Abin da ya ja hankalina na musulunta — Rabaran Adamu Shani

In har Yesu zai daga hannu ya roƙi Allah ashe shi ba Allah ba ne.

Abin da ya ja hankalina na musulunta — Rabaran Adamu Shani

Adamu Shani

Aminiya ta tattauna da wani tsohon fasto wanda ya karbi addinin Musulunci a kan dalilinsa na barin Kiristanci ya koma Musulunci.

A tattaunawa Rabaren Malam Adamu Shani ya bayyana cewa ya gano akwai tufka da warwara a littafin Baibul da sauran abubuwa.

Mene ne takaitaccen tarihinka kuma mene ne dalilan shigarka Musulunci?

Sunana Muhammad Adamu Shani, ni haifaffen garin Bakasi ne a Karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe.

Ni dan kabilar Waja ne kuma a da ni Rabaran ne kafin in musulunta. Na yi karatu a Makarantar Baibul ta ECWA Bible Training School da ke Kufai a garin Billiri a Jihar Gombe.

Bayan na gama sai na yi difloma a Makarantar Baibul da ke Kagoro (a Jihar Kaduna) bayan nan sai na yi digiri a ECWA Theological Seminary da ke Jos.

Ban tsaya ba ina ta karatu har na samu digiri na uku a kan ilimin addinin Kirista.

Kasancewata Rabaran a lokacin na zauna a kasar Isra’ila shekara tara bayan na dawo Nijeriya ne Allah Ya kira ni zuwa Musulunci inda na karbi addinin Musulunci a ranar 27 ga watan Satumban 1999 a garin Shani a Jihar Borno.

A can na shiga makarantar koyon addinin Musulunci ajin sababbin musulunta a Makarantar Imam Malik Islamic Centre na Maiduguri, bayan nan sai na tafi Makarantar Higher Islam, School of Legal and Islamic Studies a lokacin ana kiran Makarantar Borno School of Legal and Islamic Studies yanzu kuma ta dawo Mohammed Goni Colleges of Legal and Islamic Studies, Borno.

Bayan na gama sai na na yi NCE a karkashin Cibiyar Ilimi ta Kasa (NTI).

Da na gama sai na dawo Gombe na yi difloma a addinin Musulunci a Makarantar da Sheikh Bin Sale ya bude, ina gamawa sai na je Jami’ar Tarayya ta Kashere na yi digiri.

Malamina ne ya saka min suna Shani, amma ni ba dan Shani ba ne, ni Bawaje ne na Karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe.

Me ya ba ka sha’awar shiga Musulunci duk da ka zama Rabaran?

Gaskiya abubuwan da yawa sai dai in fada maka kadan.

Abu na farko da ya jawo ni zuwa shiga addinin Musulunci shi ne a cikin Littafin Baibul cikin Yahaya, Sura 1 aya ta 1 an karantar da cewa cikin farko akwai kalma kalmar nan kuma tana tare da Allah kalmar kuma Allah ne, ma’ana wannan kalma tana nuna cewa Yesu Allah ne bisa ga abin da wannan aya take magana a kai.

“In the beginning was the word and the word was with God and the word was God.”

To binciken da na yi a kan wannan magana a cikin lLttafin Baibul sai na samu akasin haka a cikin abin da Yesu ya koyar a cikin Littfain Yahaya, Sura 5 aya ta 30.

Yesu ya ce “I on my own do nothing as a I hear I do judge for my judgment is just wide do not do my will but the will of down sent to me.”

Ma’ana “Ni ba na iya yin komai ni kadai yadda nake ji haka nake yin hukunci domin hukuncina kuwa na adalci ne don ba nufin kaina nake bi ba sai dai nufin wanda Ya aiko ni.”

Idan za a duba waccan ayar da ta ce Yesu shi ne Allah to ga shi Yesu ya fadi cewa ba ya iya yin komai.

Ashe ke nan idan aka lura babu abin da Allah Ya gaza yi. Allah Yana yin komai a kowane lokaci da Ya ga dama.

Yesu kuma cewa ya yi sai ya ji sannan ya yi. To wa ya aiko shi?

Baibul ya ba da amsa a cikin Littafin Yahaya, Sura 13, Aya ta 3. Yesu ya ce a wajen Allah ya fito a wajen Allah kuma zai koma, wannan ne ma’anar ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.’

Baibul ya kuma nuna cewa an yi wa Annabi Isah (AS) kaciya a lokacin da aka haife shi, bisa ga Littafin Luka, Sura 2, Aya ta 21 zuwa ta 22.

Sun ce an yi wa Yesu kaciya a lokacin da aka haife shi a wuni na 8 a duniya.

Ashe hakan na nuni da cewa ba zai yi wu a ce an haifi Allah ba.

Abu na biye da shi ne Yesu ya yi addu’a yana rokon Allah. In har Yesu zai daga hannu ya roki Allah ashe shi ba Allah ba ne.

Da shi Allah ne da ba zai roki Allah Ya fada masa damuwarsa ba. A cikin Littafin Martha, Sura ta 27, Aya ta 46.

Yesu ya yi magana da Yaren Hibru da Armaik ya ce ‘Ilohi ilohi Ilamasta baktani,’ wato ‘Ya Allahna! Don me Ka yashe ni?’

Yesu yana rokon taimako a wajen Allah.

Har ila yau a cikin Littafin Yahaya Yesu ya yi bayani da kansa a Sura ta 14, Aya ta 1, lokacin da zai yi ban-kwana da almajiransa ya fada musu cewa kada zuciyarsu ta baci su ba da gaskiya ga Allah sannan su ba da gaskiya gare shi.

Me ya sa ya fadi haka saboda shi kansa ya ce Allah ne Ya aiko shi. Ke nan ya tabbata shi ba Allah ba ne.

