Abin da ya haifar da yakin basasar Kano
Al’amarin da ya haifar da yakin basasar Kano, kamar yadda tarihi ya nuna Galadima Yusufu mutane ke so ba Alu ba. A lokacin yana zaune a garin Garko, kuma a can ya mutu. Kafin rasuwarsa, kowa ya yi amannar cewa shi ne zai zamo Sarki, amma sai ciwo ya kamashi har ya mutu a Garko. […]
Al’amarin da ya haifar da yakin basasar Kano, kamar yadda tarihi ya nuna Galadima Yusufu mutane ke so ba Alu ba. A lokacin yana zaune a garin Garko, kuma a can ya mutu. Kafin rasuwarsa, kowa ya yi amannar cewa shi ne zai zamo Sarki, amma sai ciwo ya kamashi har ya mutu a Garko.
Daga nan sai sarakunan bayin Sarki da ‘ya’yansu suka ce yanzu mene ne abin yi? Sai wasu suka ce abu daya ya kamata mu yi, mutum daya ne kurum zai iya jagorantar mu zuwa Kano, shi ne Mallam Babba, Alu ke nan. Daga nan suka aika masa, sannan suka dora shi a gadon Mulkin Yusufu.
Bayan sun yi haka, da dare suka binne Yusufu da hasken fitilu. Suka kawo Alu suka zaunar da shi a kan karagar mulki. Suka yi masa nadi. Sai kuma aka ce fadawa kowa ya zo ya yi mubaya’a. Kaji yadda Alu ya zama Sarki. Kuma shi ne dalilin da ya sa da ya ji Turawa na tafe ya tafi Sakkwato domin ziyartar hubbaren Shehu, ta yadda Sarkin Musulmi zai amince da zaman sa Sarki tare da goya masa baya.
Jama’ar gari, mafarauta da maharba ne suka yi bore ga Sarki Alu a lokacin da yakin basasa ya barke.
Basasa a nan na nufin yakin da aka yi don dora Alu akan karagar mulki. An yi shi ne a Ramli shekarar ‘Ba-Sa-Sha’. ‘Sha’ a ilimin Hisabi na nufin 1000, ‘Sa’ na nufin 300, ‘a’ na nufin 1, yayin da ‘ba’ ke nufin 2. Idan ka hada lissafi zai ba ka shekara ta 1303 ke nan bayan Hijira. (daidai da 1894 miladiyya).
Ana kiran Alu da suna ‘Mallam Babba’ (Ma’ana babban malami), domin a wurinmu duk wani dan Sarki Malam ne ko da bai koyi karatu ba. Amma da zarar Sarki ya ba shi wata sarauta sai a daina cewa Malam, a koma kiransa da wannan sarauta.
Alu ya shiga Kano ranar wata Laraba. A wannan lokacin mutane da yawa sun bar Kano zuwa Kamri wajen Tukur, domin shi aka fi so.
An kashe Tukur ne a Gurum (Kamri da Gurum wasu kauyuka ne da ke kusa da juna a kasar Katsina). Na ji labarin cewa an ji masa raunika, sannan aka kawo shi gaban Sarki Alu. An ce Sarki Alu ya yi fushi sosai a kan cewa don me za su yi wa dan uwansa na jini haka? Sarki Alu ya ce: “Ku yi maza ku kawo masa ruwa ya sha”. Amma sai Sarki Tukur ya ce: “Kada a kawo min ruwa, azumi nake yi, ba zan sha ruwa ba”. A haka kuwa Allah ya karbi ransa. Allahu Akbar!!!
A garin Gurum aka binne Sarki Tukur, shi ya sa ake kiransa da ‘Maje-Gurum’ kamar yadda ake kiran Galadima Yusufu ‘Maje-Garko’, ake kiran Sarki Abbas kuma ‘Maje Nasarawa’.
Marigayi Alhaji Mahmud koki tafinta ne na Turawa, shi ne kuma ya ba mu wannan labari. An rubuta labarin a cikin tarihinsa, wanda aka wallafa a shekarar 1977.
ASALIN YAKIN BASASA
Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi shi ne da na biyu ga Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya rasu a wajajen shekara ta 1882 miladiyya a wani gari mai suna kauran-Namoda. Sai kanensa Muhammad Bello (shi ma dan Marigayi Ibrahim Dabo ne) ya hau karagar mulki.
An ce Sarki Muhammad Bello ya rinka kokarin karbe mukamai daga hannun ‘ya’yan ‘yan uwansa yana dasa ‘ya’yansa na cikin sa. Sannan ya kara yawan jakadu masu tattara haraji, abin da ya yi sanadiyyar jefa talakawa cikin matsi ke nan, tare da janyo masa bakin jini a gurinsu. An ce tun a lokacin ya fara share wa dansa Muhammad Tukur hanyar zama Sarki bayan ya rasu, inda ya rinka aika wa da kyaututtuka zuwa Sakkwato domin neman goyon bayan Sarkin Musulmi.
Shi kuwa Sarkin Kano Muhammad Tukur, Sarkin Musulmi Abdurrahman (danyen kasko) ne ya nada shi bayan mutuwar mahaifin Tukur din, watau Sarkin Kano Muhammad Bello. Wasu sun ce bai kai shekaru arba’in ba aka nada shi a kan karagar mulki, wasu kuwa cewa suka yi ba shi da karsashin rike mulki.
A wancan lokacin, sai dan uwansa Galadima Yusuf, wanda yake da ga marigayi Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi tare da jama’ar sa suka gudu zuwa garin Takai, wadda ke kudu maso gabashin Kano.
Mutuwar Galadima Yusuf ce sanadin dora Sarkin kano Alu a mazauninsa. Sannan a hankali suka rinka cinye garuruwan Kano da yaki. A haka har sai da rundunar su ta yi karfi, suka shigo Kano a ranar wata Laraba, 19 ga watan Agusta na shekarar 1894 miladiyya ana buga tambura na sarauta bayan ya samu nasara akan Sarki Tukur, wanda ya gudu ya bar Kano bayan rundunar yakinsa ta raunana.
Da fatan za mu amfanu da darussan wannan labari.