Abin da ya haddasa rikicin da ya jawo asarar rayuka a Bauchi

A ranar Lahadin da ta gabata ce mutane uku suka rasa rayukansu sannan wasu 18 suka samu raunuka tare da kone gidaje biyu a yayin wani yamutsi da aka samu tsakanin wasu kingiyoyin matasa a wurin wani bikin murnar ranar haihuwa wani mutum da ba a fayyace sunansa ba. An samu mabambantan bayanai kan musabbabin […]

Abin da ya haddasa rikicin da ya jawo asarar rayuka a Bauchi

Abin da ya haddasa rikicin da ya jawo asarar rayuka a Bauchi

A ranar Lahadin da ta gabata ce mutane uku suka rasa rayukansu sannan wasu 18 suka samu raunuka tare da kone gidaje biyu a yayin wani yamutsi da aka samu tsakanin wasu kingiyoyin matasa a wurin wani bikin murnar ranar haihuwa wani mutum da ba a fayyace sunansa ba.

An samu mabambantan bayanai kan musabbabin rikicin wanda ya faru a Unguwar Lukshi da ke Yalwa a Karamar Hukumar Bauchi, inda wasu ke ganin rigimar ta faru akan wata mace ce yayin wadansu ke cewa a’a.

Wani wanda aka yi yamutsin a idonsa ya shaidawa manema labarai cewa rikicin ya tashi tsakanin mutane biyu dake soyayya da wata budurwa ce, yayin da wannan budurwar ta ga fada ya barke sai ta sulale ya gudu, lamarin da ya jawo rasa rayuka da dukiyoyi, kuma ’yan sanda sun kama mutane 75 da ake zargi da hannu cikin rikicin.

Sakamakon wannan rikici ne ya jawo Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanya dokar hana fita a wadannan unguwanni guda biyar dake kewaye da Yelwan Makaranta daga karfe bakwai na dare zuwa karfe shida na safiya. Unguwanni da wannan doka ta shafa sun hada da Kagadama da Yelwan Tsakani da Unguwar Kusu da Lushi da Unguwar Ngas.

Alhaji Murtala Ibrahim shine Sarkin Yalwa, ya shaidawa Aminiya cewa ya samu labarin abin da ke faruwa kuma har da rasuwa da jin ciwo, amma rikicin ya faru ne a unguwannin dake kewaye da Yelwa ba a cikin Yalwa inda yake sarauta ba.

Sarkin ya ce ire-iren wadannan rikici na faruwa sai a dauka a Yelwa ne amma a hakikanin gaskiya ba haka ba ne, amma gwamnati ta tura jami’an tsaro kuma abin ya lafa.

Wani mazaunin unguwar Lushi, ya shaida wa ’yan jarida cewar daya daga cikin wadanda suka rasa ransu a sakamakon wannan rikicin, ma’aikaci ne a sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Bauchi. Kuma ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya ke kokarin kubutar da iyalansa daga rikicin, “a lokacin da ya debi iyalansa domin kaisu wani gida don kubutar da rayuwarsu ne, sai ya gamu da gangamin masu rikicin inda suka kashe shi suka kuma kona gidansa,” inji shi.

Wani mazaunin unguwar ya ce wasu bata gari sun yi kokarin maida rikicin na addini domin sun kona wani tsohon masallaci a wajen makarantar Sakandaren Baban Takko, amma jami’an tsaro da aka turo sun magance lamarin.

Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammadu Abdullahi Abubakar ya zaga wadannan unguwanni da wannan rikici ya faru, inda ya jajantawa al’ummar ya kuma hore su da su zauna lafiya da juna su guji daukar doka a hannunsu.

Da yake bayanin yadda lamarin ya faru, Sarkin YelwanTsakani, Mista Philip T. Tapshin, ya shaida yadda lamarin ta samo asali, ya bayyana cewar tun da fari ma sun hana irin wannan shagalin da zarar dare ya yi domin kare lafiyar jama’ar yankin.

Ya ce, “wani ne wai zai yi bikin tunawa da ranar haihuwar dansa, mai unguwar da ke wannan yankin ya yi masa magana, domin mun sanya doka kan cewar daga karfe hudu na yamma ba mu son jin kowane irin kida da raye-raye na biki ne ko na wani abu daban, domin jama’a suna dawowa daga wuraren aiki don hutawa. Ba mu son tashin hankali kowa da kowa ya gamsu da wannan matsayar da aka cimma.”

Sarkin ya ce “a ranar wajen karfe 11 na dare na ji cewar ana biki, sai na kira mai gundumar na ce masa me yesa ya bari ana biki alhali akwai doka, na ce masa a hana su yin bikin domin mu bamu son wani tashin hankali ya zo ya sake faruwa. Kafin wani lokaci kawai sai na ji labarin wai sun fara saran junansu,”

Sarkin ya kuma nuna takaicinsa a bisa yadda wasu da ba su ji-basu-gani ba rikicin ya rutsa da su, “Ina jin takaicin mutanen da basu san hawa ba basu san sauka ba da aka kashe su a sakamakon wannan rikicin,” inji shi.

Sai ya gargadi dukkan matasan da suke kokarin kawo tashin hankali a yankin da su daina, don kuwa ba za su zura ido wasu na janyo asaran rayuka ba, ya kuma koka da yadda wasu iyayen suke goyon bayan ’ya’yansu koda sun yi ba daidai ba.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar mutane uku, inda kuma mutane 18 suka gamu da munanan raunuka. Kakakin Hukumar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar shine ya tabbatar da hakan a hirarsa da ’yan jarida.

Ya ce, sun kama mutane 75 da suke zargi da haddasa wannan rikicin. DSP Abubakar ya ci gaba da bayanin cewar rikicin ya samo asali ne a sa’ilin da rashin fahimta ta kunno kai a wajen wani bikin tunawa da ranar haihuwa.

Kakakin ‘yan sandan ya shaida cewar gidaje guda biyu ne aka kona sakamakon rikicin, ya ce ’yan sanda zasu ci gaba da gudanar da aikinsu na kare doka da oda. Sai ya yi gargadin cewa duk wanda suka kama da yunkurin tada zaune tsaye zai dandana kudarsa. Ya kuma bayyana cewa wannan rikici bashi da alaka da rikicin addini.