Ganin haka ne ya sa na gane cewa kwata-kwata Annabi Isah ba Allah ba ne.

Har ila yau a cikin Littafin Yohanna, Sura ta 3, Aya ta 16, Baibul ya nuna cewa “For God soul of the world that he gabe his be gotten son so whoeber beliebe in him should not ferish but has eberlasting life.”

Wato Allah Ya yi kaunar duniya har ma Ya ba da dansa haifaffe shi kadai domin duk wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya lalace amma ya samu rai na har abada.

Baibul ya nuna cewa Yesu shi kadai ne dan Allah a nan, a can baya kuma an nuna cewa Yesu din shi ne Allah, ka ga wannan magana guda biyu sun saba wa juna.

Baibul ya ce Yesu shi kadai ne dan Allah in ka nemi Littafin Baibul sai ka ga maganar ba haka take ba.

Ga misali a cikin Littafin Irmiya, Sura ta 31, Aya ta 9, Baibul ya nuna cewa Ifiraymo dan farin Allah ne.’

A can an nuna cewa Yesu shi kadai ne dan Allah, yanzu kuma a nan an sake nuna mana cewa akwai Ifiraymo shi ne dan farin Allah.

Sannan a cikin Littafin Zabura, Sura 22, Aya ta 4, Baibul ya nuna cewa Isra’la ma dan farin Allah ne.

Ka ga ba maganar Yesu ba kuma an samu Ifiraymo dan farin an samu Isra’ila ma dan fari. Isra’ila nan fa shi ne (Annabi) Yakubu.

Hakan na nufin cewa Baibul ya nuna Allah yana da ’ya’ya da yawa ke nan?

Eh, haka ne ke nan mana, tunda ga surori daban-daban a cikin Baibul suna nuna cewa Allah yana da wasu ’ya’ya bayan Yesu.

Ya sake cewa Dauda ma dan farin Allah ne.

Ganin cewa ka kure mataki a addinin Kirista ga shi ka musulunta wane kalubale ka fuskata a wajen Kiristoci da wadanda kuke tare?

Gaskiya na fuskanci kalubale sosai. Na farko ’yan uwana Kirista suna ce min na musulunta ne don neman kudi.

Na biyu suna min ganin na musulunta na fada hannun shaidanun mutane domin su Kiristoci suna kallon Musulunci addini ne na ta’addanci.

Saboda abin da ake nuna musu shi ne Annabi Muhammad (SAW) dan ta’adda ne ‘Wa iyazu billah!’

Akwai wani littafi da kullum nake tare da shi wanda a cikinsa suka nuna cewa mu tsare kai daga addinan karya a koyarwarsu, sun ce addinin Musulunci addinin karya ne.

Ni ina ganin na fahimci gaskiya ta shiga Musulunci, su kuma suna min kallon yanzu zan koyi ta’addanci, saboda ba su fahimci cewa Musulunci addni ne sahihi ba.

Yaya iyalanka bayan dawowarka Musulunci?

Matata dai da farko sai da na shekara biyu ina zuwa kotu ina shari’a da ita, amma haka dole na hakura da ita saboda ta ki yarda ta dawo Musulunci.

Wai in har za ta dawo gare ni sai dai idan zan bar Musulunci.

Wasu kuma da nake tare da su sun tsangwame ni sosai.

’Ya’yanka fa?

Allah Ya taimake ni a cikin ’ya’yana da na haifa ina Kirista su biyar, guda hudu Allah Ya shirye su sun biyo ni, daya ne ya bijire.

Gaskiya addinin Musulunci ya taimake ni wajen ganin na yi karatu domin duk lokacin da za ka yi addini babu ilimi a ciki akwai matsala.

Karfin gwiwar da na samu a bangaren ilimi shi ne abu na farko kuma abu na biyu.

Akwai bayin Allah da suke tausaya min bayan a baya can da nake Rabaran duk wata dawainiyata, Ikilishiya ce take dauka amma yanzu na dawo Musulunci ba ni da wani aikin yi ba ni da sana’a ga shekaru sun kama ni, sai dai ’yan uwa da suke jin labarina cewa na musulunta ne suke taimaka min.

A da wace majami’a kake shugabanta?

Da farko dai ni ne Faston Cocin ECWA ne da ke Federal Low Cost a Gombe.

Mu muka kafa cocin tun yana zana har aka gina shi lokacin ni ne na canji Fasto Labari, wani mutumin Jos.

Na rike wajen a matsayin shugaban fastoci na cocin abokin aikina kuma Fasto Timothy Ibrahim wani Bawaje shi ya rike ECWA na Dukku.

Yanzu sana’ar me kake yi don rike kanka da iyalanka?

To gaskiya ba ni da wata sana’a sai noma, idan noman ya gagara wani lokacin kiwo kajin gidan gona, tunda noma sai da kudi sai kuma wasu bayin Allah da suke dan taimaka min lokaci zuwa lokaci.

Babu abin da zan cewa Shugaban Izala na Kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Shugaba na Jihar Gombe, Injiniya Salisu Muhammad Gombe da Sheikh Yakubu Musa Sautus Sunnah.

Gaskiya suna iya kokari wajen tura min ’yan kudi lokaci bayan lokaci kuma ina yi musu godiya.

Yanzu mene ne burinka a addinin Musulunci ganin ka zama malamin Musulunci?

Burina shi ne ina fata Allah Ya dauki rayuwata ina aikin da’awa da yada Musulunci.

Ina kuma rokon Allah Ya kara min karfin gwiwar dagewa ba tare da gajiyawa ba domin ina shiga lungu da kauyuka ina kiran wadanda ba Musulmi ba zuwa ga Musulunci.