Abin da ya haifar da rashin wuta a Arewa — TCN

Kamfanin ya ce matsalar ta shafi yankunan Arewa Maso Gabas, Arewa Maso Yamma, da kuma wasu yankuna na Arewa ta Tsakiya.

Abin da ya haifar da rashin wuta a Arewa — TCN

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya ce wata matsala ce ta auku a kan layin lantarki na Ugwaji-Apir mai ƙarfin 330kV.

TCN ya ce wannan shi ne abin da ya yi sanadin rashin samun wuta a Arewacin Najeriya.

“Da misalin ƙarfe 4:53 na safiya ne layin lantarkin Ugwuaji zuwa Makurdi na biyu mai ƙarfin 330kV ya samu matsala.

“Sai aka tura lantarki mai ƙarfin megawat 243 zuwa layi na ɗaya a layin domin ci gaba da samar da wutar.

“Shi ma da misalin ƙarfe 4:48 na safiya ya samu matsala, wanda hakan ya sa aka rasa lantarki mai yawan megawat 468.

“Da misalin ƙarfe 5:17, mun sake gwada layi na ɗaya da na biyun, amma dukkansu suka sake samun matsala a tare.”

Kamfanin ya ce matsalar ta shafi yankunan Arewa Maso Gabas, Arewa Maso Yamma, da kuma wasu yankuna na Arewa ta Tsakiya.

A makon da ya gabata ne babban layin samar da wutar lantarki na Najeriya ya lalace har sau uku cikin mako guda, abin da ya jefa duka ƙasar cikin duhu.

Rashin wuta lantarki a Najeriya na ci gaba da ta’azzara, lamarin da ke durƙusar da ƙananan sana’o’i da jefa miliyoyin mutane cikin duhu.

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa

Rikicin Masarauta: Kotu ta yi watsi da ƙarar Aminu Bayero