ne manya suka samu labarin kama shi suka fara kiran waya.

Ya ce Mininstan Shari’a Alhaji Abubakar Malami da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet Sheikh Isa Ali Pantami da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sakkwato duk sun yi magana da Gwamna El-Rufa’i kan a sake shi amma ya ki amincewa.

“Sai a ranar Lahadi ne Ministan Shari’a bayan ya nemi Kwamishinan ’Yan Sanda ya bayar da ni beli, sannan ya yi magana da Sufeto Janar ya kira Kwamishinan aka bayar da ni beli da karfe 9 na dare ranar Lahadi.

“Lauyana ya zo muka cike takardun da aka ba mu, na bar hedkwatar da daren tare da rakiyar wani dan sanda, saboda akwai dokar hana yawo a jihar.

“A zaman da na yi wurin ba wanda ya ci zarafina,” inji shi.

‘Makirci aka shirya’

Tun da farko dai malamin ya ce kama shi wata kullalliya aka shirya.

“Makirci aka shirya a kama ni, Allah Ya kubutar da ni, amma ya kamata su sani duk abin da ake yi duniya na yi ba abin da nake tsoro.

“Na zauna gidan yari tsawon shekara biyar, na rasa Sallar Idi 10 a lokacin da nake tsare kuma a Sakkwato nake ba wani wuri ba.

“Wannan kwana ukun shirme da wasa na dauke su, kuma wannan kamen ya zamar min alheri a rayuwa — in da ina da mabiya ko masoya 1,000 yanzu sun koma 5,000.

“Bayan nan Sakkwato da take gida na samu labarin dukkan masallatan Ahlus Sunnah da ke Kano sun yi min addu’a.”

‘Duk Najeriya…’

Malamin ya ci gaba da cewa ba a yi wa iyalansa da wadanda ke karkashinsa adalci ba domin an hana ya kammala musu bukatun Sallah alhali an san an tsara ba za a bar shi ya yi Sallah cikinsu ba.

“Duk Najeriya babu wanda ya isa ya hana ni yin wa’azi domin shi ne hanyar da na zaba; na gode wa Allah ba a kama ni don na yi sata ko neman matar wani ba sai don na yi wa’azi kuma ba zan bar wa’azi ba har karshen rayuwata.”

Ya gode wa wadanda suka nuna damuwa kan tsare shi musamman Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Jihar Kaduna da Ministan Shari’a da Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun da Sheikh Isah Ali Pantami da Malam Murtala Bello Assada wanda ya nada Sarkin Yakin Bello Yabo da sauran jama’a.

Bello Yabo bayan ya kammala bayanin ga mutanen, wakilinmu ya nemi tattaunawa da shi, ya ce, “Ai ni ba na magana da ’yan jarida sai dai ka ji bayanin da na yi za ka iya amfani da shi.”