Abin da ya haifar da juyin mulki a Sudan
Kasar Sudan a baya-bayan nan ta shiga wani mawuyacin hali sakamakon juyin mulki da sojojin kasar suka yi wa gwamnatin Janar Abdel Fattah a ranar Litinin. Aminiya ta tattauna da wani mazaunin kasar Sudan dan asalin Najeriya, Dokta Shu’aibu Shehu, inda ya bayyana abubuwan da yake ganin sun haifar da dambarwar da kasar ke ciki […]
Kasar Sudan a baya-bayan nan ta shiga wani mawuyacin hali sakamakon juyin mulki da sojojin kasar suka yi wa gwamnatin Janar Abdel Fattah a ranar Litinin.
Aminiya ta tattauna da wani mazaunin kasar Sudan dan asalin Najeriya, Dokta Shu’aibu Shehu, inda ya bayyana abubuwan da yake ganin sun haifar da dambarwar da kasar ke ciki a yanzu.
Ka yi mamakin jin an yi juyin mulki a Sudan?
Gaskiya ban yi mamaki ba saboda duk mutumin da ke bibiyar harkoki da ke tafiya a Sudan, tun daga wancan lokaci da aka yi juyin mulki na farko har zuwa yanzu ba zai baka mamaki ba, saboda na farko dai abubuwa sun jagule a baya-bayan nan, harkokin rayuwa sun tabarbare a Sudan.
Sannan harkokin siyasa sun tabarbare a Sudan, saboda a baya matasa ne suka jagoranci juyin juya hali a wancan lokaci, bayan sun shigo ciki aka dinga samun dagwalon siyasa har aka kai lokacin da aka hambarar da wannan Hambuk.
To daga bisani ’yan siyasar kasar sun kasu kashi biyu: Wadansu suna goyon bayan Hambuk da ’yan majalisarsa.
Wadansu kuma suna goyon bayan dole sai shi Hambuk ya sauke majalisar kasar, amma sun yarda ya ci gaba da jagorancin kasar, ba su yarda da ’yan majalisarsa ba, suna masa zargin cin hanci da rashawa da lalacewar al’amura a kasar Sudan.
Wannan ya kawo aka dinga zanga-zanga, zanga-zangar da aka yi ranar Abasar din da ta wuce.
Wadanda suke goyon bayan sai Hambuk ya sauka ko ya sauke ’yan majalisarsa suka je suka yi zanga-zangar suka kafa tanti a ‘Shahra Jami’a’ suka ce ba za su fice daga nan wajen ba har sai Hambuk ya sauka ko kuma ya sauke ’yan majalisarsa, in za su yi kwana bakwai ne ko wata da yaba za su gushe ba.
Bayan an yi wannan, ranar Alhamis sai aka samu ‘Muzahara’ mai girman gaske, magoya bayan Hambuk suka fito suka yi ‘Muzahara’ da wadanda suke goyon bayan sojoji da wadanda suke goyon bayansa suka fito suka yi ‘Muzahara’.
Wannan Muzahara an yi ta a fadin Khartoum, saboda haka idan an ce an yi juyin mulki a Sudan ba wani abu ne da zai baka mamaki ba.
Yaya aka yi har aka zo ga wannan matsayi?
Na farko dai tattalin arzikin kasar ya karye, an samu tabarbarewa rayuwa, an samu karin hauhawar farashin kayan abinci, rayuwa ta kazanta ta wahala.
Zan ba ka misali a shekara shida da suka wuce lokacin da ake zargin Al-Bashir ya hau gadon mulki, za ka sayi Esh wanda shi ne rayuwar ’yan Sudan, in ka ba da Junay guda daya za a baka Esh guda shida.
Amma ina gaya maka a halin da ake ciki yanzu Esh din nan ta koma fam hamsin, ka ga rayuwa ta kazanta.
Harkokin shige da fice da suka shafi motoci ko ababen hawa, za ka bada fam daya ne.
Ina gaya maka a yanzu duk inda za ka je a kasar Sudan mafi karanci shi ne zaka bada Junay 150.
To ka ga wahala ta kazanta, ka ga matsayin mutane sai dai su dinga tafiya a kasa ba ma a maganar a ci a sha.
Me kake ganin zai biyo baya tunda ga shi yanzu sojoji sun karbi mulkin kasar?
To, gaskiya kam abin da zai biyo baya Allah kadai ne Ya san abin da zai biyo baya domin na farko ka san kungiyoyin majalisar da wasu kasashen turawa da wasu kasashen Afirka sun ce sun yi Allah wadai da wannan juyin mulki da aka yi.
To tunda sun yi Allah wadai ka ga ba su yarda su goya wa sojoji baya ba.
Sannan ana kara harzuka mutanen kasar cewar dole su kare Dimokuradiyya, to amma mulkin Dimokuradiyya me ya haifar a kasar?
Bai haifar da komai ba, musamman wannan yanayi da ake ciki saboda haka Allah ne kadai Ya san me zai faru saboda mutane sun watsu a kan titi.
