Abin da ya hana gudanar da zabukan kananan hukumomi a Nasarawa – Shugaban APC

Shugaban Jam’iyyar APC mai ci a Jihar Nasarawa, Mista Philips Tatari Shekwo ya musanta jita-jitar da wasu a jihar ke yadawa cewa akwai rabuwar kawuna a tskanin mambobin jam’iyyar musamman masu fada aji da hakan yasa a yanzu jam’iyyar ta rabu kashi-kashi a jihar.  Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu […]

Abin da ya hana gudanar da zabukan kananan hukumomi a Nasarawa – Shugaban APC

Shugaban Jam’iyyar APC mai ci a Jihar Nasarawa, Mista Philips Tatari Shekwo ya musanta jita-jitar da wasu a jihar ke yadawa cewa akwai rabuwar kawuna a tskanin mambobin jam’iyyar musamman masu fada aji da hakan yasa a yanzu jam’iyyar ta rabu kashi-kashi a jihar. 

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa dake hedikwatar jam’iyyar a Lafia, inda ya bayyana jita-jitar da cewa ba shi da tushe. Ya ce ba shakka akwai jita-jita a ‘yan kwanakin nan cewa kasancewar zabukan shekarar 2019 na cigaba da gabatowa an samu rabuwar kawuna a tsakanin mambobin jam’iyyar a jihar, sai dai acewarsa hakan ba gaskiya ba ne inda ya zargi jam’iyyun adawa a jihar cewa su suke yada jita-jitar don su bata wa jam’iyyar kwakkyawan suna da ta samu tun da ta karbi ragamar mulki a jihar.

Ya ci gaba da bayyana cewa “Ina so in tabbatar maka cewa dukkanmu mambobin jam’iyyar APC a jihar nan kawunanmu a hade suke kuma jam’iyyarmu daya ce, kuma zai cigaba da kasancewa daya da yardar Allah. Babu wani rabuwar kawuna a tsakaninmu. Kuma muna da jagora wanda shi ne kuma gwamnan jihar, mai girma gwamna Umaru Tanko Almakura. Kuma kowa yasan da haka. Saboda haka duk wanda ke yada jita-jita cewa akwai rabuwar kawuna a tsakaninmu wannan ra’ayinsa ne, da bazai taba faruwa a zahirance ba da yardar Allah.

“ Game da bukatan da mambobin jam’iyyar a shiYyar arewacin jihar suke yi cewa jam’iyyar a jihar ta ba su damar fito da dan takaran gwamnan jihar a zaben shekarar 2019, kasancewa ba a taba yi gwamna a shiyar ba, Mista Philips Tatari Shekwo ya ce kasancewa APC babbar jam’iyya ce kowa na da dama ko yanci ya gabatar da irin wannan bukata. Sai dai a cewarsa a matsayinsa na shugaban jam’iyyar a jihar ba zai iya yanke hukunci akan batun shi kadai ba. Acewarsa akwai sauran shugabannin jam’iyyar a sassan jihar daban-daban zasu hadu su duba su ga ko ya dace ayi haka. 

Game da dalili da yasa har yanzu ba a gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar ba, shugaban ya ce nan bada dadewa ba wa’adin jami’an hukumar shirya zabuka a jihar zai kare sannan gwamnati zata nada sababbi wadanda zasu gudanar da zabukan ba tare da bata lokaci ba. Ya kara da cewa sau da yawa gwamnatin jihar tana bayyana wasu dalilai kuma da suka sa ba ta gudanar da zabukan a jihar ba wanda a cewarsa daga cikin manyan dalilan akwai karamcin kudi, inda ya tabbatar cewa nan bada dadewa ba idan tattalin arzikin jihar ya inganta gwamnati zata gudanar da zabukan kananan hukumomin da sauran zabuka a fadin jihar baki daya.