Abin da ya haifar da karanci mai – Sakataren IPMAN
Alhaji danladi Garba Pasali shi ne Sakataren kungiyar dillalan mai ta Nijeriya (IPMAN). A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana matsalolin da suka kawo karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan. Amma ya bayar da tabbacin cewa, nan da ’yan kwanaki za a warware wannan matsala. Ga yadda […]

Alhaji danladi Garba Pasali shi ne Sakataren kungiyar dillalan mai ta Nijeriya (IPMAN). A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana matsalolin da suka kawo karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan. Amma ya bayar da tabbacin cewa, nan da ’yan kwanaki za a warware wannan matsala. Ga yadda tattaunawat ta kasance:
Aminiya: Mene ne ya kawo karancin man da ake fama da shi a kasar a halin yanzu?
danladi Pasali: Wato abin da ya kawo matsalar man fetur da ake fama da shi a kasar nan, shi ne an samu matsaloli ne kamar guda uku. Matsala ta farko ita ce hasashen da mutane suke tayi kan cewa za a rage kudin mai, ko kuma za a kara farashin kudin mai a kasar nan. Irin wannan hasashe da kuma tsoratar da mutane cewa babu mai, ya taimaka wajen kawo wannan matsala. Amma gaskiyar magana akwai mai a kasar nan, Jiragen ruwa suna nan dauke da man fetur a Legas. Kuma yanzu ina magana da ko’odinetocinmu na Legas da Fatakwal da Warri a inda suka sheda mani cewa suna nan suna lodin mai.
Amma wannan tsoratarwa da aka rika yi wa jama’a cewa za a rage farashin mai ko kuma za a kara farashin mai shi ne ya tsoratar da jama’a. Don haka za ka ga mutane suna ta sayen mai suna boyewa a gidajensu. Kuma idan an lura a duk karshen shekara ana samun irin wannan matsala, don haka kada mutane su daga hankalinsu kan wannan al’amari.
Bayan haka akwai matsalar da aka samu kan maganar cire tallafin mai don haka mutane da yawa ba sa kawo mai. Kuma sannan mu wannan kungiya da kanmu mun bai wa ‘yan kungiyarmu umarnin su daina sayo mai. Domin a kowanne lokaci ’yan kungiyarmu suna sayo mai a Legas kan farashin Naira 87 zuwa Naira 90. To ka ga idan mutum ya je ya sayo mai a Naira 90 a Legas ko a Fatakwal yaya zai yi ya kawo Arewa ya sayar Naira 87? Don haka muka ja kunnen ’yan kungiyarmu cewa idan ba an samu man gwamnati ba kada su saya.
Yanzu komai ana son a bi ka’ida ne, domin an samu shugaba mai son a bi ka’ida. Don haka mu ma mun ce dole ne mutanenmu idan ba sun samu mai mai sauki ba, kada kowa ya je ya sayo man da yake da tsada. Saboda mu ma ba ma son mutanenmu su sayar da mai ba farashin gwamnati ba.
Matsala ta biyu kan wannan al’amari shi ne, kudaden dakon da gwamnati take biyan masu dakon mai daga kudancin kasar nan zuwa Arewa. Saboda mafi yawan man da ake daukowa ana dauko shi ne daga Legas ko Fatakwal ko Warri. Mutum ne ya dauko mai daga Legas ko Fatakwal ko Warri ya kawo Kano ko Kaduna ko Katsina ba a biya shi ba. A halin da ake ciki sashin da suke biyan kudin dakon nan suma a rude suke. Saboda yadda gwamnatin tarayya ta janye kudaden kasar nan zuwa babban bankin Nijeriya. Saboda haka a yanzu maganar da ake yi an kwana biyu ba a biya masu dauko man nan ba.
Aminiya: To yaya kuke ganin yadda hukumar lura da albarkatun man fetur [DPR] take gudanar da ayyukanta?
danladi Pasali: Damuwar ita ce fiye da shekaru 20 wannan hukuma ta DPR ba ta aikinta. Amma a wannan karon tana aikinta, shi yasa ake ganin kamar aikinta ya yi zafi, amma gaskiyar magana tana aikinta a kan ka’ida. Dama ita doka ce ta ba ba ta damar cewa kada ta bari a sayar da mai sama da farashin da gwamnati. Tun da a yanzu ta tsaya tana aikinta shi ne ya sa kowa yake jin zafin abin.
Aminiya: Ina maganar kudaden tallafin da gwamnati ta ba ku wanda kuke bi bashi a kwanakin baya?
danladi Pasali: Ka san matakan bayar da kudin gwamnati suna da yawa, domin a yau idan shugaban kasa ya ce a bayar da kudi ba wai nan take za a ce a dauko kudin a bayar ba, dole sai an bi matakai tukuna, don haka har yanzu wadannan kudade ba su shigo hanunmu ba.
Aminiya: Ina maganar matatun mai masu zaman kansu da aka bai wa wasu kamfanoni izinin ginawa a Nijeriya?
danladi Pasali: Matatun mai masu zaman kansu guda 60 da gwamnati ta ba da izinin kafawa a kasar nan, muna godiya ga shugaban kasa Muhammad Buhari, domin mu ma muna cikin wadanda aka bai wa izini. Yanzu muna da wuri a jihohin Kogi da Bayalsa wadanda za mu gina wadannan matatun mai. A kalla wadannan matatu masu zaman kansu da gwamnati ta bada izinin ginawa sai an kai kamar watanni 8 zuwa shekara 1 kafin a kammala aikinsu. Kuma wannan gwamnati ta yarda za ta sassauta wa wadannan matatu farashin kudaden danyen man fetur. Don haka ina mai tabbatar maka idan wadannan matatu suka soma aiki an daina wahalar mai a Nijeriya.
Aminiya: A karshe, wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Nijeriya?
danladi Pasali: To ina shawartar gwamnatin Nijeriya ta kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki kan harkokin mai don a tattauna wannan matsala a magance ta. Musamman maganar kudin dakon nan da ba a biya, idan ba a biya wadannan kudade ba za a cigaba da samun wannan matsala. Kuma ina son in yi kira ga ’yan Nijeriya kada su daga hankalinsu kan wannan al’amari, domin akwai mai a Nijeriya, ’yar damuwar da aka samu ta yadda za a dauko wannan mai ne. Don haka idan Allah Ya yarda nan da ’yan kwanaki za a warware wannan matsala ta mai a Nijeriya.