Amma fa akwai wasu da suke goyon bayan juyin mulkin da aka yi, to me zai faru wannan Allah ne kadai ya sani.
A ganinka kifar da gwamnatin Omar Al-Bashir ta taka rawa wajen haifar da yanayin da kasar ke ciki a yanzu?
Wallahi tabbas duk wanda zai fadi gaskiya game da abin da ke faruwa a Sudan a yanzu, akwai abin da muke magana har kullum shi ne ‘Islamic Political Thoery’ wato ainihin shi Musulunci bai yarda da ’yan tawaye ba, bai yarda da a yi wa shugaba tawaye ba ko da kuwa shugaban azzalumi ne.
Saboda yanzu an yi ‘Muzahara’ me ya haifar in banda rikici, ya dawo da rikicin siyasa to mene ne amfanin shi.
Shi mutumin nan ya kare kasar, dama su abin da suke so shi ne su rusa kasar saboda kasa ce da ta aiwatar da shari’ar Musulunci, amma yanzu an rusa kasar baki daya ba zaman lafiya, ana kashe-kashe a kasar.
Yara kuma da ake son amfani da su an rusa rayuwarsu baki dayanta.
Ya kamata a bi Al-Bashir ta hanya ta ka’ida da za a samar da shugabanci mai kyau, amma sai aka yi amfani da yara aka ba su kwayoyi aka shiga wannan ‘Muzaharar’.
Me ya haifar? Sai rikici kamar abin da ke faruwa a kasar Libya, Siriya.
Kuma abun da ya kamata sauran kasashen Afirka ya kamata su lura shi ne ana so a yi amfani da su a rusa kasashensu.
Irin haka ce taso faruwa a Najeriya lokacin #EndSARS, amma Allah Ya taimake mu muka shawo kan abin da ya faru a Najeriya.
Da abin da yake faruwa a kasashen Sudan da Libya da abin da yake faruwa a Najeriya a yanzu ke nan, ba mu da shugabanci, ba mu da zaman lafiya, wanda turawa za su samu damar satar dukiyar kasarmu.
Yanzu kana tunanin za a iya samun masalaha tare da mayar da kasar kan turbar Dimokuradiyya?
Eh insha Allahu za a samu masalaha.
Ni abin da nake so da kasashen Afirka da sauran kasashen duniya su mara wa sojoji baya da farar hula a yi zabe lafiya, in har suna son kasar saboda a yanzu a halin da ake ciki, tun farko lokacin da aka yi waccan ‘Muzahara’ matasa cewa suka yi sai dai a mika musu mulki.
Ya za a yi a mika wa matasa mulki a wannan halin da ake ciki, waye ne ma za ka mika wa mulki?
Amma a yanzu an riga an samu juyin mulki a kasar, babban abin da kasashen duniya ya kamata su yi in har da gaske suna son zaman lafiyar kasar da dorewar kasar Sudan, su hadu su mara wa sojojin baya a yi zabe lafiya a mika wa farar hula, ba wai a ce an ingiza wasu mutane suna yin tawaye suna rusa kasar ba.
A tunaninka zuwa yaushe wannan masalaha za ta iya samuwa?
Idan Allah Ya sa aka samu hadin kan ’yan siyasa da dukkanin wadanda ke da hannu a kasar aka hada kai, wannan ba wani abu ne da zai kawo matsala ba.
Sudan dai kasarsu ce ba su da wata kasa da wuce ta, saboda haka mulkin soja dole ne a samu wanda zai daidaita al’amura ba wai dole abin da ake so ba shi ne zai rika faruwa ba.
Su ya kamata su zauna su tattauna a samu masalaha wannan shi ne abin da ya dace.
Kasashen duniya sun yi Allah wadai amma wace masalaha suka kawo ko so suke a dawo a ci gaba da rikici?
A baya-bayan nan kana kasar Sudan, kafin ka dawo Najeriya a wane irin yanayi kasar take ciki?
Wallahi duk wanda ya san kasar a shekara shida da suka wuce wallahi sai ya zubar da hawaye saboda lalacewar al’amura.
Na gaya maka hauhawar farashin kayayyaki, saboda shekara shida da suka wuce canjin Dala za ka bada Dala 100 a baka Junay guda 600 ko 700 a yanzu halin da ake ciki za ka bada Dala 100 a baka Junay dubu 45.
Za mu shiga otal mu ci abinci mai kyau Junay 25, yanzu na shiga wajen cin abinci mai kyau na ci abinci kan Junay 3,000 ko 4,000.
Ka ga wannan ba karamin tashin hankali ba ne, ba karamar fitina ba ce.
Al’amura sun zama tashin hankali, musamman a kauyukansu, don haka wannan ba karamar fitina ba ce a kasar Sudan.
Ga yunwa ta yi yawa, wannan shi ne ya sa mutane suka watsu a kan titi suna ‘Muzahara’ suke ganin cewa dole sai an samu sauyin gwamnati.