Abin da ya hana matatar man Dangote fara aiki bayan wata 4 da kadadamarwa

A baya an ce za ta fara aiki a karshen watan Yuli ko farkon Agusta

Abin da ya hana matatar man Dangote fara aiki bayan wata 4 da kadadamarwa

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote

Matatar man da attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote ya gina har yanzu ba ta fara aiki ba kimanin wata hudu bayan kaddamar da ita.

A wancan lokacin dai, Dangote ya ce matatar, wacce ke da karfin tace ganga 650,000, za ta fara aiki a watan Agusta.

Yayin kaddamar da matatar da Shugaban Kasa na wancan lokacin, Muhammadu Buhari, ya jagoranta, Dangote ya ce, “Masu girma bakin da suka halarci taron nan, man da za mu fara tacewa zai fara shiga kasuwa kafin karshen watan Yuli ko a farkon watan Agusta na bana.”

Sai dai ya zuwa yanzu, kamar yadda jaridar Punch ta binciko, har yanzu ko digo daya na man da matatar ta tace bai kai ga shiga kasuwa ba.

Kakakin Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) Garba Deen Muhammad, a watan Yunin da ya gabata ya ce kamfaninsu zai rage yawan man da yake shigowa da shi da zarar Dangote ya fara tace man a watan Agusta.

Kazalika, wata majiya daga manyan dillalan man fetur a Najeriya ta tabbatar da cewa har yanzu NNPCL bai rage yawan man da yake shigowa da shi ba.

Duk kokarin wakilanmu na jin ta bakin jami’an sashen yada labarai na matatar ta Dangote dai ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

To sai dai wata majiya daga matatar ta shaida wa jaridar cewa mahukuntan kamfanin ba su da tabbacin ainihin lokacin da za a fara aikin tace man a matatar da ke Ibeju-Lekki a Jihar Legas.

Majiyar, wacce ba a amince mata ta yi magana a madadin matatar ba, ta ce, “Ya zuwa yanzu, mahukuntan matatar ba su fitar da wata matsaya ba a kan haka.”

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja