Abin da ya haddasa rushe Kasuwar Alaba Rago — ’Yan Arewa

An ɗora laifin hakan a kan ’yan Arewa shugabannin kasuwar.

Abin da ya haddasa rushe Kasuwar Alaba Rago — ’Yan Arewa

Masu harkokin kasuwanci a Kasuwar Alaba Rago sun wayi gari a farkon makon nan da rusau a kasuwar da ke matsayin matattar ’yan Arewa.

Rusau ɗin da aka kwashe kwana uku a jere ana yi ya jefa ’yan kasuwar a cikin mummunan tashin hankali lura da yadda suka yi asarar rumfunansu, wasu kuma suka yi asarar kayayyakinsu kacokan.

Aminiya ta ziyarci kasuwar inda ta tattauna da wasu ’yan kasuwar da suke ƙoƙari kwashe ɗan abin da ya rage na kayayyakinsu a cikin buraguzan gini, wasu kuma ke ƙoƙarin kalace ragowar kayan ginin rumfunansu da suka haɗa da ƙarafa da kwanon rufi da sauransu.

Ɗaya daga cikin ’yan kasuwar Malam Jibrin Hassan Alhassan, ya bayyan yadda ya ji da wannan lamari kasancewar shi haifaffen Legas ne in ji shi.

Sai dai ya ɗora laifin hakan a kan ’yan Arewa shugabannin kasuwar.

“Tun ina ƙarami mahaifina ke zuwa da ni wannan kasuwa, haka na taso na gaje shi, ni da sauran ’yan uwana.

“Ba mu san ko’ina ba sai wannan kasuwa, amma lokaci guda mun wayi gari mun samu kanmu a cikin wannan hali na rushe mana kasuwa, gaskiya wannan abin takaici ne.

“Kodayake ba laifin kowa ba ne, laifin shugabannin kasuwar ne da suka kasa haɗa kansu waje guda, wanda ya janyo mana wannan masifa, saboda sun kasa yin aiki tare don ci-gaban wannan kasuwa, kowanensu ya biye wa son zuciya da kwaɗayin abin da zai samu.

“Dalilin da ya sa na ce haka kuwa shi ne, shekara biyu da suka wuce gwamnatin Legas ta sahale wa ’yan kasuwar Alaba Rago su gyara kasuwarsu da kansu, amma shugabannin suka gaza haɗa kansu waje guda domin su yi aikin gyaran.

“Kowane sashe na baƙin cikin abin da wani sashen zai samu, wasu na ganin cewa su ne waɗanda za su yi aikin gyaran zai sa su yi arziki, sai hassada da ƙeta ta shigo.

“A haka koyaushe in na karanta a jarida manufofin gwamnati a kan wannan kasuwa ina ankarar da su, ina fassara musu abin da gwamnati ta ce ba ta son gidajen karuwai a cikin kasuwa domin suna bai wa ɓatagari mafaka, har makamai an sha kamawa.”

Ya ce, “Amma maimakon a mai da hankali a yi gyaran kamar yadda gwamnati ta ba da dama, sai aka koma gefe ana hammayar shugabanci da ɓangaranci.

“Wasu ba sa so a yi gyara sai an sauya shugabanni, ana cikin haka ne ba zato, ba tsammani aka zo aka yi wannan rusau.

Yanzu da aka rushe kasuwar sun ce in sun gina za su sayar wa ’yan kasuwa ne, ko su bayar haya, ka ga idan suka zuba kuɗi mai yawa wanda ba ya da hali dole ya haƙura, don haka wa gari ya waya?”

Alhaji Malami Muhammad ɗaya daga cikin shugabannin kasuwar a baya, ya ce rashin haɗin kan shugabannin kasuwar ne ya haifar da halin da ake ciki marar daɗi.

“Gabanin a yi babban zaɓe na ƙasa gwamnatin jihar da ɗan takarar da Shugaban Ƙasa ta hanyar Mataimakinsa Kashim Shettima da Hadiza Bala da saura shugabannin ’yan Arewa mazauna Legas da suka haɗa da Sarkin Hausawan Legas da Sarkin Fulanin Legas an yi yarjejeniya tare da sahale wa ’yan Kasuwar Alaba su gyara kasuwarsu tare da sabunta gininta. Amma abin ya faskara.

“A baya duk ƙoƙarin da ake yi na cike takardu da ni aka yi, babu ofishin da ba mu je ba na gwamnatin Legas inda muke neman a ba mu damar sake gina kasuwar.

“Akwai shugabannin ’yan Arewa waɗanda sun yi shirin tsaya mana da kuɗi su sake gina mana ita.

“Amma bayan tafiya ta yi nisa, sai muka samu labarin wasu daga cikin shugabannin kasuwar sun je sun haɗa baki da tsohon ɗan kwangilar da aka taɓa yi wa tayin sake gina kasuwar.

“Suka ɗauko shi ya fara aikin rushe wa jama’a rumfunansu, abin tsoron da muke ji wa jama’a da kanmu baki ɗaya shi ne wannan ɗan kwangila a wancan lokaci tsarin kasuwar da ya kawo babu tanadi ga masu harkar dabobbi, kuma ba ta yi daidai da irin namu tasiri ba.

“Don haka idan suka bari kasuwar ta kuɓuce mana, babu sauran maganar shugabanci balle rikici ko rarrabuwar kai a kan shugabanci,” in ji shi.

Alhaji Malami ya ce sakamakon rusau da aka yi a kasuwar, wata mace da aka rushe rumfarta ta faɗi nan take ta mutu, baya ga mutane da dama da suka suma.

Wasu ciwon hawan jininsu ya tashi saboda asarar da suka tafka.

A ƙarshe ya yi kira ga mahukunta su bai wa jama’ar kasuwar damar zama a wani yanki a daidai lokacin da ake aikin sabunta ganinta.

Ya ce bai wa ’yan kasuwar damar gina kasuwar da kansu shi ne zai hana kuɓucewar kasuwar daga ainihin masu rumfuna a cikin kasuwar.

A ɓangaren Sarkin Kasuwar Alhaji Umar Nagwaggwo cewa ya yi rushe kasuwar ta zo wa jama’a da ba-zata kuma tun lokacin da abin ya faru ba ya jin daɗin jikinsa saboda takaici.

Zuwa yanzu ’yan kasuwar na ci-gaba da lissafin asarar da suka yi a rusau ɗin, yayin da wasu ke fatan kada a rushe ta baki ɗaya domin su samu wajen fakewa, kafin a sabunta ginin.

Wasu na ganin gaba ɗayanta za a rushe, duba da yadda aka faro aikin rusau ɗin babu kaukautawa.

Har yanzu gwamnatin jihar ba ta ce komai ba dangane da rushe kasuwar wataƙila saboda ta yi zama da shugabanninta a lokuta daban-daban don neman mafita amma kwallliya ba ta kuɗin sabulu ba.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania